Daudar Gora Book 2 Page 131
.”UBANGIJI ya halicceki mace bayan akwai maza da yawa dake kwaikwayo son zama macen amma basu isa komawa ba. Ya halicceki kyakykyawa, bayan awai wasu da yawa da kyawun da bai kai naki ba suke
fafutukar nema ta hanyar sabama UBANGIJI suna amfani da abinda yace haramunne garesu. Ya baki lafiyar jiki babu ta inda kika nakasa. Bayan ga dubunki can su nakasar itace jarabawarsu. Ya baki lafiya
matsayinki na yar adam. Bayan ga dubunki can kwance a asibitoci da gidaje basu da kudin shan magani, masu kudin ma basu isa iya sayawa kansu lafiya ba koda sun kai karuna dukiya. Ya azurtaki cikin nagartaccen addini, bayan ga dubunki can na bautar wanin ALLAH cikin batan da su a karan kansu basu san bata bane ba. Ya azurtaki da tarin dukiya. Bayan akwai dubunki da abincin yini daya ma gagararsu yake ci saboda basu da kwabo na saya. Ya azurtaki a cikin katon gidan aure dana haihuwa, karkashin kyakykyawar nasaba bayan akwai dubunki da a kan titi ko cikin bukka suke rayuwa badan kin fisu ba. Ya azurtaki da karfin iko na mulki, bayan akwai dubunki da su wanna matsayin naki suke kwadayon kaiwa, ke wasu ace ma su din hadimanki ne kawai farin ciki yake sanyasu. Ya azurtaki da ilimin addini dana zamani, bayan akwai dubunki da suke zagaye da jahilci, wasu ko suna son karatun rashin mai tallafa musu Yasa suka hakura suka zama masu aikata miyagun laifuka koda zukatansu basa so, sai dai basu iya banbance abinda ya dace da wanda zai dace da tasu rayuwar. Ya azurtaki da da daya tilo tamkar da dubu da nagartaccen mijin da duniya bazata taba mantawa da su ba, bayan akwai mata da yawa da su jarabawarsu mazajen aurensu ne da yayan da suka haifa. Duk da ya miki wadannan abubuwane badan kinfi sauran halittun duniya ba. Badan bazai dandana miki mutuwa ba. Badan bazai iya jaraftarki ki kasance su ba. Badan kinfi karfinsa ba. Sai dan kawai ya miki talala har zuwa ranar da zaki tabbatar ke din bakomai bace a cikin komai. Ke din yar adam ce, yar adam din nan da aka halitta da ga yunbun kasa, yar adam din nan mai rauni, mai barci, mai kashi, mai ciwo mai jiran kwanakin mutuwa. Badan kiyi alfahari da duk wadan nan abubuwan ba kuma ya halicceki, ya baki su ne domin jarabawaki itace su, kamar yanda ya bama wasu sabanin naki domin jarabawa suma. Dan ALLAH mi kike bukata a bayan duk wadannan?
Kamar yanda ni na kawo kaina masarautar nan bake kika kawoni ba. Kamar yanda ni nai amfani da Arshaan da Jasim da Haifah basu sukai amfani da ni ba, ke shaidace kuma ga irin makomar da suka kasance duk da somin tabi ne ma na fara musu.Kamar yanda ni na bama Shahan-shan din da kike takamar da shi garkuwa bashi ya bani ba har kike hakilo da hura hancin wai ya janyeta gareni.Kin san ALLAH kiyi maza ki dawo hayyacinki ina tsoratar miki shiga jerin mutanen da zan kwancema zani a bainar nasi cikin Masarautar nan dank kuma ya musu hukunci, kiyi azamar ajiyewa ki labe bayan mutuncin danki hukuncina ya kasance tsakanin ni da ke ne kawai. Dan saura kiris a fara bankada, idan kuma aka fara akwai gagarumar matsala, dan na fahimci ke kanki har yanzu baki gama sanin wanene danki ba da ainahinsa, kinama rogo kallon kitsene kawai, sannan kina kallon kasurgumin Zaki ne da fatar mage” ta saki murmushi tare da takawa gabanta a hankali. Hannunta ta kamo ta daura saman cikinta, “Ina tayaki murna da albishir din insha ALLAHU kafin mu dawo daga hutun in amarcinmu da iznin UBANGIJI zamu dawo da jikanki a wannan babbar garkuwar, dan haka kibar wahal da kanki akan sai Maleek ya auro wadda kike son ta haifa miki shi dole ko nisanta shakuwar iyayensa da zata zama sanadin samar da shi ta hanyar madara. Da ga kuma randa kika tabbatar da samuwarsa, ki fara irga kwanakin nadamarki da dana sani har zuwa ranar haihuwarsa. Hukunci da karfin ikon Iffah a saman naki, yanzun ne zai fara Mother in-law”.