Latest Updates

Daudar Gora Book 2 Page 113

Sponsored links

“Idan baki bar turamin bakin nan ba zan maimaita ni babu ruwana”. Ya fada yana tsane mata laimar ruwan kanta da towel. Narai-narai tai da fuska zata sake masa kuka ya daura yatsansa saman bakinta ya ce, “Shilli!! Harda kuka ma”. Babu shiri ta hadiye abunta da maida bakin da sauri.Murmushi ya saki ya cigaba,Da tsane mata mata gashin…. kiran da ya shigo ta sashi dakatawa su duka suka dubi wayar, kamar bazai daga ba dan har tana gab da tsinkewa sai kuma ya kai hannu ya dauka batare daya matsa da ga gabanta ba ko dauke towel din da ga kanta.

Cikin girmamawa shugaban jami’ai ya shiga gaishesa da ga can, a takaice ya amsa masa murya a dake kamar bashine ke hidimtawa yar yarinya ba. Da ga can shugaban jami’ai ya kara nutsuwa sannan yay masa bayanin abinda ke faruwa. Shiru kamar bazaice komai ba kafin ya nisa a dan fisge da maganar nan tasa kasa-kasa ya ce, “Doctor Afif ya je ya dubasa a cikin kurkukun”. Daga haka ya yanke kiran.

Kallonsa Iffah tai da jajayen idanunta, gaba daya ya sauya kamar bashi ba ya koma mata Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed da ta fara gani a sashen Mammah. Muryarta a dashe saboda kukan da tasha ta ce, “Miya faru?”.Kamar bazai kulata ba yana cigaba da goge mata kan tsahon minti biyu kafin ya motsa lips da kyar ya furta “Jasim”

Nan ma kan ta daga masa. Komai bai sake cewa ba shima. Sai matsawa da su da yay zuwa gadon, tana a jikin nasa ya kai zaune itama ya zaunar da ita a cinyarsa. Addu’a ya fara mata a kan idanunta a lumshe, bayan ya kammala ta kwantar da kanta a kafadarsa tai luff tana sauke ajiyar zuciya a jajjere. Nan ma sun jima a zaman shiru kafin ya kirata muryarsa a can kasan makoshi.

Bata fahimci mi yake nufi ba, dan haka ta dago idanunta da jan cikinsu ke dan raguwa a hankali ta zuba masa. Bazata iya jurar kallonsa cikin ido ba dan haka ta dauke su ta maida gefe. “Ban san akan mi kake magana ba Sultan”. Sai da ya dan furzar da hucin baci ran da yake ta dannewa, a dan fuse ya furta, “Jasim!

Miyasa kika boyen ya sameki a kurkuku da maganar banza?”

Shiru kamar bazatace komai ba, sai kuma ta motsa cikin sauke ajiyar zuciya ta ce, “Kayi hakuri, a lokacin ban san ta yanda zan tunkareka ba. Ban kuma san ta yanda zaka fahimceni ba. Kuma ai ALLAH ya kareni da ga sharrinsa tunda ga shi yau gaskiya tayi halinta”.

Shiru baice komai ba, dan zuciyarsa tafasar kishi take har yanzu akan wanna kalmar, tafi komai tsaya masa a zuciya fiye da abinda Miran Jasim din ya aikata masa dan ya jima da sanin dama suna farautar rayuwarsa. Sai maganar rashin fitowar sunan Miran Arshaan shima na masa kaikawo, kamar zai mata magana akan hakan sai kuma dai ya hadiye kayansa da tunanin ko Miran Jasim din ne kawai ya fiddo mata da nasa hali. Amma in bai manta ba ranar a kalamanta ta masa nuni ne da mutane biyu ko yace fiye da daya. Hakan na nufin bayan Jasim din akwai wani kenan. To miyasa ta boye? Bashi da mai basa amsa baya kuma bukatar son ji da gareta yanzu dan ransa duk babu dadi yake ji.Itama da kanta ta fahimci hakan, dan fuskarsa a tsuke take fiye da sanda suka fita kotun. Sai duk take jin kuma babu dadi. Dan haka kawai take jin tausayinsa. Idan har zai shiga damuwa saboda halin wancan karen uncle din nasa, yaya zai kasance kuma a randa zai san mahaifiyarsa da kanta ke halaka masa matan aurensa da duniya ke kallonsa a mai halakasu tsahon shekaru. Kai kai wannan al’amarin fa na taba mata zuciya why sosai matuka. Ajiyar zuciya ta dan sauke a hankali, sai kuma ta kai hanunta saman lallausan gashin sajen fuskarsa ta shafa. Murya can ciki ta ce, “Kayi hakuri? Ka amsa da hannu biyu jarabawace. Badan UBANGIJI baya sonka ba ya jarabeka da su. Shi kansa mulkin ma da kake kai ai jarabawa ce. Kai numfashinmu ma kansa jarabawace a garemu, dan UBANGIJI ya azurtamu da shine domin yaga zamu kasance masu bin dokokinsa ne ko kuwa masu bijire masa”.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button