Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 137

Sponsored links

ita Iffah sai ma abin nasu ya bata mamaki da dariya,ta kal dubanta ga Tajwar Eshaan da yay zaman kasaitar nan tasa. Cikin langabe kai ta masa magana da ido alamar wai mike faruwa? Dauke kansa yay gefe a ransa shi kadal yasan miyake ji na farin ciki, ya kagara doctor din tace wani abu. Amma a zahiri baka isa fassara abinda ke ko”a kan fuskarsa ba balle zuciyarsa. Doctor da tai yan gwaje-gwajenta a gabansu abinka da gidan manya ta dago tana murmushi, cikin girmamawa ta fuskarci uwargidan Sultan ta mika takardar da tai yan rubuce-rubuce

“Ya ALLAH”

Uwargidan Sultan ta fada fuskarta da kayataccen

murmushi. Ta kai dubanta ga Tajwar Eshaan da ke jin kamar ya fisgo takardan hanuntan amma ya dake a zahiri. “Ina mai farin cikin kasancewa ta biyu bayan doctor akan sanar muku samun karuwa da mukai, ALLAH ya sauki Zawjata-almilk lafiya”. Wani irin lumshe idanunsa yay da sauke sassanyar ajiyar zuciya kamar wanda aka zarema numfashi. Yayinda Iffah tai fakare tana kallonsu cikin rashin fahimta sam. Dan ita kanta ma sat ya toshe kawai a wanna gabar. Har suka gara bidironsu Uwargidan Sultan ta wuce bata iya tofa komai ba..

Wani irin dagata yay bayan ficewar kowa a falon ya shiga juyi da ita. Kawal ita sal abin ma ya bata dariya ta shiga kyalkyalawa. Bai hakura ya direta ba sai da yaga ta fara date kal alamar jujuyatan da yake akwai matsala. A tare suka dinga sauke numfashi, ya tsareta da idanun nan nasa masu kaifi ga kayataccen murmushi mai matukar tada da yakan dace baka gani a fuskarsa ba, Sal dal kuma a zahirance bakin ya gagara cewa komai. Sal da ya mula dan kansa a hankali ya furta “Mrs Eshaan kin mallakeni da komal na. Da gaske fa ni din bawanki ne”. Da sauri tasa hannu ta rufe bakinsa tana zaro idanu da girgiza kanta. Cikin rawar murya kamar mai shirin sake masa kuka ta ce, “Please Sultan ka daina fadar haka karma yan kasar ruman suji sumin yankan rago. Kai fa shugabana ne, sannan ashekaru ka fini, gaka mijina,uban yayana”, Hawayen suka silalo mata a hankali. Hannunsa ta kamo ta daura akan cikinta. “Nagodema ALLAH da ka kasance mahaifinsu badan ya baka daukakar mulki data dukiya ba. Domin su a duniya aka samar mana da su a cikinta kuma zamu tati mu bari wataran. Ina alfahari da kai ne matsayin uban yayana saboda nagartarka da adalcinka. Tsoron ALLAHn ka da kyakylyawar zuciyarka. Maleek kai na dabanne a cikin daban. Ba yan kasar ruman bane kawal suka dace a dalm shugaba ba. Daular musulunci ma kai abin alfaharinta ne. Sannan kuma nice kololuwar dacewa da ka kasance miji gareni, Nauyin mulki bai sa ka gaza bani farin ciki da sauke duk wasu hakkokina ba. Kana samar da nishadi a tsakaninmu ka manta da kai sarki ne mai jagorantar talakawan kasa bawai jaha ko wani dan yanki ba,

Kwanciyar hankalin da nake samu da ga gareka bana jin wasu matan da mazansu basu da nauyin kowa na sarun makamancin sa. Maleek kai ne gwarzo na, kai ne Barde na, kuma kaine gagara badau dina”.

Idanunsa kawai ya lumshe a zahiri, maimakon ita da ke kuka a bayyane shi a zuciya yake yin nasan. Tabbas yaga ribar hakuri, kai shi baima san mizaice da UBANGIJI ba akan kyautar wanna yarinya da ya bashi. Ita din ta dabance. Tabbas itace komansa. Tsam-tsam ya rungumeta a jikinsa na tsawon lokaci, sal da ya ji tana sauke numfashi a hankali alamar barci ya dauketa sannan ya dagota. Kwantar da ita yay a hankali ya cigaba da kalionta hannunsa saman shafaffen cikinta da kamar babu komai a cikinsa abubuwa da yawa na masa kaikawo tun daga randa ya fara ganinta soyayyar farat daya ta shigesa har zuwa yau da ajiyar gudan jininsa ke à cikin jininta…

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button