Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 137

Sponsored links

Idanunsa kawai ya lumshe a zahiri, maimakon ita da ke kuka a bayyane shi a zuciya yake yin nasan. Tabbas yaga ribar hakuri, kai shi baima san mizaice da UBANGIJI ba akan kyautar wanna yarinya da ya bashi. Ita din ta dabance. Tabbas itace komansa. Tsam-tsam ya rungumeta a jikinsa na tsawon lokaci, sal da ya ji tana sauke numfashi a hankali alamar barci ya dauketa sannan ya dagota. Kwantar da ita yay a hankali ya cigaba da kalionta hannunsa saman shafaffen cikinta da kamar babu komai a cikinsa abubuwa da yawa na masa kaikawo tun daga randa ya fara ganinta soyayyar farat daya ta shigesa har zuwa yau da ajiyar gudan jininsa ke à cikin jininta

 

69

…..WASHE GARI ta kasance ranar da zasu koma kasar ruman. Da safe bayan Tajwar Eshaan ya gama ganawa da Sultan na saudiya sunyi sallama amintaccensa da

 

Sayeed Tasadduq-Husain da sai daga baya yazo ya samesu a saudiyyan da wasu mutane biyu suka samesa. Cikin girmamawa suka mika gaisuwa, kafin Sayeed Tasadduq-Husain ya mika ma Amintaccensa file din hannunsa. Amsa yay da sauri yaje gaban Tajwar Eshaan din shima ya ajiye.

 

 

“Wannan shine result din binciken ALLAH ya kara ma adalin shugabanmu lafiya da nisan kwana. Sannan wadan nan sune sukai binciken. Sun kuma kasance kwararrun likitoci ta wanna fanin”.

 

 

 

Da sauri daya a cikinsu ya karbe zancen Sayeed Tasadduq-Husain din cikin harshen turanci, “Idan mukai bincike so daya ba’a samun kuskure, amma domin cire tantama sai da mukai wanna sau uku. Abu daya yake tabbatar mana shi namijin mahaifinta ne, mace kuma ba ita ta haifeta ba. Bayan muni sau uku mun sake bayarwa was asibitocin ga results din nan dai duk abu guda suke bayarwa”.

 

 

 

Baice komai ba, sai amintaccensa ne ya amsa da

 

yawunsa. Da ga haka sukai masa sallama Sayeed Tasadduq-Husain yay musu rakkiya. Duk abinda akeyi Iffah na daga kofar falo na biyu ne tsaye zata fito zuwa sashen Uwargidan Sultan da zasuyi sallama. Duk da bata san manufar zancen ba sai duk taji ta tsargu, amma kasancewar yanzu an koyi wasu halaye musamman akan hadiye abu koda ta fito wucewarta kawai tavi tunda yasan da fitar tata.. Koda taje can kuma abun nata mata kaikawo har tana jin kwadayin son sanin abinda ke a tattare da file din da son sanin akan wama ake maganar da har sai anzo wata kasa za’ai binciken bayan kowa yasan kasar su suna daya a cikin masu kwararrun likitoci a duniya. Sai kuma a ka kara yin sa’a lokacin da take dawowa sashen ta samu Sayeed Tasaddug-Husain da Tajwar Eshaan din suna maganar again. Cikin kasaitar nan tasa da magana a fisge yake sanar masa. “Ayi musu komai da ya dace, nan da kwanaki biyar bayan anyi salla sai ku biyo bayanmu, dan ina son ku iso ne randa zamu koma zaman shari’ar”.

“Umarninka da cikawa shine abin jiranmu Insha ALLAHU”

 

 

 

Iya abinda Iffah kenan ta iya ji ta shige. Lokacin da ya shigo dakin zai shirya tata fatan ya shigo da file din amma sai ya shigo babu komai. Kuma bai mata maganar ba. Amma koda suka kammala shirinsu suka fito Sultan da kansa yau ma da yayansa maza biyu da uwargidansa sukai musu rakkiya har airport Iffah harda kwallarta hakama Uwargidan Sultan abinka da sabon mata bayan shigarsu jirgi sun zauna tana a jikinsa yana lallashinta sai ga file din nan ajiye a gefensa. Ta danyi mamaki amma sai ta basar, sai dai zuciyarta na sake tabbatar mata da koma akan wa file din ya kunsa yanada matukar muhimmanci ga mijin nata. Jirginsu na dagawa babu dadewa barci ya kwasheta……

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button