Daudar Gora Book 1 Page 15
……..Zaune takai a kujerar dake duban tasa tana mai kallon agogon hanunanta. Ya saki murmushi cikin kafeta da idanu. “Daga zuwa sai duba agogo?”.
“Hakan dolene Sir, domin ko lokacin islamiyya zan cinye anan. Kaga kenan sai da tsantseni”.
“Okay”.
Ya faɗa yana gyara zamansa. “Ba buƙatar maimaita abinda ya faru baya, na gaba kawai yanzu shine zanyi iya ƙoƙarin ganin na haɗu da abokin nawa koda ta waya ne, kin san aikin nan nasu yana hanasu samun isashen lokaci matuƙa kasancewarsu manya dake tare da babbar kafar yaɗa labarai mai aiki da kamar duniya gaba ɗaya. Ke yanzu a gareki miye shirinki?”.
Kafaɗa Iffah ta ɗan ɗage cikin jan iska da hurowa. “Kusan dukan shirina a kammale yake, burina kawai nasamu yin hira da African Aye👁️🗨”. “Indai hakane haɗuwa da abokina kawai ya rage mana, fatana dai bayan ni kar wanda yasan wannan hatta a gidanku, inba hakaba zamu iya shiga haɗarin da har burin rayuwarmu ma bazai cikaba bayan wannan. Nikuma zanyi duk yanda zanyi insha ALLAHU wajen hana wannan sirrin fita daga gareni….”
“Shi abokinka ɗin fa?”.
“Baki da matsala da shi domin shi aikinsa ne”.
Kai ta jinjina masa fuskata cike da murmushi. Sai kuma ta rissinar da idanunta alamar jin kunyarsa saboda kallon daya kafeta da shi. Kunyar nada nasaba da tuna yanda ta dinga wancakalar da shi da manufarsa a sanda yake malaminta. Sai gashi shine na farko data fara tunkara da matsalata a yanzu duk da kuwa tana kallonta a kan matsalar data shafi kowa na ƙasar Ruman ne. Sautin murmushinsa ya sakata ɗagowa ta ɗan kallesa, sai kuma ta sake kauda kanta gefe itama tana murmushin.
“Hummm!”
Ya faɗa yana miƙewa. Itama miƙewar tayi batare data yarda sun sake haɗa ido ba. “Kije gida zamuyi waya”.
“Nagode sir, ALLAH ya tsare gabanka da bayanka”.
Jin sautin murmushinsa ya tabbatar mata jin daɗinsa, amma sai tai gaba da sassarfa tunkan ya sake cewa komai……..
Katafaren ɗaki mai ɗauke da ƙayatattun kayan more rayuwa, kwance take bisa lafiyayyen gado da dukkan nau’in shimfiɗunsa suka kasance na alfarma. Sautin dariyar dake tashi cikin kunnuwanta tamkar mafarki ya sata buɗe idanu, cikin tsumar jiki ta ture lallausan bargon da take ciki, tamkar walƙiya ta dire ƙasan lafiyayyen kafet ɗin dake malale gaban gadon tai kneel down tamkar mai neman gafara, kanta a risine alamar nuna tsantsar girmamawa…..
Tamkar shirin film ko labaran almara tsohuwa tukuf sanye cikin jajayen kaya ta bayyana bisa baƙar kujerar ƙarfe mai ɗauke da adon gold a cikin ɗakin. Baƙace matuƙa mai tsananin muni da jajayen idanu, yanda ta zauna ƙafa a harɗe kai ka ɗauka itace Shahanshan ɗin…..
“Lafiya da tsahon rai su ƙara kasancewa a rayuwar *_Uwa_* mai share kukan masu kuka”. Hamshaƙiyar matar ta faɗa cikin tsantsar girmamawa ga tsohuwar dake harɗe saman kujerar tata tamkar sarauniyar ingila.
Cike da isa da ƙasaita tsohuwar taja wani kakkauran numfashi da sake faɗaɗa girman ƙofofin hancinta ta hanyar hurashi, ƙara harɗe ƙafafunta tai tana mai motsa yatsun hanunta, idanunta jajaye kafe akan matar. Cike da isa da ƙasaita mai ɗauke da rashin daɗin muryarta ta tsufa ta fara magana. “Ta-ƙurya kin kusa cin nasara wajen cika sharaɗi na biyu akan alƙawarinmu. Na tayaki murna, saura sharaɗinki na ƙarshe, mafi wahala a cikinsu”.
Ƙasa ta ƙarayi da kanta cike da girmamawa a gareta, da dukkan ƙarfin zuciyarta ta furta, “Kece madubin nasarata Uwa!, duk inda akaga naje da jagorancinki na isa. Yanda na cika na farko shima na biyu zan cika sa, nayi alƙawarin cika na ƙarshe ma fiye da yanda kike tsammani…..”
Jajayen idanunta masu kama da garwashin wutar gidan biredi ta ɗago tana kallon ƙyaƙyƙyawar kuma hamshaƙiyar matar dake gurfane a gabanta. Ta ƙyalƙyale da wata dariya mara daɗin saurare ga kunen kowa, sai kuma ta gimtse tamkar ba ita tayi ba tana zaro manyan jajayen idanunta kamar na dodanni. “Ta-ƙurya nasan zaki iya, sai dai akwai wani babban ƙalubale dake tunkaro cikar nasararki ta biyu, kuma gab yake da cimmawa, idan baki gaggauta datsesa ba, zakiyi biyu babu”
A razane ta ɗago tana kallonta cikeda bushewar zuciya, sai kuma ta maida kanta da sauri ta rissinar “A gafarceni Uwa, a kawar da ko miye mai son yima cikar burina kutse. Na rantse da ALLAH daya halicceni, koda cikin yankin ahalina ne bana buƙatar numfashinsa Uwa!!”.
Dariya ta sake ƙyalƙyalewa da shi sai kuma ta gimtse fuska. Kanta ta shiga girgiza mata da dukkan isa. “Ta-ƙurya wannan karon akwai banbanci da koyaushe, dama na taɓa faɗa miki bayan cikar nasararki ta farko akwai ƙalubale dana gani akan cikar ta biyu, sai dai ba’a buɗe mun komaiba a wancan lokacin, alamar haka na nuna ƙarfin taurarin mai yunƙurin, amma a daren jiya dana tsananta bincike akan mafarkinki na gano wani yanki da ƙyar. Ƴar shilar suda na ƙoƙarin yin cara irin ta gawurtattun zakaru a kunnen bututu da taimakon wata zuciya mai son kusantar tata.”
“A taimakeni a kawar mun dasu gaba ɗayansu Uwa. Ko a bani damar kawar da su da kaina”.
“Hhhhhhh!!!! Ƙaddarar ƴar shilar bata mutuwa bace cikin sauƙi. Tana kuma da ƙarfin taurarin da zata iya cin nasarar dusashe naki”.
Bugawar da ƙirjinta yayi ta zata zuciyarta ce zata fito ta bakinta dan tsabar razana. Ta kafeta da idanu cikin wani irin yanayi mai wahalar fassara. Sai kuma tai saurin maida kanta ƙasa ta rissinar tana faɗin, “A gafarceni Uwa”.
Wani irin kakkauran numfashi mai cike da gargaɗi tsohuwar taja, cike da ƙasaita tana yamutse mummunar fuskarta ta cigaba da faɗin, “Zamu iya samun mafita sai dai akwai ruɗani a cikinta. Har zuwa yanzu kuma ban samu buɗewar ruɗanin ba kai tsaye. Dan haka kina da zaɓi biyu. Kodai ki ƙara yin duk yanda zakiyi igiya ta ƙullu tsakanin Malik-alMuluk da wannan ƴar shila muyi duk yanda zamuyi tazama cikamakin aikinmu na biyu, ko kuma ki barta ta cimma burinta…….”