Daudar Gora Book 1 Page 98
Kasancewar Barrister Akeem ba baƙo bane na shigowa gidan masu hidima a gidan suka dinga gaidashi. Amsa musu Barrister Abdallah ya dingayi da fara’a da kuma muryar Barrister Akeem data zama yana
kwaikwaya a yanzu kamar yanda aka horar da shi. Ya iso katafaren falon da yaji komai na more rayuwar duniya, ga kamshi na tashi irin wanda aka san duk wani jinin ƙasar ruman da shi. Cikin girmamawa ya kai zaune fuskarsa da murmushi ya shiga gaida babban mutum ɗin dake zaune a falon cikin shigar kayan ƙasar na alfarma.
Da ƴar sakin fuska mutumin ya amsa masa da faɗin, “Barrister sai yau ake ganinka? Bayan kuma tun jiya nasa a sanar maka na dawo ƙasar”.
“Amun afuwa ranka ya daɗe, an ɗan samu wani tazgarone daya riƙeni a dalilin zaman da Boss namu ya kira, nayi zaton zamu tashi akan lokaci harna iso nan ɗin sai hakan bata yiwu ba, ganin dare yayi kawai na wuce gidan dan nasan kana bukatar hutu”.
“Hakane kam. Yaya aikin naku?”.
“Alhamdullh ranka ya daɗe munata bubbugawa”.
Murmushi mutumin yayi, sai kuma ya ɗan gyara zamansa da zuƙar shisha ɗin hanunsa yana gyaɗa kai. Shiru ya biyo baya kasancewar ɗaya daga cikin masu masa hidima ya kawo ma Barrister shayi. Sai da ya kammala ya fice mutumin ya ajiye marikin shisha ɗin da fesar da uban hayaƙin daya tara a bakinsa.
“Barrister dama ina maka wani neman gaggawa ne akan abokinka mai shegen taurin kai Barrister Abdallah Aas”.
“Tofa oga ya ƙara yin wani laifi ne?”.
“Kusan haka kam, dan akwai wani case na aminina dake a rufe sai ƙoƙarin ganin ya buɗosa yake yi. An masa gargaɗi kusan sau uku amma bai ji ba har sai da yajama kansa aka kauda shi kasan mutumin na ka da taurin kai”.
“Kauda shi kuma ranka ya daɗe?”.
Barrister ya faɗa cikin nuna rudanin as shine Barrister Akeem. Murmushi mutumin yayi irin nasu na manya yana ɗage kafaɗa alamar ko’a jikinsa. “To in basu kaudashi ba mi kake so suyi Barrister?. Yana da taurin kai ne gaskiya. Nasan dai kaji zancen tashin bomb ɗin can na jihar Hubab..?”
“Yes Yes ranka ya daɗe, ai kowa ma dake ƙasar nan yaji wannan baƙon al’amari mai tada hankali tunda bai taɓa faruwa ba a wannan ƙasa tamu……”
“To ga abokinka kam yaja ya faru, dan an tada wannan bomb ɗinne da shi kasancewar a cikin motarsa aka sakashi”.
A matuƙar razane Barrister ya furta “What! Ranka ya daɗe abokin nawa?”.
“Kaga kwantar min da hankalinka wannan ba wani abu bane. Sakamakonsa ya amsa a hannunsa. Kaga ko anan gaba masu shirin taurin kai irin nasa sai su kiyaye. Ba wannan ne abin damuwa bisa maƙasudin kiranka nan ba. Muna son ne ka maye gurbinsa a wancan case ɗin ne domin kwaso mana dukkan wasu bayanai da ya haɗa. Mun zaɓoka ne saboda kamaninku ɗaya, har yanzu kuma babu wanda yasan da shi bomb ɗin ya tashi. Kafin masu bincike su gama gano motarsa ce wadda bomb ɗin ya tashi a ciki muke bukatar ka kamla komai”.
Hannu ya ɗaga masa da sauri. “Karkace komai Barrister, nasan zafin rasashi kakeji, ina maka ta’aziyyar hakan. Sai dai ka sani, wanda ya ɓatar da shi kaima zai iya ɓaddaka kai da duk a halinka wannan yafi shan shayi sauƙi a garesa. Dan haka ka kula. Akwai saƙo na kafin alkalami a motar ka mu yini lafiya🙏”.
Hakan da yay na nufin ya sallamesa. Barrister Abdallah ya miƙe jiki a sanyaye. Gaba ɗaya tunaninsa ya rabu da zuciya da kwakwalwarsa. A yanzu kam ya gagara fahimtar komai gaskiya. Shin idan har waɗan nan ɗin sune mugaye a garesa, waɗan da kuma su yake bibiya a case ɗin su Babiy to sukuma waɗan da suka sakashi wannan aikin fa? Kenan fa kuɓutar da shi sukai a waccan ranar ko mi abinda sukai ɗin ke nufi? Ya ALLAH mike shirin faruwa da ni ni Abdallah?.
Ya tambayi kansa batare da yasan ina zai kama ba har ya ƙaraso jikin motarsa ya shiga. Da ƙyar ya iya tuƙin zuwa waje, yana hawa titi ɗan nesa da gidan aka dakatar da shi akan cewar yay parking ta cikin bluetooth ɗin kunnensa. Hakan ba karamin taimako bane a garesa, dan a yanda yake jinsa tabbas zai iya kife kansa a titin ma gaba ɗaya……..