Daudar Gora Book 2 Page 21
Daga nesa da masarautar ya tsaya a inda suka ɗauka motar, Ta-ƙurya dake a bayan motar ta jawo dukkan kayan ɓadda kamarta ta maida a jikinta, haka shima hadimin nata sannan suka fita a motar. Kamar yanda suka fita ta ɓarauniyar hanya da taimakon hadimintan haka suka koma cikin masarautar. Ta sauke bahaguwar ajiyar zuciya lokacin da take zubewa a saman ƙawataccen gadonta. Har yanzu kanta juya mata yake, har yanzu warin da ta shaƙo ya gagara barin hancinta. Ga matsanancin tashin hankali, taya ita kam zata lallashi uwa, bayan ɓacin rai ya rufe idanunta ta faffaɗa mata maganganu marasa da ɗi. Ta ina zata fara? Matsaloli sake yawa suke a rayuwarta….
Samun lafiyar Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed ta saka razanin a zukatan wasu a cikin masarautar matuƙa. Dan da gasken gaske ba haka suka so ba. Ga soyayyar mutanen ƙasa tako ina bisa ɓoyayyun alkairansa da suka gano sanadin ganin fuskar a zahirin Shahan-shan ɗin su yanzu. A yanzu kam babu inda zakaje kaji ana zaginsa sai abinda ba’a rasa ba kasancewar duniya duk masoyanka sai ka samu maƙiya, hakama duk maƙiyanka sai ka samu masoya.
Shari’ar farko da yay shirin fara gabatarwa itace kawo dai-daito tsakanin iyayensa. Sai dai kuma sam hakan yaƙi yiwuwa saboda Malikat Bushirat ta matuƙar ɗaukar zafi. Dan gaba ɗaya tana kallon Malikat Haseenat ne a mai son kanta da fifita bare sama da gudan jininta. Harzuƙar tata na hauhawa ne bisa jagorancin rura wutar da su Miran Jasim keyi ta bayan fage. Yayinda ita kuma Malikat Haseenat tai biris kamar ma bata san mike faruwa ba. Ta kuma tsaya tsayin daka wajen bama Iffah kariya da ƙara tsaurara tsaro na hana bama kowa hanyar iya cutar da ita. Al’amarin na ƙara rikitar da kowa dan an kasa gane bakin zaren takun saƙar tasu akan Iffah balle manufar kowanne.
A randa doctor ya sallami Iffah dole aka maidata kurkuku, dan rikici neman tashi yayi a zaman fada tunanin wasu haka shine take-taken Tajwar Eshaan ɗin. Shi dai komai baice musu ba har suka gama cece kucensu. Sai a washe gari ya bada umarnin tsaida ranar da za’ai zaman shari’a. Dan a zahiri ba su Miran Arshaan bane kawai ke tada jijiyar wuya kan ganin anyi shari’ar, har Malikat Bushirat zungurarsa take yi matuƙa akan al’amarin. Acewarta in har bai gurfanar da Iffah ba ita zata ɗauka duk matakin da ya dace a kanta…
Rana ce data kasance na zaman shari’a tsakanin Iffah da ahalin Tajwar Eshaan akan yunƙurin halaka ɗan su. Ƴan jarida sun so halartar wannan shari’a ƙwarai da gaske, hakama jama’ar gari. Sai dai hakan bata faru ba sakamakon cewar Shahan-shan wannan shari’a ce ta cikin gida. Ba haka su Miran Jasim suka so ba, sai dai basu ce komai ba dan kar nuna zaƙewarsu yay yawa ya harbosu dan sun san hatsabibi ne. A yanzun ma suna cikin taka tsantsan ne a duk wani motsinsu.
Kasancewar shari’ar cikin gida ce kamar yanda Shahan-shan ya faɗa da kansa anyi zaman gudanar da ita ne a falonsa na biyu. Zaman ya kasance a iyakar waɗanda ya shafa, sai manyan masu faɗa aji a ɓangaren shari’a. Falon yay tsit kowa ya nutsu kawunansu a rissine duk da kasancewar duk iyayensa ne a wajen da kuma yayunsa, sai dai girman da ALLAH ya ɗaura masa na shugabancin da har suma suka kasance a ƙarƙashin sa ya tilasta musu biyayyar da girmama wannan girman koda basa so. A sannu ya ke binsu da ido ɗaya bayan ɗaya har idanunsa ya sauka a kanta ƙyam. (Miyasa kika fi yarda da zaɓa mana haka a lokacin da zaɓin ya fi rinjayen kasancewa a zaɓin wasu?) Ya ayyana a zuciyarsa cikin ɗan jansu idanunsa luuu, lumshesu yay tare da ɗan matsesu, sai kuma ya buɗe yana mai kauda kansa. Kusan tsahon mintuna biyu yaja isaka ya fesar yana mai ɗanyin gyaran murya da sake saita kansa.
A nutse Sayeed Hanifud-Din ya fara da, “Alhmdullih kamar yanda na sani kuka sani yau ranar 21/4/2022 zamu fara sauraren wannan ƙara. Muna roƙon UBANGIJI ya bada ikon kamanta zartar da hukuncin adalci wajen bama mai hakki hakkinsa batare da san zuciya ba”.
A tare aka amsa da amin har lokacin kawunansu dai a ƙasa. Ƙoƙarin hana idanunsa da ke fusga gareta yay. Sayeed Hanifud-Din ya cigaba da faɗin, Muna buƙatar sake ji da ga bakin masu ƙara. Muna fatan abinda ke a zukatansu ne zai fita a harsunansu, kuskuren hakan na nufin ɗaukar mataki takowace fuska da shari’a a ta koyar damu”.