Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 24

Sponsored links

Wani irin cije lips yayi daga can, hawayen da tun randa labarin auren wadda ya fara so yake kuma kan so yazo masa da wanda yafi ƙarfinsa suke kwaranya ya kasa sharesu suka shiga rige-rigen zubowa daga idanunsa, yasan ta ƙare kuma, abinda ya rage kawai ƙyautatama masoyiyarsa koda hakan zai kasance sadaukarwa ta ƙarshe da zaiyi a rayuwarsa.

“Na barki lafiya, ki kasance cikin aminci da kariyar UBANGIJI”. Ya faɗa harshensa a sarƙe da yanke wayar a lokaci guda.

Wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga gudu a fuskar Iffah, bata san tana son Sir Fawzan ba sai a yanzu. A yanzun da kowa zai iya kiransa ƙurarren lokaci a rayuwarta. Zata cigaba da masa fatan alkairin samun madadinta koma wadda ta fita, jin kamar motsin ana tunkaro ɗakin yasata saurin kwanciya taja bargo har saman kanta….

Muhammad Zayyan!”.

 

Kaka ya kira Babiy tamkar yana gabansa cikin matsanancin damuwa da firgici na zahiri dake kan fuskarsa. Ɗago kansa dake sunkuye yay a hankali shima tamkar yana a gaban Kakan. Hakan ya bayyana jajayen idanunsa da damuwa ta rinar. Sun rabu ne tun a wajen ɗaurin aure basu dawo nan gidan ba suka wuce Jumna.

 

“Na’am Baba”.

 

“Kayi haƙuri. Karku zama masu baƙin ciki kai da matarka. Ku zama masu juriya da karɓar ƙaddara rubutacciya daga UBANGIJI. Nasan akwai raɗaɗi, nima kuma makamancin irinsa nakeji a ƙirjina. Sai dai bazan gaji da faɗa maka *_Kibiyar ajali sulke baya tareta sai ta gitta ba_* kamar yanda babu wata duster data isa goge abinda alƙalamin ƙaddara ya rubuta. Mu mun wuce yanzu, dan mungama namu ku ya rage kuyi naku mu barma UBANGIJI sauran, dan dama duka nasa ne. Iyyani itace zata shiryata kafin isowarsu ɗaukarta, nau’in turaren da yake a cikin gidanka kawai nake buƙatar fitar ƙamshinsa daga jikinta. Ta kuma sha iya adadin madara datake gidanka kawai daga yanzun har zuwa wayewar gari. Ta kwana a ɗakin daba shi aka ajiyeta ba. Karta karɓa daga wanda zuciyarta tai rawa a kansa. Ta zama ƴar kallo a takun farko, ta zama kurma a shigar farko, ta zama mai rauni a tawagar farko, tasa a ranta kariyar UBANGIJI na tare da ita. Na barku lafiya”.

Ummu ta juya ta kalla Babiy dake riƙe da wayar a hannu tamkar dasashen gunkin da akai ado dashi domin tunawa a tarihi. “Lafiya kuwa? Baba ma baida wata mafita ko? Shiyyasa yaƙi dawowa tanan ya wuce gida?”.

 

 

Idanu ya cigaba da tsura mata tsahon wasu sakanni harta fara kuka, ya ciza leɓensa na ƙasa yana mai haɗiye abinda ya tokare masa maƙoshi. Gefenta ya kai zaune, tamkar mai bitar karatu ya shiga maimaita kalaman baba a zahiri _“Iyyani za ta shiryata kafin isowarsu ɗaukarta, nau’in turaren da yake a cikin gidanka kawai nake buƙatar fitar ƙamshinsa daga jikinta. Ta kuma sha iya adadin madara datake gidank…….”_

 

Kallonsa Ummu tai da share hawayenta a lokaci guda, cikin rashin fahimta tace, “Mi kake son faɗa?”.

 

Kansa shima ya girgiza mata. “Ba dagani bane ba, Baba ne. Amma na kasa fahimtar komai Jamaima. Ko ke kin fahimta?”.

 

Har zatace a’a sai kuma tai ɗan jimm idanunta masu girma da su Iffah suka gada a kansa. Itama maimaita kalaman tayi kamar yanda ya faɗa har sau uku, “Idanfa har na fahimta, Baba yana nufin _Iyyani ta shirya Iffah da kanata, idan sunzo da wani turare karmu bari tai amfani da shi, sannan ko taje can an bata wani abu kar taci……, Kaga kenan daga nan mu saka mata turaren, sannan mu bata abinci taci cikinta ya cika. Mu kuma……”

Numfashi ya ja daga hancinsa a hankali ya saukar a ƙirjinsa, itama ta sauke numfashin mai haɗe da zubar hawaye sakamakon dakatar da ita da yay da hannu alamar ya fahimta ba sai ta ƙarasa ba. duk da bawai nauyin da zuciyarsa tayi ya ragu bane, ya dai samu sassauci daga kalaman Baba duk da basu san manufarsuba kai tsaye. Sai dai bin umarninsa a garesu tilas ne…….

★ Tsaf Iyyani ta shirya Iffah dake faman zubda hawaye har yanzu cikin shiga ta alfarma kamar yanda Kaka ya bada umarni. Wata haɗaɗɗiyar riga ce da akanga irinta kawai a jikin hamshaƙan matan gidan sarauta na ƙasar ruman mai kama da alƙyabba da ita kanta Iyyani bata taɓa sanin a kwaita a gidansu ba Kaka ya kawo yace a saka mata. Duk da shirine bana daɗin rai ba tayi ƙyau matuƙa. Ga wasu nau’in sirrika na ƙamshi na tashi daga jikinta har suna hawa kai. Tsaff Ummu da kanta ta shirya mata wasu abubuwa masu muhimmanci nata duk da sun san zama ne na taƙaitaccen lokaci ga ƴar tasu mace tilo data rage yanzu. Daga Babiy har Ummu zama sukai suna mata nasiha, nasihar kuma gaba ɗayanta tafi ƙarfine akan addu’a, ta kula da addininta, azkar, karatun alkur’ani kar tai sakaci da su. Babiy da kansa ya ɗakko wayar Fariha ya bata yace ta ɓoye kozasuna rinƙa jinta, baima san ta Arfa ma na hanunta ba. Isowar jama’ar daular ruman ta katse zaman nasu. Inda mayan matan da suka shigo gidan tare da rakkiyar tawagar hadimai suka buƙaci a basu amarya da ruwa mai ɗumi su shiryata. Kan Babiy a ƙasa ya basu amsa da

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button