Daudar Gora Book 2 Page 111
Wata irin wawuyar ajiyar zuciya Malikat Bushirat ta sauke. Gaba daya sai taji abinda ya tsaya matan a makoshi ya fada a cikin cikinta.Dari bisa dari ta yarda da zancen uwa, dan bata taba mata karya ba (hummmm). Fuskarta dauke da murmushi ta sake gurfana a gabanta. “Yanzu kam na fahimta, na fahimci komai uwa. Dama ni nasan bazaki bari na fadì ba. Amma naso ace kin sanar min tuni, da sai na daidaita rayuwa jasim,sai na kafa tarihi akansa irin wanda harara wani bazai sake kwatantawa ga Saiful- malik dina ba a wanna masarautar”
Wani irin shegen dariya uwa ta kwashe da shi.”K yar halak ce ta-kurya, shiyyasa nake sonki fiye da duk wanda ya kasance a karkashin baiwata. Na miki alkawarin bazaki sake yin kuka ba, zan cigaba da tsaya miki fiye da tsayawar da nai miki a baya. Zan cigaba da kare Ajlaan fiye da kariyar da kike tunanin yana da (Wa”iyazubillah. Ya rabba ka tsaremu da aikata shirka koda a cikin duhun jahilci ne @ A). Zan baki mamaki, tabbas zan baki mamaki ta-kurya”.
“A kullum cikin bani mamaki kike ai uwa, shiyyasa bazan gaji da fada ba, bazan gaji da maimaitawa ba ke ta dabance a cikin daban”.
A wani bala’ in firgice ta farka da ga barcin da ya figeta bayan idar da sallar azhar. Kanta dake wani irin sara mata ta dafe tana ambaton sunan ALLAH. Ta kai tsahon minti uku a haka kafin ta mike daga saman sallayar da anan barcin ya kwasheta. Gaba daya jikinta tsuma yake, yayinda zuciyarta ke mata tariyar mafarkin nata dalla-dalla. Jin jiri na neman zubdata kasa tai saurin zubewa bakin gado tana sake dafe kai. A hankali ta furta, “Uwa!! Wacece ita? Ta ina zan fara bincike saninta”,. Kantane ya sake sara mata, tunda take mafarke-mafarkenta bata taba mai nauyi irin wannan ba. Duk da bataga fuskar wadda ke zaune a kujerar karfen nan ba zagaye da wasu irin munanan halittu taji a ranta dole ta kasance abar toro. Sai kuma gain Malikat Bushirat da tai a gabanta dirkushe, shin minene hadin Malikat din da wadan nan munanan hallitun? Tajwar Eshaan a gefe daddaure da wasu irin igiyoyi wuta, sai dai shima bata ganin fuskarsa amma tana iya jin yanda yake ambaton sunayen ALLAH radam.
Dagowa tai da sauri dan sam bata san da shigowarsa cikin dakin ba, hasalima bata san ya dawo ba. Idanunta data kafeshi da su ta dan janye tana kara tsarkake sunan UBANGIJI mahaliccin wannan bawa. Komai nasa mai kyau ne da birgewa. Hatta kayan zaman gida dan ya saka badan kwalliya ba sai su fidda cikar kamalarsa da zati.
Ta fada kanta a kasa dan kallon nan nasa na kasa-kasa da ke daburta mata lissafi bata son shi. (Aljanun sunzo kenan) ya fada a zuciyarsa yana wani dan yamutsa fuska. A zahiri kam baice komai ba ya dai cigaba da kallonta. Kusan minti daya sannan ya motsa da cigaba da takawa a hankali cike da kasaitar nan tasa. A gabanta yaja ya tsaya, tare da zare hannunsa dake cikin aljihun wandon jeans dinsa ya mika mata. Idanunta ta dago ta kalli hannun da ke fari tas da shi, ga jini nata kaikawo a tafin kamar ba namiji ba. Idanunsa ya dan lumshe da budewa a lokaci guda yana gyada mata kai alamar ta daura nata. Kamar mai jin tsoron hakan ta dago natan ta dora a cikin nasan. Sake lumshe idanun vavi kamar wani wanda maganadisu va taba.
din akwai wani kenan. To miyasa ta boye? Bashi da mai basa amsa baya kuma bukatar sonji gareta yanzu dan ransa duk babu dadi yake ji. Itama da kanta ta fahimci hakan, dan fuskarsa a tsuke take fiye da sanda suka fita kotun. Sai duk take jin kuma babu dadi. Dan haka kawai take jin tausayinsa. Idan har zai shiga damuwa saboda halin wancan karen uncle din nasa, yaya zai kasance kuma a randa zai san mahaifiyarsada kanta ke halaka masa matan aurensa da duniya ke kallonsa a mai halakasu tsahon shekaru. Kai kai wannan al’amarin fa na taba mata zuciya why sosai matuka. Ajiyar zuciya ta dan sauke a hankali, sai kuma ta kai hanunta saman lallausan gashin sajen fuskarsa ta shafa. Murya can ciki ta ce, “Kayi hakuri? Ka amsa da hannu biyu jarabawace. Badan UBANGIJI baya sonka ba ya jarabeka da su. Shi kansa mulkin ma da kake kai ai jarabawa ce. Kai numfashinmu ma kansa jarabawace a garemu, dan UBANGIJI ya azurtamu da shine domin yaga zamu kasance masu bin dokokinsa ne ko kuwa masu bijire masa”.