Daudar Gora Book 1 Page 42
Cike da jin tausayita Daneen Ammarah ta shafa kanta, “Duk ɗa na gari dolene ya kasance cikin kewa a lokacin da yay nesa da ahalinsa, da ace inada dama da a yau sai na kaiki kinga su Ummunki. Amma dokar masarauta ce Zawjata-almilki tana fitane kawai bisa ƙwaƙwaran dalili, zuwa gidansu kuwa tana yinsa ne sau biyu tak a shekara, ɗaya a sirrance, ɗaya a bayyane tare da rakkiyar hadimai. Shiko mafarki ai na gaskiya bane Ibnati, MANZANNI ne kawai idan suka yisa yake gaskiya a garesu, amma mu namu yakanzo da wasu sigogi ciki harda sheɗanu”.
A hankali hawaye suka silalo a kumatun Iffah, bawai lokacin ziyarar bane yay mata nisa, rashin tabbacin kaiwa lokacin ziyararne ya sata zubar hawaye. Ita dake zaman jiran ƙaddarar mutuwarta taya zatai tunanin zuwan waɗan can damarmaki guda biyu na ganin su Babiy, maganar mafarki kam ta san gaskiya Mamyn ta faɗa, itama kuma ba tana dangantashi da zama tabbaci bane, kawai tana matuƙar jin tsoron faruwar wani abu ne a dalilin mafarkanta na baya…. Ganin hawayen Iffah ya matuƙar tada hankalin Daneen Ammarah, a rikice ta shiga tambayarta kamar yanda ta saba in har ta ganta a makamancin damuwar nan. Hannu Iffah tasa ta share hawayen nata da ƙirƙiro murmushi.
“Mamy ki kwantar da hankalinki hawayen sunzo ne kawai da kansu babu dalili”. “Haba Ibnati, dama ana kuka babu dalili ne? Ko baki faɗaba nasan kinada dalilan yin kuka, amma idan kika zama mai haƙuri da juriya wataran ke zakiyi dariya a gaban waɗanda suka cancanta suyi kuka.” (ALLAH ya tabbatar da wannan ranar) Iffah ta faɗa a zuciyarta, a zahiri kam sai ta goge hawayen tana murmushi. Hakan yasa Daneen Ammarah yin murmushin itama, kafin kuma ta mike tsaye da kama Iffah suka koma kan dardumar da aka shirya abinci acan gefe na ɗakin, dan ɗakine ƙaton gaske mai dauke da komai na jin daɗin duniya. Tare sukaci abincin, Daneen Ammarah har tana bama Iffah wani lokacin a baki, jitake inama Iffah ɗiyartace, dan da’ace tana gidan aurenta har yanzu ɗiyarta ta fari zata iya kasancewa dai-dai da shekarun Iffah ne. Kulawar Daneen Ammarah ta sake saka sassauci a zuciyar Iffah harta ɗan saki jikinta. Bayan sun kammala ta sakata shiga bayi tai wankan maganin da take amfani da shi, data fitoma da kanta tai mata hayaƙin turare. Iffah ta hau gado ta zauna, Daneen Ammarah a gefenta da littafin tarihin annabawa acewarta zata dinga karantama Iffah har sai taga tayi barci domin ɗebe mata kewa.
Iffah ta jinjina kanta da sauke ajiyar zuciya, “Immm Mamy dama…” sai kuma tai shiru dalilin gargaɗin da zuciyarta ke mata tunda har yanzu fa Bama wai tasan matsayin Daneen Ammarah ɗin bane a masarautar.
“Dama mi? Kinga karkiji komai kimin duk tambayar da kike buƙata, insha ALLAH zan kasance mai baki amsa, idan kuma bata dace ba zan baki shawara kodan nan gaba”.
Kai Iffah ta jinjina “Dama dan ALLAH zance ne yanzu mutuwar su hadiman can shikenan ta tafi a banza baza’ai wani bincike a gano ba?”.
Kallo na kusan sakan biyar Daneen Ammarah taima Iffah da har tama ɗauka tai laifi, amma sai taji taja numfashi da maida kanta kan littafin hanunta. “Mutuwarsu bazai tafi a banza ba saboda dalili mai ƙarfi Ibnati. Dan duk wanda ya kashesu yana gudun tonuwar asirinsa ne akan cutar da ke da akai yunkurin yi. A yanzu haka Shahanshan ya saka kwamitin bincike, muna fatan kuma ta wannan hanyar za’a gano koma wanene ya saka ki a halin da kika tsinci kanki. Kuma dama kema ana jiran ƙara samun lafiyarki ne aji ko akwai wani abu da kika sani, ko kuma bayan su ukun can da ɗayar da aka samu nasarar ceto ranta ko akwai wasu..”
Da sauri Iffah ta dubeta. “Mamy akwai wadda bata mutu ba dama?”.
“Eh akwai amintacciyar hadimar Umm-Jasrah (haka take kiran Malikat Bushirat) mai suna Diwa. Ita an kaita asibiti kafin gubar da suka sha ta karasa katsa ƴan hanjinta. Alhmdllh kuma an dace dan yanzu haka tana kan shan magani, tana kuma zagaye da tsatstsauran tsaro”
“ALLAH ya ƙara bata lafiya, sai dai kuma banajin tanada hannu a cikin al’amarin Mamy, dan da ganinta mutiniyar kirki ce”.
“Gane mutanen kirki ba’a ido yake ba Ibnati musamman a wannan masarautar da kowa kansa kawai ya sani, a mafi yawan lokuta ma ba’a gane maƙiyi da halayya. Akwai rikitattun abubuwa dake a matuƙar cuɗe a wannan Daular da gani da ido bazai wadaci mai kallo ba, dan haka nakeso ki nutsu kisa hankalinki waje ɗaya kafin ki koma sashenki ki koyi abubuwa da yawa na salon mulki da tsarin matsayinki na Zawjata-almilki. Saboda kunada matuƙar tasiri da girma a tsarin ƙarfin iko na masarauta da kaikawon talakawan ƙasan ruman. Fatana kuma kece Malikat a cikin Zawjata-almilki insha ALLAHU”.
Sam Iffah bata fahimci komai ba ga kalaman Daneen Ammarah, amma sai bata sake cewa komai ba dan a ganinta tana buƙatar samun lokacin yin nazari na musamman a kansu kafin ta fahimcesu dallah-dallah…….