Daudar Gora Book 1 Page 30
Kamar yanda Malikat Bushirat ta bada umarni an maida Iffah sashenta, a kuma cikin ɗakin barcinta da babu wani mahaluki daya taɓa shiga bayan Tajwar Eshaan da Jasrah. Hakan ya bama dukkan hadiman sashen mamaki da tabbatar da lallai wannan Zawjata-almilki ɗin tana da wata daraja ta musamman ga Malikat. Dan kaf Zawjata-almilki da suka rasa rayuwukansu a gidan babu wanda ya iya ganin makamancin damuwar Malikat Bushirat irin ta yau. Ƙarin tabbaci har hawaye sai da ta share na tsagwaron tausayin Iffah. Lallai halin da Iffah ke ciki ta cancanci duk mai imani ya zubda mata hawaye, dan sauran Zawjata-almilki na baya mutuwarsu kawai akeji bayan kaisu turakarsa. Amma ita ko kaitanma ba’ayiba, a kwana ɗaya tak da tai a gidan batare da an kammala gagarumin taron bikin da aka shirya ba dominta gata a halin da gara mutuwa da shi…
Bayan idar da sallar isha’i Malikat Bushirat na hakimce a katafaren falonta na uku Malikat Ashwaq ta iso da tawagar hadimanta duba Iffah. Malikat Ashwaq itace mace ta farko ga marigayi Tajwar Haysam ibn Abdull-majeed. Hamshaƙiyar mace ce data isa take kuma amsa suna Malikat. A ƙa’idar Daular ruman matar data haifi yarima mai jiran gado a cikin matan sarkice kawai ake kira da Malikat. Mafi yawanci kuma ana samu ne daga matan farko. Sai dai ga Tajwar Haysam hakan bata faru ba. Dan matarsa ta farko Ameera Ashwaq bata taɓa haihuwa ba kamar sauran matansa, tadai taɓa ɓarin ciki na wata huɗu daga shi kuma bata ƙara ba. A zahiri mace ce isashiya mai baza mulkin da yafi na kowace mace a gidan bayan malikat Bushirat, amma kuma bata da damuwa sam. Ƙaryarka kace ga wani mugun halinta na zahiri saboda tasan kanta. Rana ɗaya aka ɗaura aurenta dana Malikat Bushirat matsayin Zawjata-almilki. Amma itace uwargida. Duk da mulkinta Malikat Bushirat ta fita, ta kuma fita zafi da nuna kishi a zahiri dan sam ita bata da haƙuri, hakan yasa ake matuƙar jin tsoronta fiye da kowace Zawjata-almilki, dan Malikat Bushirat ba kanwar lasa bace ƙwarai da gaske, sai dai mace ce mai son ƙyautatama wanda yay mata da na ƙasa da ita, hakan ya taimaka mata samun soyayyar hadiman gidan. Haihuwar Miran (Yarima) mai jiran gado Eshaan tasa dole sunan Malikat ya koma kan Malikat Bushirat. Wato Sarauniya Bushirat kenan. Amma duk da haka sai Mahaifiyar Tajwar Haysam mai suna Malikat Haseena ta bada umarnin cigaba da kiran Ashwaq da suna Malikat Ashwaq. Hakan ya ƙona ran Malikat Bushirat, sai dai babu yanda zatayi. Amma ta sake tsananta kishin da takema Malikat Ashwaq ɗin fiye da da, yayinda ita kuma Malikat Ashwaq ke nuna tamkar babu komai a zahiri, amma a baɗini hummm.
Koda ta shigo Malikat Bushirat bata nuna tasan da shigowar tata ba. Sai dai ta ɗagama hadimanta yatsu biyu da ya sakasu rige-rigen fara barin falon. Zaune Malikat Ashwaq takai bisa ɗaya daga cikin kujerun falon tanama nata hadiman nuni dasu fita suma. Da sauri suma duk suka fice aka barsu su biyu kawai. A hankali Malikat Ashwaq ta ɗan sakin murmushi daya danne zafin yarfin da Malikat Bushirat ɗin tai mata, ita ta fara gaisheta da tambayar ya mai jiki?. A daƙile Malikat Bishirat da tai kamar zata basar ta amsa mata cike da isa. Nanma Malikat Ashwaq dai murmushi kawai tayi da haɗiye ɓacin ranta. Sosai ta nuna tausayi akan Iffah ta kuma mata doguwar addu’a da bada shawarar mizai hana a kira likita ma ya duba ta ko wani abune daban da wanda ake tunani.
Karan farko Malikat Bushirat ta ɗakko manyan idanunta tai mata kallon tsakkiyar ido. Cikin yamutsa fuska taja numfashi da fesarwa, “Haihuwar magajin Daular ruman daga tsatson Malikat Bushirat rubutacciyar ƙaddara ce da duk yaƙi da gwagwarmayar masu son daƙile hakan. A baya basuci nasara ba, Taya suke tunanin samunta a yanzu kan _Saifulmulk_ ɗi na?. Kamar yanda aka haifesa daga matsayin gudan jinin Shahan-shan, Tajwar Haysam ibn Abdul-majeed. Shima haka za’a samar da Ɗa daga gudan jininsa da izinin UBANGIJI masu lissafi su fara…”
Muƙutt Malikat Ashwaq ta haɗiye yawun dake neman kufce mata, a zahiri kuwa murmushi ta saki da ɗan girgiza kanta. Batare da tace komai ba tai yunƙurin miƙewa domin barin ɗakin tana mai ƙoƙarin danne zuciyarta dake yunƙurowa. Har tayi taku biyu sai kuma ta tsaya, batare data juyi ba ta saki murmushi. “Idan dai har Eshaan ya kasance gudan jinin Shahan-shan ne babu gauraye, muma irin wannan fatanne a bakunanmu garesa kasancewarmu uwaye a wajensa. Fatan alkairi da samuwar lafiya ga Zawjata-almilki…..”
Har tsakkiyar kai kalaman ƙarshe na Malikat Ashwaq suka daki zuciyar Malikat Bushirat, sai dai kafin ta samu wani damar fassarasu sallamar Ameera Danish-Ara da suka kusan kiciɓus da Malikat Ashwaq ya dakatar da ita. Itace mata ta uku ga Tajwar Haysam. itama da tata tawagar hadiman. Kallon juna sukai da Malikat Ashwaq, Ameera Danish-Ara ta saki wani malalacin murmushi a kaikaice. Sai kuma ta matso cikin girmamawa ta gaishe da Malikat Ashwaq ɗin datai mata kallo guda ta ɗauke kanta. Amsa mata tai cike da ƙasaita, kafin ta matsa ta bata hanya ta shige, itama ta fice tawagarta biye da ita.
Saɓanin Malikat Ashwaq ita ta samu tarba daga malikat Bushirat. Dan duk da take mata itama ga Tajwar kuma Malikat Bushirat kishiya a gareta hakan bai hanata risinawa ta gaidata ba da matuƙar girmamawa tana mai tambayar jikin Iffah. Malikat Bushirat dake kishingiɗe har yanzu a yanda Malikat Ashwaq ta barta ta amsa mata da sassauci mai haɗe da jimami. Cike da makirci Ameera Danish-Ara ke nuna tsantsar tausayin Iffah tana mai yin ALLAH wadai ga duk mai hannu akan waɗan nan al’amura.
Malikat Bushirat taɗan jinjina kai irin na ƙasaitattun mata da yamutsa fuska kaɗan, a saman lips ta furta, “Nagode”.
A kaikaice Amera Danish-Ara ta ɗan saƙi murmushi tare da harararta ta ƙasan ido. A zahiri kuwa zamanta ta gyara tare da risinar da kanta. “Wannan abunda ya shafemune ai gaba ɗaya ranki ya daɗe. Domin Zaki ɗammu ne, fatammu dai ALLAH ya warware waɗannan al’amura cikin sauƙi”.