Daudar Gora Book 2 Page 119
sai dai was tsurface-tsurfacen tsafi da Uwa ta fara kawowa a kansa yasa nace a kaisan, ta
nuna bakin cikinta sosai akan hakan da nayi, har tai gargadi mai girma akaina da cewarta ni na
cika shiga mata hanci ni da zuri’ata. Sam wani kurarinta da tsubbace-tsubacenta basa bani
toro, dan da UBANGIJI NAna dogara akoda yaushe. Dan haka na cigaba da dagewa har sai
da Tajwar Abdul-majeed ya yarda aka kaisa kasar Cuba. Haukane kawai Uwa da Bushirat
basuyi ba, sai dai kamar ALLAH ya saka tsorona ne a zukatansu ni ban sani ba. Dan duk
hatsabibancin uwa iyakarta borenta a kaina a bayan idonane, taci alwashi sosai a kaina dalilin
dauke Eshaan har ma abin ya dinga daure mun kai amma sai na daukesa aikin banza dan bata
isa mun abinda bai kasance jarabawata ba. Komai ya lafa kowa ya cigaba da harkokinsa aka shiga watan azumin ramadan. Azumi nada
kwanaki bakwai sai Tajwar Abdul-majeed ya sameni akan zan masa rakkiya ya duba Eshaan da ga can muje umrah da shi bayan salla sai mu
maidasa Cuba mu dawo gida. Ban kawo komai a raina ba na shirya mukai wannan tafiya har da Haysam. Munyi-munyi Ammarah ta bimu taki,
ashe lokacin ta samu wani saurayi ne ya kuma mata alkawarin dinga zuwa shan ruwa wajenta. Sai da na nuna bacin raina kan rashin son binmu 12:47
Sai da na nuna bacin raina kan rashin son binmu a zatona bata son taje ne su hadu da yar uwarta, sai da ta zauna ta fahimtar dani. Naji dadi sosai, dan tace tana son bashi damane ta karanci halayyarsa anay in bikin sallah ai aurensu
kawai. Muni farin ciki da hakan, mun kuma mata fatan alkairi.”
“‘Tafiyarmu itace mafarin kaddarar Ammarah,sannan itace mafarin yakice uwa da ga wannan zuri’ ar, sannan itace mafarin yin kuka garemu
dama duk al’ummar kasar ruman, sannan itace mafarin hawan Haysam karagar mulki matsayin
madadi ga mahaifinsa. Bayan wucewarmu umarah, bisa yarjewar Jasim UWA ta sakasu yin yankan nan dai dana sa Tajwar Abdul-majeed bijire mata akansa, ta kuma basu umarnin daura auren daya daga cikin kannensu da wani bawa
ko cikin talakawan gari. Son zuciya da sanin makomar dan da ake so a samar ko ya ta
wannan hanyar suka aurar da Ammarah ga dan mai dinka kayan dokin masarautar, domin a
ranar sunzo kawo kayan kwalliyar dokuna na bikin al’ada dake tunkarowa. Babu waya a
lokacin balle ta sanar mana ko wani ya sanar mana,hasalima sunyi auren ne a sirrance sai ita
da suka dauka suka kai wa yaron bisa tirsasashi Ya kusanceta in ba hakaba zasu kashe dukkan
ahalinsa da shi kansa. Dolene ya tsorata ya aikata abinda suke bukata yana kuka itama
tanayi. Shi UBANG|JI mai hikima ne, sun taya ya kuma isar musu bisa ikonsa, badan baya son
Ammarah da wannan bawan ALLAH bane, ba kuma dan yana son nuna Uwa a saman kokarin
mu bane. A’a wannan itace kaddararsu. Kuma ALLAH ya rubuta sai an samar da wannan abun haihuwar ta wannan hanyar. Sai dai alhmallh, ina godema ALLAH da sake gode masa, dan kuwa koba komai ta hanyar biyan sadaki da sheda aure abinda ya farun ya faru. Mun dawo muka
tadda Ammarah a wani irin yanayi, dan kuwa ta birkice musu matuka, a lokacin kowa ya sake
tabbatar da iska a tare da ita. Muni kuka ni da Mahaifinsu da dan uwanta sosai, mahaifinsu
kuma ya fusata a wannan karon har ya kulle Jasim a kurkuku tare da duk wanda suka goya
masa baya akan aikata aikin, yayi kiranyen uwa amma taki zuwa, an sa malamai domin mata
kiranye nanma taki zuwa. Har takai an hada da bokaye irinta amma amsa daya suke bamu tafi
karfinsu. Hankalinmu ya tashi matuka, musamman bayan wasu watanni da ciki ya bayyana ga Ammarah, gashi lafiya taki samuwa gareta, tama koma wata iri kamar mai ciwon
hauka, ta daina magana da kowa, sai kuka,abinci ma sai an tsaya kanta take ci.ALLAH ne kawai
ya zama kariya ga wannan ciki har zuwa ranar haihuwarsa. Tajwar Abdul-majeed ya sakka
a nemo masa mijin da suka aura matan, sai dai anje ba’a dace da samunsu ba, wai sun bar asalin kauyensu a wani dare. Iya nema da bincike kuma ba’a dace ba dole aka hakura. A daren wata juma’a ALLAH ya sauki Ammarah
lafiya, sai dai tasha matukar wahala kafin ALLAH ya kawo haihuwar. Ta haifo yarinyarta mace kyakykyawa, sai dai babu ta inda take kama da ita sai tambarin tabon tawadar ALLAH da zuri’ar wannan gida ke da ita, bamu san mahaifinta ba kuma balle musan ko da shi take kamar. Mun amsheta hannu biyu, sai dai zagaye take da addu’ar neman kariyar UBANGIJI da ga sharrin uwa. A randa aka haifi yarinyar a ranar ALLAH ya