Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 176

Sponsored links

Sayeed Hanifud-Din ya cigaba da fadin, “Kotu na bukatar jin duk tsiyatakun daka jagorancesu aikatawa”.

 

 

 

Cikin rawar murya data baki ya shiga zayyane komai. Da ga karshe ya dora da fadin, “Naki fada musu gaskiya ne tun farko saboda karsu daina bani kudin da suke bani. Amma ni nasan anfi karfinsu a duk inda suke kai hari. Bakuma zasu samu cikar burinsu ba har abada”.

Ba wanda suke a kotun ba hatta Miran Jasim da Miran Arshaan wan irin kallo suke masa mai ban mamaki, sai dai ko sau daya yaki yarda ya dubesu shikam, Bayan shi an fiddo hadiman da suka kashe Sayeed Khairul-Bashar. Inda suka zayyane komai har yanda Miran Jasim ya sakasu aikin, da yanda suka sacesa lokacin da yake fitowa da ga sashensa zaije sallar asuba. Sun azabtar da shi matuka, dan azabtarwarce ma ta kaisa ga rasa rayuwarsa. Sosai wasu ke kuka, iyalansa kam su kadai suka san irin zafin da sukeji a zukatansu. Babu abu mafi ciwo sai gain amintaccen hadiminsa a cikin wadanda suka halakashi.

Sayeed Hanifud-Din ya ja numfashi da fesarwa yana mai sake fuskantar kotu. “To Alhamdullah wanna kenan. Sai kuma gwajin kwayoyin halittar da wanna kotu ta bada akai mata tsakanin Zawjata-almilk da mahaifanta guda uku, inda gwajin ya tabbatar da Zayyan ibn Abbas da Ammarah bint Abdul-majeed Ally Qutb matsayin mahaifanta na gaskiya. Wadan nan sune gwaje-gwajen, gashi za’a jaranto.”, tiryan-tiryan ya karanto komai, a take matasan nan da Iffah yanzu ta jawo jikinta suka cika kotun da kabbara. Da kyar aka tsawatar suka lafa.Miran Jasim kam sai kawai yaji ya fashe da kuka tsabar yanda zuciyarsa tai wani irin kunci da takurewa waje daya a kirjinsa,

Bayan shirun da kotun ta dauka kowa ya zuba ido da baza kunne na jiran yanke hukunci ga Shahan- shan da kuma makarrabansa da ke zaune yau a kusa da shi domin yanke hukuncin. Yaja tsahon mintuna hudu shiru kafin yaja numfashi mai sanyi, cike da nutsuwar nan tasa da kamewa ya motsa tausasan lips dinsa idanunsa kyam akan Iffah ta cikin bakin gilashin daya sakaya su. Tana kwance ne a jikin kafadar Malikat Haseenat idanunta a lumshe da alamar har yanzu batajin dadin. Janyewa yay a hankali ya maida ga takardun gabansa ya sake motsa lips dinsa.

“A bisa hujjoji da kwararan shaidu da ji da ga bakin masu laifin wannan kotu mai adalci tayi dubi da nauyin laifukansu da hukunce-hukuncensu masu nauyi daya dace ta musu. Domin saukaka wahalarwa ga kotun ta yankema Miran Jasim da Miran Arshaan hukunci ta hanyar rataya a tsakkiyar al’ummar wanna kasa a dunkule bisa laifukansu…..

A take kotun ta dauki kabbara cikin motsuwar zukata da tsananin rudani musamman ga Miran Jasim da Miran Arshaan da sukai wata irin zabura. Da kyar aka samu aka lafa ya cigaba da fadin. “Za’a yanke musu hukuncinne a ranar bikin al’ada dake hada kowa da kowa da za’a iya bukata da fatan su shaida Kafin hakan zasu cigaba da zama a cikin kurkuku, zakuma su bayyana dukkan laifukansu a gaban yan jarida. Bama bukatar wata kungiya a duniya wajen mana katsalandan akan hakan, zakuma su biya diyyar ran yarinyar Sayeed Hifzur-rahaman da ta Sayeed Khairul-Bashar ga iyalansa. Hakama zasu biya kudade masu nauyi ga ahalin Fhareedah bint Zayyan da suka wahalar bisa son zuciya. Bokansu an bashi damar zaman kurkuku na daurin rai da rai idan yana da rabon shiriya ALLAH ya shiryar da shi. Hakama hadiman da sukai musu ayyukansu an yanke musu hukuncin daurin rai da rai suma. Wannan kotu ta sallami wanda ya samar musu da dafin macizai abisa gargadin kiyayewa. Idan ya sake sakaci makamancin wanda yay zai yabama aya zakinta. Haifah za’ai mata hukuncin bulalar aikata Zina tare da zaman kurkuku na shekara goma bisa yunkurinta da hadin bakin son yin kisa. ALLAH yasa mufi karfin zukatanmu, ya yafe mana kurakuranmu mu da zuri’armu da al’ummar mu baki daya”. Da ga haka ya mike. Babu wanda ya iya motsawa har sai da ya fice. Kotun tai wani irin harmutsewa kowa na ALLAH wadai da halayyar su Miran Jasim da kuna da tashin hankalin karshen su Miran Jasim da kuna da tashin hankalin karshen su yama hanasu iya duban kowa. Arshaan sarkin rudiya ma kuka yakeyi, dan yayi nadamar biyema Jasim a rayuwarsa duk da shima da nasa kudirin. Amma bai taba samun kwarin gwiwar aikatawa ba sai da suka dunkule. Haka aka wuce da su da kyar da ga cikin kotun aka maidasu kurkukun…

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button