Daudar Gora Book 2 Page 175
Ajiyar zuciya kawai kakeji na sauka da al’ajabin wadan nan abubuwa wai kamar wata almara. Banou da kowa ya sani mafi zama kololiwar amintacciya ga Malikat Haseenat dai, wadda inba abincin data girka mata ba batacin abincin kowa sai Daneen Ammarah. Kai to ai yanzu kowama ba abin a yarda da shi bane hatta hadiman nasu.
Kaka ya jefama Banou tambayar, “Mutane nawa kika cutar a shekarun zaman nan naki?”
Salati wajen ya dauka da sallami, kowa na tsinema wa da banou. Cikin girmamawa Kaka ya dubi Shahan-shan da shi gaba daya ma komai ya tsaya masa cak. “ALLAH ya karama adalin shugabanmu lafiya da tsohon rai mai amfani, a ganina barin wadan nan bashi da wani amfani, a samu dutsina a juye musu ruwan maganin nan kawai a musu rajamu anan, dan wadan nan mutane nada karfin tsafin da rufesu ko musu hukuncin zaman kurkuku bazai taba iya magance matsalarsu ba. ALLAH yasa ban shiga hurumin da ba nawa ba”.
Shiru baice komai ba. Kusan minti uku sannan ya dubi Sayeed Fayzul-haq. Da ga haka ya taka a hankali gaban Iffah. “A gusa daga jikinta”,. Iya abinda ya fada kenan. A take kuwa tai hamma jikinta ya saki gaba daya. Rikota yay cikin jikinsa ya rungume. A take kowa da kowa na wajen yay saurin yin kasa da kansa cikin hanzari. Shiko ko’a jikinsa ya dagata cak dagakasa kamar ya manta ma da wasu halittu a wajen yay wucewarsa.
🥱Wannan fa shine ga abin fada babu damar magana 😝
Kamar yanda kaka ya fada kuwa haka akai, tuni hadimai suka cika wajen da duwatsu, kaka ya yayyafesu da ruwan magani, Kamar jira suka shiga diba ana ambaton sunan ALLAH ana jifan su Banou.Ihu suke mai tsananin kururuwar sauti. Amma mutanen nan ko’a kwalar rigarsu. Dama wasu harda fushin Banou tai musu sanadin yaya wasu iyaye, wasu maza, wasu matansu. Dan a cikin wanda ta halakar mafi rinjaye hadimai ne. Babu wanda ya tausaya musu a haka aka jefesu har sai da suka daina numfashi.
“Ni ban san adadi ba. Amma na halakasu da yawa, dan akwai ayyukan da na dinga ma uwa da yarjewar wata babba a gidan nan. Sannan akwai wadanda na kashe dan radin kaina da wanda na dinga cinyewa cikinsu. Na karshen nan dana cinye shine na Jasrah a randa Zawjata-almilk bata da lafiya
Kamar yanda kaka ya fada kuwa haka akai, tuni hadimai suka cika wajen da duwatsu, kaka ya yayyafesu da ruwan magani, Kamar jira suka shiga diba ana ambaton sunan ALLAH ana jifan su Banou.Ihu suke mai tsananin kururuwar sauti. Amma mutanen nan ko’a kwalar rigarsu. Dama wasu harda fushin Banou tai musu sanadin yaya wasu iyaye, wasu maza, wasu matansu. Dan a cikin wanda ta halakar mafi rinjaye hadimai ne. Babu wanda ya tausaya musu a haka aka jefesu har sai da suka daina numfashi.
Kakane ya ce abar gawawwakin a wajen masu su zasu aiko a debe su, dan sune aiken farko da zasu turama kabilarsu. Haka kuwa akayi, sai dai dan daukar da was samari da yammatan gidan sukayi a wayoyi suka saka a social media cikin kankanin lokaci al’amarin yay amsa kuwa. Wasu kungiyoyin kare hakkin dan adam suka shiga caccakar al’amarin a bayyane ta kafafen ya da labari, kafin wasu awanni labarin ya shiga zagaye duniya, ya zama video mafi rinjaye da ke yawo kuma ake kallo…..
Sun iso gareta a whale, wahalar da duk wanda ke cikin wanna zuri’a sai da ya girgiza. Hakan yasa su yin cirko-cirko da zaman sauraren abinda sukazo da shi. Ita ko tana zaune a cikin kujerar tsafinta hancinta da Iffah ta gundile ya kara saka fuskar munana matuka. Hakama sauran raunikan da taji sun kumbura fuskar ta kara zama humm.
Cikin gurfana da garshekar hakin rudani daya da ga cikinsu ya shiga zayyane mata abinda ke bakinsa, “Shugaba wannan aikin yafi karfinmu, ba namu bane ba sai dai ke. Sun halaka Rudde da Zambo da Banou Sun halakasu har lahira uwarmu mai share kukanmu”.