Daudar Gora Book 1 Page 31
Har cikin zuciya Malikat Bushirat taji daɗin kalaman Amera Danish-Ara, dan haka a lips ta amsa da “amin” tana mai sauke ajiyar zuciya, dan bata cika samun damuwa da ita a gidanba tunma sunada ƙuruciya. Amera Danish-Ara mace ce mai tsananin kissa da ba lallai a lokaci guda ka iya gano wacece ita ba. Duk da kasancewar ita Zawjata-almilki ce a daular ruman zakasha mamakin irin girman da take bama Malikat Ashwaq da Malikat Bushirat a gidan a zahiri tunda ta shigo. Kai hatta da Amera Haifah dake amarya kuma ƙarama a cikinsu ita bata taɓa bari saɓani ya shiga tsakaninsu ba a zahiri. Wannan halin nata yasa sanda surukarsu Malikat Haseena ke da lafiyar ƙafa take sonta da janta a jiki fiye da su Malikat Bushirat. Wani lokacin har kwatance take musu da halin Amera Danish-Ara ɗin wai suyi koyi ta fisu dattako. A yanzu haka da take zaune babu lafiyar ƙafa Ameera Danish-Ara ɗin tafi kowa sintirin zuwa dubata da mata hidima a zahirance, duk da itama Malikat Bushirat na kamantawa sai dai babu ruwanta da sai wani ya gani yace tayi.
Shiru falon ya ɗauka na wasu mintuna, Amera Danish-Ara na son taga Iffah babu fuska ga Malikat Bushirat, dole ta miƙe cikin ƴan kame-kame tana tambayar ko Amera Haifah tazo kuwa?.
Kallon ƙasan ido Malikat Bushirat tai mata tana ƙara tsuke fuska, dan ita duk yanda take da zafi babu wanda zaice ga ranar data zauna maganar wani a cikinsu koda da su Jasrah ne kuwa. A ganinta idan tai hakan sunma isa kenan a wajenta. Murmushin yaƙe Amera Danish-Ara tayi cike da basarwa. Sai dai ƙasƙantaccen kallon da Malikat Bushirat tai mata ya matuƙar sokar mata zuciya. Taɗan risina da faɗin, “Na barki lafiya ranki ya daɗe”.
Kai kawai Malikat Bushirat ta jinjina mata batare data ko ɗago ba. Amera Danish-Ara ta cije baki da ficewa hadimanta dake jiranta daga falo na biyu suka take mata baya.
Sam Amera Danish-Ara bata gaban Malikat Bushirat, kalaman Malikat Ashwaq ne keta faman mata kaikawo a zuciya musamman na ƙarshe. (Fatan alkairi da samuwar lafiya ga Zawjata-almilki) waɗan kalamai bakwai a cikin tarin kalaman Malikat Ashwaq sunfi komi tsayawa Malikat Bushirat a zuciya. Dan kuwa tana fassarasu ne da wani abu daban ne. Haka manyan mutanen masarautar suka cigaba da shigowa duba Iffah daga sassa daban-daban na gidan. wasu iyaye ne, wasu yayu, wasu ƴaƴa harma da kakanni maza da mata duk da basu samun damar shiga ciki iyakarsu wajen Malikat Bushirat. Bata damu kanta ba sai da dare yaja. Koda hadimanta suka dawo sallamarsu tai dan tafi buƙatar kaɗaici a yanzu saboda son ƙara tunani akan kalaman Malikat Ashwaq da suka gagara haɗiyuwa a gareta. Da kuma nazartar kowa daya shigo sashen nata domin duba Iffah. Tun tana a zaune har takai ta miƙe tsaye hannayenta goye da bayanta tana faman kaikawo tamkar mai safa da marwa……….
Dare yayi nisa, bakajin motsin kowa a daular ruman sai sassanyar iskar dake kaɗa bishiyoyi kaɗan-kaɗan. Sai kuma Hadiman da ake kira Ghazi a masarautar ne kawai ke faman kaikawo domin bada tsaro ta kowacce kusurwa ta gidan musamman a sashen Tajwar Eshaan.
Iffah dake kwance samɓal a katafaran gadon alfarma na Malikat Bushirat idanunta a rufe kai kace batama numfashine ta fara zabura a hankali kamar wadda ake mintsini. Jasrah ce kawai tare da ita a ɗakin, tana daga gefe barci ya ɗan figeta mai cike da wani irin mummunan mafarki. Wata gigitacciyar ƙara da Iffah ta fassa tare da girgizar data saka gadon shima rinƙa girgizawa yasa Jasrah farkawa a kiɗime. Tsalle tai gefe jikinta na rawa ganin yanda Iffah da gadon ke girgiza, hatta shi kansa ɗakin ji Jasrah keyi na mata rawa shida fitulun da suka haskesa, dan sai daukewa suke suna kawowa. Wani irin tari Iffah ta farayi mai tahowa da aman jini ta baka ta hancinta harda ta kunne. Jasrah ta fara ƙwala kiran sunan Malikat Bushirat a matuƙar firgice tana sake manne jikinta da bango hanunta na laluben ƙofa amma ta kasa buɗeta…
Malikat Bushirat da dama ba barci take ba saboda tsabar damuwa ta buɗe idanunta a hankali jin sautin muryar Jasrah tamkar a sararin samaniya tana yawo. Cigaba da jin sautin ya sata miƙewa zaune ta sauka a gadon baki ɗaya. Babu wani hadimi dake da damar shigowa sashen ɗakunan barcinta sai masu gyarawa kawai suma da safe ne, hakan ya sata ɗora abaya kawai a saman kayan barcinta ta fito…. Jasrah da ta gama fita hayyacinta gaba ɗaya ta faɗa jikin Malikat Bushirat, rungume ƴar uwar tata tayi, a hankali ta shiga hura mata iska a kunne tana bubbuga bayanta. Jasrah da ƴar nutsuwa ta fara zuwa mata tai lamo tana sauke numfarfashi a jajjere, sai kuma ta ɗago a hankali hawaye wanke da fuskarta…
“Mike faruwa?”.
Malikat ta faɗa a hankali. Ɗakin Jasrah tabi da kallo, kafin ta fara mata bayanin komai har yanzu hawayenta sun kasa tsayawa. Sosai hankalin Malikat ya ƙara tashi, sai dai kamewarta yasa ba lallai ka fahimta a kan fuskarta ba. Cikin takunta na ƙasaita ta isa gaban gadon inda Iffah take. Kwance take samɓal tamkar ba itace ta gama buge-buge ba yanzun. Idanu ta tsura mata a karan farko, yarinya ce ƙarama sosai kuma ƙyaƙyƙyawa matuƙa, duk da halin ciwo da take ciki da canjawar fatar jikinta ƙyawunta da kwarjininta basu gushe ba, tausayinta mai tsanani da ƙaunarta suka sake ratsa zuciyarta. Zaune ta kai gefen gadon ta kai hannu ta shafa yalwataccen gashin Iffah daya gama bajewa a kan filon.
“Ibnati kiyi haƙuri zaki samu lafiya bazasu taɓa samun galaba ba kinji”.
Iffah da sarai take jin maganar Malikat dan ba barci take ba azaba ce kawai ke ratsata tai murmushin ƙarfin hali a zuciyarta, a karan farko taji ƙaunar matar a ranta da sake ganin kima da girmanta…….