Daudar Gora Book 1 Page 27
A karo na farko Malikat ta motsa laɓɓanta, cike da izza da ƙasaita irin ta manyan masu mulki. “A kaita masaukinta”. Ƙasaitacciyar muryarta ta ratsa zuciyar Iffah tare da girgiza gaɓɓanta cikin ikon harbawar jini. Sunan ALLAH ta ƙara tsarkakewa a zuciyarta dan tabbas Malikat ta cika Malikat ɗin babu tantama. Saboda muryar tata kanta barazanace ga duk mai yunƙurin kawoma girmanta wargi da saka tsantseni a zuciyar duk wani talaka dake a ƙarƙashin mulkinta.
“Ki huta lafiya, cikin aminci da farin ciki”.
Iffah ta faɗa cikin risinar da kanta alamar girmamawa lokacin da take miƙewa bisa taimakon ɗaya daga cikin matan nan. Yin hakan ya sake saka zukatansu a mamaki, ita kanta Malikat Bushirat da kallon ƙasan ido ta bisu har suka fice. A ƙasan ranta tana mai jin farin cikin samuwar Zawjata-almilki data dace da gudan jininta tilo kuma Shahan-shan na ƙasar Ruman gaba ɗaya. A ganinta lokacine daya dace tai yaƙi da maƙiyanta masu yaƙar Zakinta a yanzu dake zagaye da su…..
★★Kamar yanda Malikat Bushirat ta bada umarni amarya Iffah (Zawjata-almilki) an isa da ita sashenta dake gab da sashen matan Tajwar Eshaan su biyu da har yau suke raye, sannan kuma kusa da katafaren sashen Tajwar Eshaan da yafi kowanne gini ɗaukar hankali da kayan kyale-ƙyale da tsagwaren dukiya a cikin Daular Ruman harma da tsantsar tsaro… Sashen Iffah ya kasance shima sashe dake ɗauke da nau’in kayan more rayuwa da a kallo ɗaya mai karatu zai tabbatar da sai dai Zawjata-almilki ɗince kawai kam ta dace da zama a cikinsa. Kamar yanda al’adar take anyi rakkiyar Iffah dake kan keken doki tare da busar sarewa mai daɗin saurare har zuwa sashen nata. Iya masu hurumin shiga kawai suka shiga har cikin bedroom da suka kira matsayin master bedroom nata. Sai dai suna fita ta miƙe daga zaman ɗofanar da tai a gefen gadon, cikin ambaton sunan ALLAH da zubar hawaye ta jaye hular alƙyabar ta ta ƙarema ɗakin kallo na tsahon mintuna uku. Komai batace ba ta ɗauka akwatinta da aka shigo da shi ta fito a ɗakin tare da jawo ƙofar. Bata wani tsaya kallon falon data fito ba, sai dai tabi kowace kusurwa na cikinsa domin lissafa adadin ƙofofin dake a cikin. Ƙofar da lissafinta ya tabbatar mata ta nufa, cikin ɗan jimami da tausayin kai ta murɗa ƙofar mai kalar ruwan gold. Ɗakin ta shiga bayan ta leƙa kanta cikinsa. Shima ɗin dai a ƙayace yake da komai na alfarma. Sai dai komai nasa ya banbanta da kalar na wancan ɗakin. Amma shima duk abinda ke cikinsa royal ne irin kayan da suka dace da gidan hamshaƙan masarautu kamar Daular Ruman. Ajiyar zuciya ta sauke bata samun nutsuwa ba, sai ta son rage nauyi mai danƙarewa a ƙirji kawai har numfashi ya gaza samun damar fita yanda ake buƙata. Jikkar ta ajiye tare da zama bakin gadon ta rushe da sabon kuka………
Wannan dare darene na tarihin da har abadan Iffah bazata taɓa mantawa da shi ba. Badan wani abu ya faru bayan wanda ya faruba, wanda ya farunne bazai taɓa zama shiɗaɗɗe a zuciyarta ba. Kwana ɗaya tak ta kasance cikin ɗimuwa da tsananin kewar ahalinta. Wanda ta riga ta gama sallamawa ta rabu dasu kenan har gaban abada. Sai dai bayan mutuwarta suzo jana’izarta batare da ko kan gawarta an barsu matsawa ba. Sam babu wani barci koda ɓarawo da yaci galabar ɗaukarta a wannan dare. Hakama abincin da aka biyo bayanta da shi na buɗa bakin azumin da tace batacisa ba. Kuka taci ta ƙoshi har
kusan rabawar dare kafin ta miƙe zuwa bayi tayo alwala ta nutsu gaba ɗayanta gaban UBANGIJIN talikai maji roƙon bayinsa. Duk da tsananin tsoro da take a ciki na kasancewa ita kaɗai a katafaren sashen haka ta dinga jarumtar son dannewa a zahiri. Sai dai duk ƙanƙantar motsi yakan saka zuciyarta harbawa da tunanin anzo kashetane.
Tana idar da sallar asubahi barci yafa ce ya shirya, dan duk yanda take faman turesa da son ƙin yinsa sai da yakaita ƙasa, dole takai kwance kan lafiyayyen kafet ɗin dake gaban gadon kafin ƙiftawar ido ta fara sauke numfashi….
Barci sosai Iffah tasha na tsahon lokaci mai tsayi da har sai da aka tadata ta fahimci hakan. Ƙyawawan idanunta dake cike da barci ta buɗe da ƙyar akan matar dake tsaye a gabanta kanta a rissine. Babbar mace ce mai shekaru sosai, sai dai shigarta ta tabbatar da cewa ita ɗin bakomai bace sai hadima a masarautar. Amma kuma da alama hadima ce mai babban muƙami da matsayi….
“Barka da safiya ya Zawjata-almilki”.
Ta katse tunanin Iffah ta hanyar gaisheta. Yunƙurawa tai ta tashi zaune idonta na a kanta, kanta ta gyaɗa da faɗin, “Mama ina kwana”. Dan shekarun girma na matar ya wuce ta zauna saita gaisheta. Sosai ta ga ruɗewa da kiɗima a idanun matar. Cikin yin waige-waige na tsoron kar wani yaji ta zube ƙasa da rawar harshe. “Ranki ya daɗe na roƙeki dan ALLAH wannan sunan yabar fita a bakinki. Kece uwa a garemu, ke kika cancanta mu kira da sunan bani ƙasƙantacciyar baiwa mai miki hidima ba. Sunana shine Diwa, zaki iya kiran Ama (baiwa), ni shugabar hadimai masu kula da tsaftar sashen Malikat ce. An kawo miki abin karin kumallone tare da wanda zasu shiryaki da hadiman da zasu kasance masu hidima a gareki”.
Idanu kawai Iffah ta tsura mata cike da tausayawa. Sai dai komai bata iya cewa ba ta kauda idanunta zuciyarta na ƙuna na raɗaɗin ƙasƙancin da su talakawan ruman ke fuskanta a ƙarƙashin waɗannan masarautu. Hadima Diwa miƙewa tai da sauri ta fita. Mintuna kaɗan sai gata ta dawo tare da wasu mata guda biyu.
“Ranki ya daɗe, waɗannan matan sune zasu shiryaki a yanzu”.
Yanzun ma iyakarta ɗago ido ta kallesu kawai, sai dai batayi musu ba wajen basu damar fara aikinsu. Amma a zuciyarta ta cigaba da yin addu’a sakamakon harbawa da ƙirjinta keyi da sauri-sauri tamkar mai tsoron tunkarar wani abu. Tsaf suka kwance kitson dake kanta, dogon gashinta da mafi yawan ƴan ƙasar ta Ruman keda ya bayyana.
“ALLAH ya ƙara miƙi tsahon rai da lafiya, wannan lokacine na wanka”.
Komai Iffah batace musu ba ta miƙe, dan tanabin huɗubar Kaka ne daki-daki. Da zata shiga bayi dakatar da su tai daga ƙoƙarin binta da suke.