Daudar Gora Book 1 Page 38
Babiy da hawaye suka gama wanke masa fuska ya share yana duban Abu Moosa “Kenan kai ne ka ƙulla na uku ma?”.
“Wlhy a’a bani da alaƙa da wannan, hasalima ban san ƴar wajenka bace sai ranar da aka kawo kuɗin aure”.
“Waye ya kashe min ƴaƴa? Kai kuma miya faru da kai?”…….
Abu Moosa dake sonyin magana ya dafe ƙirjinsa da numfashi ke kokawar kufcewa, tari ne ya suɓuce masa sai ga jini. Hankalin Babiy da Ummu ya tashi, amma Hanash ko’a jikinsa. Da ƙyar tarin ya lafa, Babiy dake riƙe da shi yace, “Kayi haƙuri muje asibiti, aman jini fa kake yi”. Murmushi yay mai ciwo da kaɗa ma Babiy kansa da ƙyar. “Abu Hanash zuwa asibiti bazai canja komai ba, dan gubar da aka shayar da ni bata da makari a ko’ina sai a wajensu.”
“Ya ALLAH! Guba kuma?” “Wannan shine hukuncin daya dace da masu irin halina ai karka damu, kai dai kawai ka saurareni zan gaya maka ta hanyar da zaka kuɓutar da yarinyarka, ina fatan hakan ya zamar min aikin alkairin dazan samu sassauci a kabarina”. Babiy zai yi magana ya dakatar da shi. “Ka saurareni kawa Ab…..” ya kasa ƙarasawa saboda sabon tarin daya sake sarƙesa. Sosai Babiy ya rikice ya shiga ƙwala kiran Hanash duk da yana a kusa da shi. Hanash dake jin tamkar yasa wuƙa ya ƙarasa numfashin wanan shegen tsoho ya amsa da ƙyar.
“Kaga kamashi maza muje asibiti”. “K…k…karku wahal da kan.. Ku. ka saurareni kawai”.
Abu Moosa ya tari numfashinsu da ƙyar yana dafe ƙircinsa da tari ke yunƙurowa. Babiy ya buɗe baki zai yi magana cikin taresa shima sai kawai sukaga yarab alamar rai yayi halinsa. Salati suka ɗauka a tare, wanda yay dai-dai da shigowar jami’an tsaro dake na ƴan sanda a ƙasar, bayansu wata mata ce ke rusar kuka… “Ranka ya daɗe dama na faɗa muku, na faɗa muku mutumin nan baya ƙaunar mijina, yanzu kun gani da idonku gashi nan ya kashe mini shi, dama kullum yana faɗa min neman rayuwarsa yake yi, ashe dai shine ɗin zai zama ajalinsa…..” ta zube ƙasa tana cigaba da kuka harda kururuwa…….
Hankali tashe su Babiy ke kallon wannan mata da jami’an tsaron, ba shigowarce ta tada hankalinsu ba da farko, dan tunaninsu ya basu duk wanda ya bama Abu Moosa guba shine yasa suka biyo sa. Furicin wannan mata da kai tsaye Babiy ya gane matar Abu Moosa ce ya firgitar dasu. Cikin ƙarfin hali Babiy yace, “Yallaɓai taya daga taimako kuma zan zama mai kisa? Abu Moosa abokina ne tun ƙuruciya kowa ya sani, ban kashesa a da da muke tare ba sai yanzu da a ƙalla nama kai shekara biyar kenan ban sakashi a idona ba sai yanzu dana gansa ayam cikin gidana babu zato…..”
“……Shiyyasa akaga gawarsa a cikin gidanka yanzu daka samu damar ganin nasa ko?”. Jami’in ya tari numfashin Babiy da sauri yana wani makirin murmushin ƙeta…
“Allahumma ajirni fi musibati wa’akhlifni khairin minha” Babiy ya faɗa a zahiri gumi na karyo masa. Duban jami’in yay zaiyi magana matar ta taresa tana cigaba da kukanta mai cike da bori…. “Ƙarya yake wlhy yallaɓai, shekaran jiya jiyan nan sai da yaje har gidanmu ya faffaɗa masa magana mara daɗi da tabbatar masa shine ajalinsa, idan ya ƙaryata ai munada shaidar hakan”.
Hanash da zuciyarsa tazo ta tokare maƙoshi a hasale yayo kan matar, wata shegiyar shaƙa yakai mata saiga idanunta tamkar zasu fito waje. “K! baƙar matsiyaciya, dan kawai anga gawar mutum a waje sai ya tabbatar masu wajen suka kashe shi!!”. Idanuta ta rumtse da ƙarfi jikinta na ɓari, ta fara kakarin azaba dan da gaske ta shaƙu. Tuni jami’an tsaron duk sukai kansu da ƙoƙarin ɓanɓare hanun Hanash a wuyanta amma sun kasa. Ummu kuka ta sanya, yayinda Babiy keta kiran sunan Hanash da faɗin ya saketa amma sam babu alamar yana ma jinsa. Da ƙyar aka iya ɓanɓare Hanash, ta zube gefe tana sauke nunfashi da ƙyar hanunta riƙe da wuyanta. Sai da suka bata ruwan da suka fita suka ɗakko a mota da sauri tasha ta samu dai-daiton numfashi.
Cike da gadara ogan tawagar ya bama yaransa umarnin kama Babiy da Hanash. Sosai Ummu ke kuka da roƙonsu amma babu wanda ya saurareta, har ƙofar gidansu daya cika da mutane tun isowar jami’an tsaron ta biyosu amma kamarma basu san tanayi ba. Haka aka saka Babiy da Hanash a mota, sai gawar Abu Moosa a Ambulance da sukazo da ita (Alamar akwai dai lauje cikin naɗi kenan. Inba hakaba miye na zuwa da Ambulance ɗin?
Matan anguwar ne suka rufu kan Ummu data yanke jiki ta faɗi bayan wucewar motocin. Amma koda suka zuba mata ruwa bata farfaɗo ba. Hankalinsu ne ya sake tashi, makwafcinsu ya bada umarnin a sakata a motarsa a kaita asibiti. Da taimakon matan aka sakata a mota, matarsa da wata mata dake anguwar itama mijinta ya rasu suka shiga. Sai lokacinne mutane suka samu bakin magana. Wasu na nuna tausayawa ga wannan ahali, wasu na jin farin ciki badan sun taɓa musu komaiba, sai dan kawai dalilin hassada na rashin dalili.
A asibiti kam har an amshesu za’a fara dubata sai sukaga Doctor ɗin ya dakata sakamakon kiran wayarsa da akayi. Kansa ya girgiza musu ya nufi barin ɗakin yana sanar musu yanada uziri. Hankali tashe makwafcin nan nasu da ake kira Abu Zainab ya shiga roƙonsa amma bai sauraresu ba. Sun fara neman taikon Nurses suma sai zuƙewa suke saboda gargaɗin da Doctor yay musu. Al’amarin kamar wasa anƙi taɓa Ummu, dole suka ɗauketa suka bar asibitin zuwa wani, sai dai acan ɗin ma har an amshesu aka koresu. Basu gajiyaba suna kuka suka nufi privet ko acan za’a dace tunda aikin kuɗine. Anan sun amsheta, amma sun sara musu maƙudan kuɗaɗe kafin su taɓata, acewarsu dokarsu kenan. Matar nan da mijinta ya rasu ta fashe da kuka tana girgiza kai. “Suma basa son su amshemu ne kawai, shiyyasa suke mana kora da hali. Inba kora da hali ba ai banajin Abu Hanash ya mallaki koda kwatar waɗan nan kuɗaɗen da suka ambata inba dai kaddararsa zai saida ba”.