Latest Updates

Daudar Gora Book 1 Page 62

Sponsored links

Dukan matakin shawarar da Sir Fawzan ya bata shi tabi, dan tunda sukai bankwana da Daneen Ammarah tai shirin barci ta sakama ƙofarta key. Ta fara da buɗe Watsap, sannan ta lalubo number Ajmaal. Cikin sa’a kuwa yana online, wani farin ciki ne ya ratsata. Taja kakkauran numfashi da godema ALLAH.

_Assalamu alaikum_

Ta fara turawa da fatan samun amsa zuciyarta na harbawa da sauri-sauri. Tsahon mintuna kusan goma babu alamar zama a buɗe saƙon. Sake tura sallamar tayi a karo na biyu. Ta dasama wayar ido kamar mai irgan fitan numfashinta. Kamar a mafarki taga an buɗe, tai kasare tana jiran taga an amsa sai dai shiru har kusan wasu mintuna goman. A yanzu kam zuciyarta ta sosu, dan duk yanda take buƙatar abu ga mutum ta tsani a wulakantata. Ta cije lips da ƙarfi tana danne fushin dake son mata tasiri.

_Wa’alaikissalam_.

Aka amsa mata a bazata. Nannauyar iska ta furzar, itama ta buɗe saƙon ta share. Da ƙyar ta iya danne zuciyarta mintuna bakwai suka cika.

Tai shiru tana kallon amsar, sai kuma taja tsaki na takaici. A fili ta furta, “Aikin banza. Ka sani shine baka san aikinka ba mtsoww!!”.

Sharewa tai, ta rubuta masa.

_Kwanaki na kira, amma akaimun tarbar da har yau ina mamakinta. Shin dama manyan ƴan jarida haka suke da wulaƙanta bukatar marasa ƙarfi?_

Tsahon minti ashirin da buɗe saƙon babu alamar za’a amsata. Hakan yay mata ciwo matuƙa. Sir Fawzan ta kira, bugu biyu kuwa ya ɗaga. A ɗan rikice yace, “Iffah baki ganin akwai matsala yawan kiran nan? Masarauta fa ba irin ko’ina bane sunada hanyoyin tsaro ɓoyayyu ciki harda cctv”.

“Hakane Sir, amma nima dole ce ta sakani kiran. Anya kuwa wannan abokin naka da gaske ɗan jaridar ne? Sam baya ɗaukar al’amarina da muhimmanci, duk ɗan jarida na kwarai zaka samesa da zumuɗi akan labari, musamman ma irin nawa daya kasance babba”.

“Miya faru? Bai amsa saƙonki ba ne?”.

“Ya amsa. Amma yanamun yanga. Harna fara jin gundira a huɗɗa da shi”.

“Karki saurin karaya, amma nayi mamaki dan masan Ajmaal ba mutum bane mai irin wannan siffar wlhy. Inaga dai akwai aikin da yake yi a wannan gaɓar shiyyasa. Kin san su abubuwan nasu da yawa. Kin san kuwa yanda ya ƙagu akan son jinki, dan ɗazun na fara ƙyara masa abinda ke ranki kaɗan”.

Ta ɗanji sassauci daga haushinsa. Taja ajiyar zuciya a fili da faɗin, “Shike nan bara na koma”.

_Masha ALLAH hakan yayi, sai dai a maimakon kwana uku mizai hana muyi mako-mako. Dan wani abun da zai zo yana buƙatar bin diddigi da faɗaɗa bincike mu tanan a garemu._

_Yanda kace haka za’ayi. Ni dai fatana ka kasance ɗan jarida mai gaskiya da riƙon amanar kimar ƙasarsa. ALLAH shine shaidata na baku dukkan yarda kai da Sir Fawzan. Idan akasin nasarata ya biyo bayan yunƙurina ku zan zarga. Duk kuma yarinyar data samu kanta a irin halin da ƴan uwana da ni muka kasance kuma zaku amsa sunan azzalumai ne kamar yanda Shahan-shan ɗin ke amsawa a yanzu. Ku kuma dinga tunawa da mala’iku tare da ku masu rubutawa daga ayyukanku na zahiri da baɗini. ALLAH ya cigaba da tsare ƙasar ruman. Idan kanada wata tambaya zaka iya tura min text message na Barka lafiya_.

Bata jira amsa daga garesa ba ta fita gaba ɗaya. Watsap ɗin ta goge ta kashe wayar gaba ɗayama tana sakin ajiyar zuciya a jajjere. Sai takejin wani kaso na damuwarta da nauyin zuciyarta ya ragu kaɗan. A wani gefe kuma kamannin mutumin can da wanda ta gani a jiya matsayin Shahan-shan ne ke ta faman mata kaikawo babu alamar zai barta ta huta……

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button