Daudar Gora Book 2 Page 117
.”Labarin ya fara ne tun zamanin iyaye da kakanni da ya kasance akwai karancin ilimin addini. Ba a daular ruman kawai ba hatta da sauran dauloli da ma talakawan kasar RUMAN kowa yasan ani matukar imani da tsafe-tsafe a karnikan da suka shude. Zaki
samu duk talaucin mutum duk yawan arzikinsa yanada wani boka da ke fada masa motsinsa ko wani abu dake tunkarosa, ko bashi Sa’a a abinda zai yi ko yake yi. A lokacin da addinin musulunci ya fara kutsowa cikin wanna kasa tamu idan akaji ka amsa sai an halaka ka, dan kuma kai shugaba ne to fa za’a tubeka a koreka kai da duk ahalinka. ALLAH sarki, masu shiga musulunci da masu hidimar gain an shiga sunsha matukar wahala a wancan karnin. Komai ya canja da cajawar labarin wanna kasa dalilin wani fari da akai na tashin hankali, ruwan dake zagaye da wannan tsuburi da kasar RUMAN take ya zagaye komai hadda gidaje da dukiyiyi har ma da rayuka. Ba kasar ruman ce kawai ta girgiza ba, Africa da ma duniya baki daya wannan al’amari ya matukar girgizasu, inda aka shiga kawo mana dauki ta kowane bangare. Wannan shine mafarin fara samun canji, domin a cikin wanna yanayin ne tarin bayin ALLAH mabiya addinai daban-daban suka fara yakin ganin sunja ra’ayoyin mutane da dukiyoyi da wasu abubuwan kyale-kyale na duniya, harda masu yimusu tayin binsu kasashensu suyi rayuwa.
Babu mai son yabar kasarsa tushensa dan haka mutane suka fara bijirewa, sai ko wani bawan
ALLAH ya basu goyon baya mai suna SHEHU UTHMAN DAN-FODIYO da ga kasar NIGERIA.
shine ya tabbatar musu kasarsu itace yancinsu, itace gatansu, itace martabarsu, su tashi da
karfin kwanji su gyarata yayi alkawarin tallafa musu da karfin jiki da ga tawagarsa. Zantukansa
sun kayatar da kowa sun saka karsashi a jikin mutane, musamman yarima mai jiran gado Miran Aliy Qutb. Ganinfa Miran Aliy Qutb ya amshi wannan tunatarwa tun ya samu mabiya.
Abu mafi daukar hankalin mutane SHEHU UTHMAN DAN-FODIYO ya kasance MUSULMI
ne, hakama almajuransa da sukayi masa rakkiya, amma sai bai taba cema wani dole sai
ya shiga addininsa ba ko masa tayi da wata dukiyar da zai shigan, ya dage dai tukuri da
taimakonsu yana ibadarsa. Hakan sai ya shiga birge mutane tuni suka fara karbar musulinci.
Sai kuma cikin kankanin lokaci kasashen musulunci manya irinsu Saudi Arabia suma suka
fara yunkurowa, mabiya addinin islam suka hada karfi da karfe wajen hidimtawa wanna kasa ta
RUMAN ta sake ginuwa ta komawa kan kafafunta. A cikin abinda bai wuce shekaru
kalilan ba abubuwa suka cigaba da canjawa acewar munada tarin tattalin arziki ka davan-daban. An dauki babban mataki akar
ruwan dake zagaye da mu, aka kuma kara fadada kasar ilimin addini ya yawaita, kafirci ya
fara nisa a cikin al’ummar mu. Masu bautar gumaka da yin imani da bokaye duk suka fara
janye jiki, wasu bokayen ma da kansu suka dinga ajiye kayan tsafe-tsafen suma suka koma
ga ALLAH. Masu taurin kan cikinsu kuwa sai suka bijire da jan tunga, wasun su suka koma