Daudar Gora Book 2 Page 108
Shiru tai tana kallon wayar bayan ta yanke.Zuciyarta sai faman mata kaikawo take da tunani kala-kala. Sai kuma ta dage gira da dan tabe baki tana ajiye kan wayar ta mike. Ficewa tai da ga dakin ta nufi can saman ginin dan wajen na matukar kayatar da ita. Tana kaunarsa fiye da kowane waje a masarautar.
“Abu Harith kana lafiya kuwa? Tunda muka baro kotu ka kasa zaune ka kasa tsaye. Duk da dai nasan abinda dan uwanka ya aikata ga wannan bawan ALLAH dole ya tabaka, amma sai nake ga damuwar taka da rudanin kamar sunma fi na kowa. Ka tuna nima fa dan yar uwata ce dat rikeni tamkar uwa, sannan shugabanmu baki daya. Mu dukanmu ya sakamu muka haukace akan baiwar ALLAHr yarinyar nan da bataji ba bata gani ba. Why har kunyar haduwa da ita nakeji yanzu. ALLAH sarki Mammah tai ta son nuna mana gaskiya muna bijirewa, duk da
nuna mana gaskiya muna bijirewa, duk da ALLAH ne shaidata kai ne ka dinga kara tunzurani har idanuna sukai makancewar kasa hasashen komai gashi na kare da dana sani”
Kallonta kawai yake tana zabga zance ko hadiyar yawu batayi, bata san jima yake tamkar ya shakota ba tsabar takaici da takura masa da tai. Shifa shi kadai yasan irin kalar tashin hankali da rudanin da yake ciki akan al’amurin nan. Da farko yayi zaton hadiminsa na aikine bisa aikinsa na tsawon shekaru da ya daurasa a kai akan bibiyar dan uwansa, sai dai kallon da yarinyar nan Iffah tai masa sanda suke fitowa daga kotun ya matukar saka zuciyarsa neman bugawa. Idan har ya canka dai-dai lokacin da take shigewa *_Next.…_* ta rubuta masa akan iska fa. Wannan kalmar itace ta tsaya masa a zuciya taki fadawa sai faman kaiwa da komowa take…..
“Ya ilahi Abu Harith!!”.
Jasrah da ke hargowar kwala kiran sunansa ta katse masa tunani. Cikin bacin rai ya nuna mata kofa alamar ta fice masa. Rai bace take dubansa itama, har taji ta kasa hakuri ta ce,”Kamar ya na fita bayan kuma magana muke?Wai shin kodai kaima da naka kashin ne a jiki banda labari, dan wannan yanayin naka kam ya fara sakani a rudani..
“Jasrahhh!!!”.
Ya fada cikin karajin da ya sakata zabura. Cikin wata irin birkicewa da bata taba fuskanta da ga garesa ba ya sake nuna mata kofa. “Wihy idan baki fita min ba sai na kwashe fuskarki da maruka. Banza kawai kin dameni, ki barni naji da abinda ya isheni ban san wawanci”.
Ba karamin tsorata Jasrah tayi ba kam, dan wutar bala”i ta gano kuru-kuru cikin idanunsa da kan fuskarsa. Cike da sassarfa ta nufi hanyar fita ranta a bace da tsawar da yay mata…. Tana gama ficewa yaja wani shegen wawan tsaki da raka bayanta da harara ya ce,
“Tinkiya kawai, ban san damuwa”,. A wani irin zafafe ya koma jagwab cikin kujerar ya zauna yana dafe kansa da ke sara masa da karfin masifa. Dai-dai nan kira ya shigo wayarsa. Sharewa yay bai dauka ba har ta tsinke, sai kuma ga wani ya sake shigowa. Tsaki yaja da finciko wayar daga aljihu da niyar kashewa gaba daya yaci karo da sunan Ameera Haifah baro-baro. Kamar bazai daga ba nan ma sai kuma ya amsa a fusace da kaita kunnensa. “Ke kuma miye kike wani kirana a wannan lokacin bayan kin san mi ake ciki”.
Da ga can cikin muryar tashin hankali ta ce,”Dolene na kiraka Arshaan. Dan tabbas akwai matsala. Matsala babba why. Na kasa gane komai, ka saka zuciyata a rudani gaba daya game da abinda ka aikata a kotu. Shin mi hakan ke nufi? Taya komai da muka aikata mu ukkoma kansa shi kadai? Kai ne kai hakan kokuwa hatsabibin yaron can ne ya kulla mana gadar zare ta hanyar yar iskar yarinyar can. Wihy kaina ya kwance gaba daya, dan ALLAH ka zaba mana wajen haduwa yanzu da gaggawa kar zuciyata ta buga”