Hausa Novels and Stories

Zafin Kai 2

Sponsored links

Samirah ta rasu ne bayan da azabar tayi masu yawa ta girmi tinani da dauriyarsu harma da duk jarumtar da suke tinanin sunada ita,

Cikin tsakiyar dare guraren karfe uku na dare ta fita dan guduwa bayan ta tabbatarda a lokacin bacci mai karfi yake daukan Ababa sbd yawanci yana kaiwa karfe daya koma harda mintina kafin yayi bacci sbd babu daren da baya lissafin dan arzikinsa da kuma lissafin yanda zaiyi da rayuwarsu kota hanyar siyarwa kota hanyar samun masu kudin da suka amsa sunan asalin masu kudi su auresu koda a matsayin matan biyan buqata ne kawai shi dai idan zasu fita rayuwarsa amma a dayan bangaren tinaninsa shine karatun daya sakasu sbd idan har bai fanshe komai nasa a gurin masu fataucinsu ba to tabbas dole idan masu dollars ne zasu auresu kota tsiya yasan dole ana buqatan ilimin boko da ‘yar wayewar ilimin a tare dasu kafin su shige.

A daren kwanon abinci daya suka samu su dukansu wanda dukkaninsu loma bibbiyu sukai suka barwa mahaifiyarsu sauran sbd karfinta na shekaru da wahala ta cinye,

A cikinsu yanzu Annen tasu ta zama tamkar itace qaramar kanwarsu gabaki daya sbd kowannensu tausayinta yake ji fiyeda junansu,

Tafi su gazawa,

Tafisu jigata hakama tafisu buqatan abinci a koda yaushe aka basu din sbd rauninta.

Samirah a cikinsu ta kasance batai jin qan sauran ba sbd a koda yaushe indai zasuyiwa ‘dayansu sacrifice na wani abun itace take kasawa shiyasa koyaushe batada burin guduwa daga wannan rayuwar mai kama data fataucin bayi,

 

Burin guduwa da tserewa mahaifinsu yasa abin ya zauna a ranta har kusan ta shafawa Safnah kwadayin guduwa daga wannan masifar dasuke kira da rayuwar gidan ubansu

Yunwa,azabar zafi data sauro daya zama tamkar bugun numfashinsu sbd babu yanda zaayi su kwana su tashi batareda sauro fiyeda dari a dakinsuba sakamakon rashin kofa sai labule windon dakinma kusan dan kada su gudun ne ko barayi su shigo ta nan su masa sata a gidan yasa ya saka musu sbd yana ta bayan gidan ne windon.

Tashi zaune samirah tayi ahankali daga kwancen datake gefen mahaifiyarsu akan babbar tabarmarsu dasuke kwana zube akai kaman an shanya su,

Annenta ta zubawa ido Ahankali jikinta na mutuwa tareda karayar zuciya da tsananin kaunarta da tausayinta na yanda zataji a matsayinta na uwa idan aka wayi gari babuta ta bata ta shiga duniyar da Anne da yan uwanta basu saniba ko zasu sake haduwa har abada,

Hawaye masu zafi ne suka gangaro mata sbd tinanin azabar da zasu iya sha daga mahaifin nasu akan guduwarta saidai bazata iya zama a cikin wannan rayuwar ba sbd tsoron dake zukatansu wadda mahaifinsu ya saka musu kawai zata iya kashesu kokuma su qare da juyayyar qwaqwalwa kaman mahaifiyarsu wadda ta zama ita da qaramin yaro wani lokacin banbancin kadan ne.

Hannuwanta ta daga Ahankali ta kallo tafin hannuwanta dake a cabe suna wani irin ruwa sbd azabar ruwan zafin da akai mata a jiya

Ta tabbatarda zata rube a hakan a yanke hannuwan kokuma ta warke amma bazaa taba kallonta a nuna an mata hukuncin ba bare a neman mata magani,

Zata gudu tabar gida koda yan uwanta da Annensu zasu samu ragin mutum daya abincinda ake basu ya dan qara yawa a cikinsu sbd tasani har abada idan har a gidan zasuyi rayuwa bazasu taba cin abincin da zasu qoshiba,

Qin da Ababa yayi musu zuwa gaba lokaci yakuma ja yaga baida mafita komaima zai iyayi dan ya kawai dasu daga gabansa ciki kuwa zata iya cewa harda kashewa dan karfin ransa da taurinsa babu kowane kalar tausayi ko imani acikinsa,

 

Abu daya ke karyar da taurin ransa da girmansa shine kudi,

 

Bai hada komai da dukiyarsa ba wadda idan ana maganar masu dukiya baya cikin layi ko kusa amma kaman yanda yake fada kowa da nasa yake tinkaho,

 

Baya roko,baya daukan reni a gurin kowa sbd a ganinsa babu mai kudin da zai iya basa irin kudin dayakeso sbd shi a gurinsa masu lissafi da dollers din America sune masu kudin gaske dasuke isa su fada ya saurara.

Bin ‘yan uwanta tayi da kallo daya bayan daya hawayenta na sake gangarowa da dumi mai zafi tana sake kallon yanda kowannensu yake fidda wahalallen numfashin dake fitowa daqyar sbd yunwa amma a hakan suke bacci kaman jarirai da basusan matsalar komaiba tsaban tawakalli da rungumar rayuwar da Allah ya jarabcesu da ita.

Kan benazir da zatafi kowa daukan wahalarsa ta tsaida idanuwanta tana jin tausayinta sbd azabarta tafi ta kowannensu akoda yaushe amma Allah zai duba lamarinta da sauran yan uwan da mahaifiyarsu wadda guduwanta saiya taba Annen sosai.

Tana numfashi da qyar ta fito daga dakin ta tsaya tsakar gidan ta saki wani wahalallan numfashi mai dumi da azaba hawayenta na kasa gangarowa daga idanuwanta dasukai ja.

 

 

 

Safnah dake rabe bakin kofa daga cikin dakinsu tana hango samirah din taga komai ya tafi daidai ta fito sake tsayuwa tayi daga cikin dakin tana dan sake ziro kanta kadan dan kafarta bazata sako tsakar gidanba dan hakan kawai zai iya sakata rasa qafafunta idan Ababa ya kamasu gashi tana ganin dakin Hande da samirah din ta bari a bude wanda iska da sanyi zai iya farkar da ita taganta amma bazata iya fitowa tace mata ta rufe dakinba dan ta zabi ta boye kanta ga wannan aikin dayake sunan siradin tsira kona halaka.

Kofa samirah ta nufa jikinta na rawa sosai sbd hannuwanta dasuka kasa riqe mukullan da kyau,

Hannu na wata irin rawa ta kamo katon padlock din dayafi karfin hannunta ta saka key din daqyar amma ta kasa saka karfi ta murda ya bude sbd hannuwanta dake jini gabaki daya wutar takoma mata sabuwa gashi duka hannuwan biyu,

Ninka tashi hankalinta yayi tareda wani irin firgitaccen tsoro dataji yana shigarta mai karfi a lokacin sbd kaddararren aikin tsautsayine da babu komawa baya sbd tariga ta barko barnar tunda ta sato mukullin gwara duk tsanani ta balle ta gudu akan Ababa ya risketa tabbas hannuwanta bazasu qara moruwaba kuma.

Yanda jikinta ke rawa yana jijjigar tsoro da firgici tareda tashin hankali mara misali yasata kofar da padlock da mukullan suka fara bada sauti mai karfi,

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button