Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 96

Sponsored links

Danne takaicinta tai ta sake sallamar, nan ma shiru dai babu ma alamar za’a amsa. Cikin suɓutar baki taja tsoki da faɗin. “Nifa a rayuwa na tsani walakanci wlhy, shiyyasa komai nafi yarda naima kaina. Yanzu haka wani ɗan iyan dake ƙarƙashin sa ya ɗaga kiran kamar waccan ranar dana fara kira, ƴan hana ruwa gudu kenan. Nima badan ƙaddarar faɗawa hannun wannan Dodon ba da yanzu ina can ina karatuna na jaridar a daina yarfani. Kai insha ALLAHU kafin naga bayan a azzalumin nan ko sau ɗaya ne sai na hau kujerar karagar mulkin nan nayi tankaɗe da rairaya cikin duk ƴan jaridar ƙasar nan da jami’an tsaro aikin banza……”

Jin kamar sautin fitar murmushi a kunenta ya sata saurin ciro wayar ta kalla. Dai-dai ana yanke wayar. Ido ta kwalalo waje da dafe bakin. Sai kuma ta janye da faɗin, “Kai kamarfa daga cikin wayar ne sautin nan ya fito wlhy. Kai ina”. Ta sake faɗa tana ɗan wawwaigawa babu dai alamar wani a ɗakin sai itan kaɗai. “Oh ni Iffah anya bakin nan nawa bazai yankani ba wataran, yanzu hakama shine yazo ya amshi wayar inata zuba ban sani ba”. Tai tagumi cikin takaicin kanta. Kamar kuma wadda aka ɗan zabura sai ta sake ɗaukar wayar. Cikin sa’a tai tozali da ganinsa online har an amsa mata sallamarta ma. Sai kuma ta shiga kokwanton tayi magana ko kawai ta share. Wata zuciya ta amsa mata da (Kema kin san bashi bane ya ɗaga miki waya. Ki basar kawai). Da alama ta gamsu da shawarar, dan haka ta saki murmushi da buɗe saƙon.

“Sorry kin kirani bana kusa yarona ya amsa”.

Amsar data samu kenan bayan sallamarta da aka amsa. Har cikin rai taji daɗi, dan haka a fili ta furta “Alhamdullah dama naji haka a jikina”. Shi kuma ta bashi amsa da “Babu damuwa Sir”.

“kina da fahimta Shahrbano”.

“Bankai nan ba😣”.

Ta bashi amsa da emojin yamutse fuska. Sharewa yay da faɗin,

“Ta samu ne?”.

Itama sai ta share da bashi amsa da.

“Kusan haka. Sai dai a wannan gaɓar lamarin akwai ban tsoro Sir Ajmaal. Da gaske mutanen nan matsafa ne kuma suna aiki da aljanu”.

“Ya arrahaman! Kamar ya? Har kimsa na tsorata fa”.

“Tab tunma kan na faɗa kenan. To kama cire dan wlhy ba aljanu ba ko bataliyar ifiritai ce sai naga bayan mutumin nan. Wai fa jiya da dare nabar sashen nasa na koma inda sukace nawa kawai yau na wayi gari na ganni an sake maidoni sashen Dodon nan. Ɗakin dana kwana kuwa duk da haɗuwarsa na rantse maka a harmutse kamar anci dambe”.

Ya share zancen farko ya amsa na ƙarshe.

“Wlhy kuwa Sir! Sai dai fa ni wannan bai damenba. So nake nasan ta yaya aka ɗakkoni aka maido ni inda ba nan na kwanta ba”.

“Kina da gaskiya dan akwai alamar tambaya kam. Amma ke yanzu wane mataki kika ɗauka?”.

“Komai banyiba har yanzu, nadai fara bincika irin kamshin da naji jikina nayi, inma shine ya aika aljanunsa suka ɗakkoni dan ya kashe ni”.

“🤭”.

Ya bata amsa da emojin rufe baki alamar tare dariya.

“😞Bafa abin dariya bane wannan, abin a dubane. Idan kuma aka halakani kafin ƙwato muku ƴancinku ku kukayi asara Sir Ajmaal”.

“Eh gaskiya hakane kuma ranki ya daɗe. Yanzu dai ƙarasa bani labarin dan in san ina zan kama. Saboda na gama shirye-shiryen buɗe wani sashe na shiri na musamman akan wannan case ɗin, sai dai komai zai kasance cikin hikima”.

“Aiko da naji daɗi Sir, dan gara kam a fara kafin ma na mutu na dinga ji. Dama inason maka zancen wancan tashin bomb ɗin, ko ka san mutumin nan ko damuwa bai nuna ba akan lamarin tsabar bai ɗauki rai bakin komai ba. Wlhy naji kamar na shaƙesa a jiyan kowama ya huta dan takaici”.

“Wai da gaske kike zancen nan ranki ya daɗe?”

“Wlhy kuwa babu wasa. Ni ka daina kirana da wannan sunan bana so”.

“Kiyi haƙuri kin cancanta ne ai. Zawjata-almilk guda ai ba abin wasan mu bace. Nima dai tsaurin ido yasa har nake iya zaman tattaunawa da ke”.

“🙄😏”.

Ta tura masa tana kashe data ɗinta. Daga can Ajmaal ya ƙurama emojis ɗin ido yana mai ƙoƙarin danne dariyarsa amma hakan ya gagara, dole yay faffaɗan murmushi har haƙoransa na bayyana yana ayyana (ƙuruciya daɗi) a zuciyarsa. Ganin ta kashe datan shima sai ya kashe kawai dan yana son sai ya nutsu yay zaman nazari akan abinda suka tattauna ɗin…..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button