Daudar Gora Book 1 Page 80
A firgice ta farka a ɗan barcin daya figeta bayan ta idar da sallar azhar. Ta dafe kanta dake sara mata. Irin mafarkin da tai da dare ne dai babu banbanci. Huci ta furzar da faɗin, “Wace madara ce haka? Tabbas kodaga ina zata fito babu alkairi a cikinta tunda har mafarkin nan ya sake maimaita min kansa. Ya ALLAH”. Ta furta a fili zuciyarta duk babu daɗi, dan zuwa yanzu Iffah ta fahimci wani ɓoyayyen al’amari game da ita, tabbas in har zatai mafarki taita kuma maimaita irinsa sai wani abu ya biyo bayansa mai taɓa zuciya, ta gane hakanne a ɗan zamanta cikin masarautar nan, sai kuma auna abubuwan da suka faru a baya kafin yau ɗin. Sai dai tana ƙoƙarin ƙin gasktama kanta hakan dan kar zuciyarta ta shagala kan abinda zai sakata kaucema umarnin mahaliccinta kuma. Ga kanta jingim kamar yanda yakeyi a duk lokacin datai mafarki makamancin haka, sai zufa data jiƙeta sharkaf tamkar wadda tai wanka. Shigowar saƙo a wayarta da ke gefenta ya sakata tsurama wayar ido na kusan mintuna biyu, kamar wadda aka zaburar wani abu data shafa’a kuma sai ta jawo wayar. Data ta kunna a take tai downloading WhatsApp app…, Bayan ta kammala dai-daita komai tai searching number Sir Fawzan da zuciyarta ke ayyana mata ta fara nema, cikin rashin sa’a taga kusan kwana uku ma baya online ta hanyar lastsin ɗinsa. Duk da hakan bai mata daɗi ba batai wani yunƙurin kiransa ba ta maida akalarta kan number abokinsa Ajmaal. Cikin sa’a shikam dai yana online. Sallama tai masa a taƙaice ta tura, sai dai har kusan mintuna biyu babu reply (yana aiki) zuciyarta ta ayyana mata. Aminta da hakan ya sata cigaba da ajiye masa saƙo kawai a kan duk abinda ya sake faruwa bayan wanda ta tura masa ranar. Daga karshe ta aika masa da roƙon ya bincika mata iyayenta dan har yanzu hankalinta ya kasa kwanciya dangane da su. Ta haɗa masa da adireshin gidansu, da faɗin (In har kaci amanata ko yaudarata na barka da mahaliccin rana da wata yay maka hukunci da alhakin dukkan al’amuran ƙasar ruman da zalincin mulkin wannan shaiɗanin dodo ke tafin hanunsa). Daga haka ta fito shima Sir Fawzan ɗin ta tura masa gajeran saƙo ta goge WhatsApp ɗin gaba ɗayansa ta ajiye wayar.
Da ɗan layin nauyin jikin dake tare da ita ta miƙe, tana ƙoƙarin shiga toilet taji kamar an gitta mata ta baya. Idanunta ta ɗan rumtse sai kuma ta waigo. Komai babu dai a zahiri dan haka ta kaɗa kanta kawai ta shige bakinta da addu’a….
Fitowarta kenan bayan ta watsa ruwa alerm ɗin ƙofar yay ƙara alamar ana knocking. Sai da ta zira doguwar rigar abaya data ɗakko cikin kayanta sannan ta ƙarasa ƙofar ta buɗe. Hadimar dake tsaye ta zube ƙasa cikin girmamawa tana kwasar gaisuwa. Amsa mata Iffah tai, zuciyarta babu daɗi akan yanda suke ƙasƙantar da kansu, ta amsa cikin sauƙin muryarta dake a sanyaye sakamakon mafarkin da duk ya sakar mata kasala..
“Wani abu ya faru ne?”.
Ta tare hadimar tunkan tace komai. Kai ta gyaɗa mata tana sake rissinar da kanta. “A gafarceni ya Zawjata-almilk. Dama abinci ne aka kawo daga sashen mai Babban ɗaki”.
Iffah tai ɗan jim tana hasashen wace kuma mai babban ɗaki? Kamar hadimar ta fahimta tai saurin mata fashin baƙi da “Malikat mai babban ɗaki”.
(Malikat Haseenat) shine abinda zuciyarta ta ayyana mata. Ta kaɗa kanta da faɗin, “Okay ba damuwa zan fito”. Daga haka ta maida ƙofar ta rufe. Ciki ta koma, sai dai maimakon zama sai ta koma kaikawo kamar mai Safa da marwa abubuwa masu yawa na faman mata kaikawo. Ta jima a haka sosai kafin ta sake kimtsa jikinta cikin wata tsadadiyar abaya mai adon stones dake ta ƙyalli da ɗaukar idanu. (Wannan yana cikin horon Daneen Ammarah data tabbatar mata koda wasa karta zauna da kazamar shiga ko fitowa da ga ɗaki a raguwar kwalliya. Dolene inhar zata bar cikin ɗakinta ta tabbatar komai na jikinta ya isa a kalleta da shi. A tsarin masarautar hakan ba fariyya bane mutunta kaine ga kowa. A kuma ɗan zaman Iffah cikinsu ta fahimci hakan sarai). A yanzu ma kamar ɗazun turarrukan sa ta baza har ƙamshinsu na rige-rigen fita kafin ita ta fita. Ta fito cikin takunta na nutsuwa da ƙasaita kamar wata budurwar macen ɗawisu (🥱😉lol)………