Daudar Gora Book 1 Page 20
★Bayan cikar awanni biyu da tafiyar Babiy sai gashi ya dawo, dawowa irin wadda ya saba a duk lokacin da makamancin kira irin wannan ya samesa daga daular Ruman. Yanda ya kafe Iffah da idanunsa dake zubda hawaye ya saka Ummu zubewa ƙasa cikin kuka. “Abu Hanash itama zamu rasata ko? Itama ka ɗaura mata aure da Tajwar…..?”
Hawayene masu ɗumi da ƙuna suka ziraro a idanun Babiy, ya girgizama Ummu kansa a hankali alamar a’a, tare da girgiza kan nasa kuma alamar tayi shiru. Hawayen nata ta share kamar yanda ya buƙata, sai dai jikinta bai bar tsuma ba. Kamar yanda Iffah data kafesa da idanu bata iya ko ƙyaftawa ba. Ummu ta sake gyara zamanta da fuskantar Babiy da ƙyau….
“Idan ba abinda muke tunani bane to minene ya faru?”.
“Ki kwantar da hankalinki babu komai f…..”
“Bazan taɓa yarda babu komai ba. Sai dai idan kana so ka rufeni ne. Hakan kuma shine mafi ƙololuwar kuskuren da banajin zan iya yin afuwa gareka a kanshi. Dan inaji a jikina zuwanka masarauta nada nasaba da rayuwar yarinyata data rage min, idan har zuciyarka ta iya ɓoyewa ƙwayoyin idanunka basu lulluɓe komai ba, garama ka sanar min”.
Babiy ya fahimci idon Ummu ya rufe ta manta Iffah na wajen, dan haka ya cigaba da ƙoƙarin ganin ya kufcema faɗar abinda yazo da shi har sai sun keɓe amma ta dage akan itafa ya faɗa mata a yanzu. So yake ya buɗe ido amma bashi da sauran ƙarfin zuciya a yanzu, dan haka a sanyaye ya rumtse idanunsa da launinsu yay matuƙar komawa ja. “Ba’a ɗaura mata aure da shi ba. Sai dai….” ya kasa ƙarasawa.
“……Sai dai me? Dan ALLAH ka faɗa min”. Ummu ta faɗa tana mai sake fashe masa da kuka mai matuƙar sake ɗaga masa hankali. Miƙewa yay yunƙurin yi tai saurin riƙe masa ƙafa. Babiy ji yake shima kamar ya fashe da kuka ya huta kawai. Ya dawo ya durƙusa gaban Ummu tare da riƙo mata hannu, “Akan abinda suka faɗa munada mafita tunda yasha ban-ban dana baya Jumaima. Dan haka na gama yanke shawarar zamu bar garin nan dama ƙasar gaba ɗaya a daren yau insha ALLAH. Dan sun buƙaci izinin neman auren Iffah ne a gareni, sun kuma bani damar zuwa nai shawara daga nan har zuwa ƙarshen makon nan”.
Kafin Ummu ta samu damar cewa wani abu sulalewa da faɗuwar Iffah a lokaci guda ta riski kunnuwansu. A tare suka zabura kanta jikunansu na matuƙar rawa da tsuma. Ummu ta fashe da kuka dai-dai tana ɗago Iffah dake wanwar a ƙasa taga ta koma yaraf alamar babu rai a tare da ita…..
Sosai kukan Iffah ya sake ɗaga hankalin Babiy. Dan tunda aka zuba mata ruwa ta farfaɗo ta haɗe kai da gwiwa. Suma idanu kawai suka zuba mata suna hawayen zuci, rikicin yana a kantane kawai, amma sune suka fita jin raɗaɗin a zuciya saboda ita akwai ƙuruciya tare da ita. A ganinsu bai zama lallai ma tana hange irin wanda su suke matane ba.
Kusan mintuna talatin suna a haka, kafin Babiy yay ƙarfin halin miƙewa suma yay musu umarnin su tashi su koma ciki. Sai da taimakon Ummu Iffah ta iya miƙewa, har sun kusa shiga ɗakin ta tsaya, ɗagowa tai ta dubi Ummu ta juya ta dubi Baby hawaye na sauka da gudu bisa ƙyaƙyƙyawar fuskarta.
“Bazamu gudu ba Babiy, zan aure shi….”
Kaɗan ya rage Babiy yaci uban tuntuɓe saboda firgitaccen furicin Iffah mai kamanceceniya da gawurtaciyar sautin saukar aradu cikin tsakkiyar duhuwar dare. Ummu ma dai da taima Iffah sakin bazata ƙirji ta dafe dukanin idanunta na firfitowa…..
Iffah ta share hawayenta da sakin murmushi a karo na farko. “Ummu! Babiy! ku kwantar da hankalinku, kar kuma ku ɗauka ba’a cikin hayyacina nake ba. Nasan burinku shine ku kuɓutar dani daga mutuwa, sai dai kuma a duk inda zanje ku sani tana tare da nine. Wannan azzalumin ba guje masa ya kamata ayi ba, tunkararsa ya kamata ayi. Kamar yanda kaka ya faɗa, a wasu lokutan gujema ƙaddara ba mafita bace sake kirawowa kai halaka ne. Amma tunkararta gaba da gaba ƙarfafa imani ne sannan jarumtace. Shin idan mun gudu kunada tabbacin zamu iya tsere musu bayan ƙasar a hanunsu take? Sannan idan mun tafi ina zamuje bayan babu inda muka sani sama da ƙasar Ruman. Fir’auna ma da yay nasa zamanin mulkin da ko kama kafarsa wannan shaiɗanin baiyiba UBANGIJI maida ANNABI MUSA (A.S) yay cikin gidansa ya rayu bisa ƙudirarsa da tabbatar masa shine mai iko akan kowa da komai. Azzalumin nan ba gudun masa ya kamata ayi ba, daƙilesa ya kamata ayi, domin idan ni kun kuɓutar dani, su sauran iyayen da zasu iya fuskantar makamancin halin da kuke ciki fa bayanku?. Babiy zanyi biyayya kamar yanda ƴan uwana sukayi, kuma ku sani da iznin ALLAH nice zan kashes……..”
Cikin rawar jiki Ummu ta zaburo tare da toshe bakin Iffah. Sai faman waigen bayansu take domin sanin dakarun Daular Ruman na ƙofa gidan har su biyar. Babiy ma gaba ɗaya kalaman Iffah sun sake rikitashi. Sai dai kafin wani cikinsu ya samu damar cewa wani abu ta shige cikin ɗakin. Idanu suka tsirama juna shi da Ummu harna tsahon mintina biyu, kafin Babiy yay ƙarfin halin janyewa yana mai jan nannauyan numfashi da barin wajen ya shige ɗakinsa. Da ƙyar itama Ummu ta sauke numfashin, har zatabi bayan Iffah sai kuma ta fasa ta nufi ɗakin Babiy ɗin itama.