Daudar Gora Book 2 Page 172
Duk wanna al’amarin Iffah nacan kwance tana shan barcinta bata san bikin da ake ba. Dan sai la’asar ta tashi. Wanka tai tayi salla. Bayan ta kammala kimtsawa ta fito neman abinci dan yunwa takeji. Hadimanta da ke dan kus-kus din su suma akan al’amurin Malikat Bushirat din sukai saurin mikewa. Kallo daya ta musu ta dauke kanta, dan har yanzu zuciyarta babu dadi. Zama tai tare da bada umarnin a kawo mata abinci anan. Cikin ko kankanin lokaci amintacciyarta ta jere komai. Ta bude zata zuba mata ta dakatar da ita idanunta kur akan abincin. “Waya dafa wannan abincin?”Ta fada tana kallonsu. Cikin rawar jiki amintacciyar tata ta sanar mata itace da mai girki. Ta nuna mai abincin. Shiru Iffah tana duban wadda aka nuna matan sai faman sinkuy da kai take. Ai bama tasan ta daka mata tsawa ba tace ta dago. Ba ita da taima tsawar ba hatta sauran hadiman sun matukar razana. Dan abu ne da bata taba musu ba. Wani irin kallo Iffah take ma matar rai bace. Jikinta har tsuma yake ga idanunta sunyi jazur na tashin hankali. Duk wanda ya dubeta sai ya razana, idan ma irin su Bily ne fitsari zamu saki a zani😝Dan gaba daya ta juye tabbacin ba Iffah bace.
Wani irin shakota Iffahir tayi ta dauke ta da bahagon marin da ya idasa tsurar da sauran hadiman jikunansu suka fara rawar mazari. Marin matar nan Iffah take tamkar ALLAH ya aikota. Gashi ta shaketa da iya karfi. “Ubanwa ya aikoki nan?”. Ta fada da wata irin gigitacciyar murya mai matukar razanarwa da amsa kuwwa. Cikin kakarin azaba matar da gaba daya ta gama jiyo kamshin mutuwa da kyar ta ce, “Uwa.”
“Uwa. uwa. Iffah ta fada kamar mai bitar sunan, sai kuma ta kyalkyale da dariya ta kuma hade fuska. Cikin dage gira da zuba jajayen idanunta a tsakiyar na matar da ke a shake har yanzu a hanunta ta ce, “Ohhhyyyyo ita bata gane karatun kurma kenan. Bakuma ta gane gargadin makawo sai ya doka sandarsa. Shin wai dolene sai ta fusatani ne?!!!!!. Nace sai ta ga ainahina sannan zata tabbatar nafi Karfinta?!!”. Ta sake fada cikin karaji tana gwara kan matar da centre table. Wata iriyar wahalalliyar kara ta sake illahirin jikinta na rawa dan fa ta bugu matuka duk da katako ne. Tuni hadiman sun fara sakin fitsari a wandunansu. Yayinda Iffah da bata san sunayi ba tana cigaba da maka kan matar nan jikin centre table. Sai da tai mata ligi-ligi har numfashinta na fita da kyar ga jini yay mata faca-faca sannan ta dagata tsaye, cikin daka tsawa ta dubi amintacciyarta tace a kira mata Ghazi guda biyu. Cikin kankanin lokaci suka iso kuwa. Jefa musu matar tayi taki zube yaraf a gabansu. Rai bace ta ce, “Ku dauketa, a dauremin ita a tsakkiyar masarautar nan”. Cikin rawar jiki suka amsa mata da “Umarninki shine abin jiranmu ranki ya dade”. Kota kansu batabi ba ta nufi dining, wajen wanke hannu ta nufa ta wanke hanunta da jini ya dan bata, har yanzu a birkicenta take. Bedroom dinta ta koma, babu jimawa ta sake fitowa cikin sabuwar shiga. Har yanzu hadimanta na lafe jikin bango a tsorace. “Ku biyoni da wannan abincin”. A zabure duk suka mike, Itako tuni ta ma fice abinta. Kamar yanda ta saba tafiya duk inda take so a kafa yanzun ma hakane. Sai dai yau ko sau daya bata kula gaisuwar kowanne hadimi ba. Koma kallo basu isheta ba har ta isa sashen Malikat Haseenat. Anan din ma babu hadimin data kula Sai dai tana binsu da kallo daya bayan daya. Ganin babu wadda take nema cikin wata irin razananninayar murya ta kwala