Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 156

Sponsored links

“Tabbas anyi haka”.

Cewar Malikat Haseenat. Murmushin Kaka yayi, da cigaba da fadin a lokacin amintaccen mahaifina ya bani gawar wata jaririyar dana canji jaririyar da ita ya fito da wadda aka haifa. Bakowa bane kuma sai wanda a yanzu kuke kira da Baba mai magani a gonar yaro, shugaban masu magajin gargajiya na wanna masarautar, saboda shi din yaron mahaifina ne”…

 

.….”Na iso gida da farin cikin wasan ya kare, sai dai ina danka jinjirar a hannun mahaifina ya kalleta da juya bayanta ya tsirama tambarin tawadar ALLAH dake a bayan nata idanun, sai cewa dani yay (A sanadin ta kullika da yawa zasu bude. Harma da wanda ba’ai zato da tsammani ba. Zata zama tauraruwa mai hasken gaske a cikin taurari, zata kuma zama shahararriya a duniya bama a kasar ruman kawai ba. Zata auri mutum mai daraja da cikar kamala, amma sai kunyi hakurin jure rasawa kafin ita ta samu. Sai kun boye komai kafin komai ya bayyana. Hatta da mahaifinta zai raineta ne batare da yasan ita bace) ban fahimci mi yake nufi ba, Ni damuwarta ma a lokacin yanda zamuyi da yarinyar nan. Kamar da ga sama sai ga Zayyan, baba ya sani na boye jinjirar sannan aka bashi izinin shiga. Bayan ya gaishemu yake sanar mana Jumayma na nakuda ne, yazo amsar mata magani ne a wajen kaka kamar yanda ya saba basu. Babu musu mahaifina ya hada masa komai ya basa, tare da sanar masa ya gaggauta komawa a bata tasha. Bayan wucewarsa da kadan mahaifina ya ce nai haramar daukar jinjirar nan nabi bayansa, dan Jumayma zata haihu yarta babu rai, na dakko waccan na alive musu wannan din. Da mamaki na tambayesa yanda akai yasan haka, danni dai dama wadan nan abubuwan nasa yasa nake kyamatar harkokinsan. Dan murmushi kawai yay, da fadin kusan wata guda kenan Jumayma a sanarmin batajin cikinta na motsi, a ranar karshe da tazo kuma na fahimci yaron cikinta ya mutu mata a ciki ne, shiyyasa ma nace matarka taje ta zauna da ita a can ita da Maman Zayyan. Nan ma a tsorace nace to kace baka son kowa ya sani, amma taya zan canja yarinyar bayan su zasu amshi haihuwar? Nan ma sai da yay yar dariya sannan yace karka damu jeka kai dai ka basu. Kaina a daure da wannan lamari nasa na tafi, na sake dawo da jinjira cikin Daular ruman. Ban yarda na shiga gidan ba, na saka aka kiramun matata (lyyani) a sirrance, a mamakina koda ta fito na bata jaririyar bata nunamin damuwar komai ba face rungumeta da tai da sumbatarta ta shige abunta. Ashe ni ban fahimci yanda al’amarin yake ba sai da na dawo gida yake sanarmin ba lyyanin bace, suffarta kawai aka shiga. Nasan zaiyi fiye da hakan ma, sai bance komai ba dan banda abin fadar. A takaice dai yarinya taci suna Fhareedatu, amma iyayenta na mata alkunya da Iffah, da gani sai babana muka san ba yarinyar da

Jumayma (Ummu) ta haita bace. Sun cigaba da rainonta cikin yanayin ciwuka daban-daban, dan tanata laulayi har sat da takai Jumayma ta dawo da zama Jumna tare damu. A lokacin jikin baba yayi tsanani, amma haka ya dinga fadamin abubuwan maganinta, dan ya tabbatar min abinda sukai niyyar yi da itane ya tabata tun tana a ciki, ALLAH ya bata kariyane baiyi tasiri ba, sannan iskokin da ke akan mahaifiyarta ma masu karfine, a yanzu haka ma sun dawo jikinta itama. Kwanan Jumayma bakwai da zuwa gida ALLAH yay ma mahaifina rasuwa shima, inda ya barni da wasiyya mai girma akan Iffah. Ya tabbatar min hatsabibiyar bokanyar nan zata dawo, zata dawo cikin wanna masarautar dan akwai wanda ke tare da ita da jimawa, zata dawo ta jikinsu kuma zata cigaba da illar daukar fansa. Dan tun fil’azal tanada burine darna akan karagar mulkin Shahan-shan. Ya umarcenta karna sake zuwa cikin masarautar, amma Zayyan ya cigaba da kai zumarsa babu wanda ya isa ya ganeshi, hatta ita mahaifiyar yarinyar ma bazasu tapa hada koda hanya ba sat bayan komawar iffah cikin masarautar matsayin matar aure. Hankalina ya tashi, na tambayesa ta yaya kuma zata koma. Ya cemin la kudirar UBANGIJI, amma st kansa bai sani ba. Abinda kawai zanyi shine a duk lokacin da hakan yazo duk abinda na gani a mafarkina har sau uku

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button