Daudar Gora Book 2 Page 145
Abdul-Shakhur in Khairul-Bashar shugaban tawagar ya share kwallar da suka ciko masa ido. Cike da girmamawa a gareta ya ce, “Lallai ke alheri ce garemu gimbiyarmu. Ke haske ce mai haskaka fararen fitulun da ke zagaye da daular ruman. Kasancewarki damu sake buda mana sanin wanene adalin shugabanmu yake da kyawawan halayensa a koda yaushe. ALLAH ya kara miki daraja, ya albarkaci rayuwarki data shugabanmu, ya zagayeku da kariyarsa da ni’imominsa. Yay riko da hannayenku ya baku ikon sauke nauyin al’umma da adalci. ALLAH ya bamu ikon muku biyayya ya karemu zaginku koda a bayan idanunku. ALLAH ya karya makiyanku koda jininmu ne ya azurtaku da zuri’a masu irin kyawawan halayarku da dabi’unku. ALLAH ya jika magabata, wanda suka rage ALLAH ya rabaku da su lafiya…
Haka ya cigaba da jero addu’oi sauran a amsawa da Amin tare da hadiman da suka zagayesu cike da farin ciki. Iffah kam sai taji har hawaye na ciko mata idanu. Tabbas babu abinda ya kai kyautatawa dad da soyayyar mutane. Da ace dan adam ya gane da ya kasance mai kyautatama mutane sabanin munana masu. Kyautatawa na bada muhimman abubuwa uku a lokaci guda. *_DARAJA. SOYAYYAR MUTANE.
SANNAN LADA A WAJEN UBANGIJI_* Cikin kankanin lokaci masarautar ta harmutse, bakin kowanne hadimi ka kalla a washe da farin ciki musamman idan ya kama yan kudadensa da kayan sakawa kusan kala biyar uku a hannu. Ga iyayen kaji da shanu an zube musu na girkin salla. Ga albishir na basu damar yin shagalin bikin sallarsu kamar yanda kowa keyi. Harda damar yin gyaran jikinsu matsayinsu na mata Iffah tabama matan, dama albishir din kawo masu gyaran jiki โฌikin masarautar saboda hadimai matan kawai. Kai jama’a harda masu kuka, kaunar Iffah kam da Shahan-shan din kansa ba’ magana a zukatansu. Sai sukejin kamar an yanta rayuwarsu ne da wani haske na musamman a yau din.
Ba cikin masarautar ruman kawal ba. A cikin al’ummar. kasa ma duk wanda ALLAH ya tsaga da rabonsa a kayan’ nan ya tsinta kansa a farin ciki mara musall. Badai ta wadata kowa da kowa ba. Amma ta ragema was radadin talaucin da suke ciki. Ta faranta
ran marayu marasa iyaye. Duk da alkairi ne na sirrince da akaki bama yan jarida damar sani sai gashi ya fita karar wata amsa kuwwa a katafen yada labarai, Ya koma latest topic na wanna ranar harma da washe gari. Dan cikin aminci, UBANGIJI a ranar akaga watan salla washe gari aka tashi da farin cikin zagayowar wanna rana. Inda karfe tara dal-dai Shahan-shan da Kansa ya jagoranci sallar idi a massalacin Masarautar da mutane kasar suka ziyarta ta ko’ina a jar, harma abin ya bada mamaki, dan duk da ana cikashi dama duk shekara sai gashi a wannan shekarar ya ninka da ninki mai ban mamaki,. Talakawa da yawa sunzo cikin Dahab City yin salla domin kawai suga Shahan-shan.(Haka rayuwa take, duk kasancewarka mai mugun hali ko wanda za’a gogama bakin fenti da kayi alkairin da yay shura tsakaninka da ALLAH badan duniya ta gani ta fada ba ko a yaba maka sai kaga ALLAH ya saka soyayyarka a zukatan wadan nan mutanen dake aibantaka da kyararka a baya. Yan uwa mu dage da alkairi domin ALLAH, idan ka cire Naira dari a cikin dubu da ya baka sai ya sakama sauran albarka ya kuma daga darajarka. Dan shi alkairi da gaske danko ne baya faduwa kasa banza inji hausawa. Dan ko yayan cikinka kaima shi sake kaunarka suke, hakama iyayenka)
Tajwar Eshaan yayi addu’oi masu ratsa zukatan bayan idar da salla. Hakama lokacin khuduba kalamansa masu ratsa zukata ne da hikima a cikinsu da mutare duk jikinsu yay sanyi da yanda suke kallonsa a baya. Bayan kuma kammala addu’oin yay wani dan gajeren nasiha da Fatan alheri ga kasarsa da ma al’ummar kasar da musulman duniya baki daya. Ya rufe da musu Barka da shan ruwa.
Wannan jawabi a Tajwar Eshaan Ibn Haysarn Abdul-majeed Ally Qutb shine ya dinga amsa kuwwa a kafafen yada labarai, masu fashin baki nayl talakawan kasa da basu samu halarta ba nayin nasu suma,
*Duk gayun da Iffah taci domin kayatar da zuciyar Maleek dinta bata samu ganinsa ba har sallar zuhur. Bataji haushi ba, sal dal ta kagu su hadun. Duk da itama da kanta tai masa shirin fita sallar. Yayi matukar kyau kamar wani dan saurayin dawusu (lols ๐๐)) harda fada masa ita why kamarma ya fasa kishin fitarsa a kalle mata shi takeyi haka. Amintaccensa da ke jinsu (okacin da take bashi shayi sai kasa ya karayi da kansa kawai yana murmushi.
Bayan ta idar da sallar azhar ta fito domin zuwa gaida Jaddah da Malikat Bushirat da ya kasance dole tayi. Sai lokacin ta fahimci yanda masarautar ke cike. Ashe dole ne duk wani Tajwar a sauran jihohi sai yazo a yau din yayma Shahan-shan barka da shan ruwa, Hakama manyan attajirat da masu fada ajin kasar da dattijai. Zasuci abincin salla da Shahan-shan su kuma tattauna matsalolin kasa da shawarwarin magancewa. Gaba daya sai Iffah taji ta Kara tausaya masa. Dan lallai mulki ba wasa ba, yanda ta sanshi bal son hayaniyar nan yana can cikin takura ne.