Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 17

Sponsored links

“Shike nan ALLAH ya tsareki, dan ALLAH kiyi maza ki dawo kafin Abbin ku ya dawo gidan nan ko ɗan uwanki”.

“Insha ALLAHU Ummuna”. Iffah ta faɗa tana rungumeta. Shafa kanta Ummu tai tana murmushin ƙarfin hali itama, dan ba wani zuciyarta ta samu nutsuwa bane ita dai, ta bartane kawai saboda tace fitar ta shafi karatunta. Amma zata cigaba da rakata da addu’a harta dawo………✍

Kasancewar wajene daba kowa ke shiga ba anyhow yasa sai da Iffah tai kiran Sir Fawzan bayan saukarta a bakin gate. Umarnin bama security ɗin wajen wayar ya bata. Bayan yayi magana da security ɗin suka bata damar shigewa batare data san miya faɗa musu ba. Tafiya take a nutse tana ɗan kallon wajen da tsarinsa. Dan babban garden ne mai cike da ababen kallo da ni’imtattun korayen ciyayi da ƙawatatun filawoyi. Ta taɓa shiga sau biyu a dalilin taron makarantarsu ta Islamiyya da aka gudanar a wajen. Ya riga ya faɗa mata inda zata samesa, dan haka kanta tsaye take nufar wajen ranta fes da nishaɗi tamkar ance mata ga wuƙa ga maƙoshin Tajwar Eshaan ta yanka.

 

Sai da taje kusan ƙarshen garden ɗin ta tsaya, sai kuma ta shiga canki in canka na number wajen daya bata kasancewar akwai rukuni-rukuni na ɓoyayyun wajen hutawa da manyan mutane sukafi tu’ammali da su idan basa buƙatar wata hayaniya. Cikin ɗan ɗage kafaɗa ta nufi na farkon da zuciyarta tafi karkata. Ƙawatuwar wajen takai mai kallo shagala harya iya manta abinda ya kawoshi, kamshin firanni da wani iska mai busawa a hankali kaɗai na dabanne. Jitai kamar da shakku na shigowarta wajen, amma sai ta dannesa a ƙasan zuciya ta cigaba da takawa tamkar mai sanɗa tana leƙe-leƙe. Ta isa kusan tsakkiya zuciyarta ta shiga gargaɗinta ganin babu alamar akwai mutum mai numfashi a wajen, cak ta tsaya tare da ciro wayarta domin neman sir Fawzan.

 

“Ya ALLAHU”.

 

Ta faɗa jin ana sanar mata bata da kati kona sisi a wayar. Kamar zatai kuka ta sauketa daga kunenta tana ɗan ƙara danne-danne da cigaba da takawa a hankali batare data san mike a gabanta ba. Kaɗowar iska da sassanyan ƙamshin turare mai daɗin gaske ya sakata tsayawa cak ƙirjinta na harbawa da ƙarfi. Fararen idanunta ta janye daga kan wayar tare da ɗago kanta gaba ɗaya, a kan mutumin dake kishingiɗe bisa wani lallausan jan darduma daya haɗu da kalar korayen ciyayi ya bada ƙyaƙyƙyawan tsari ta sauke. Rabin jikinsa akan tum-tum yake. Kansa a risine yana kallon lap-top ƙirar kamfanin apple dake akan wani ƙaramin tum-tum ɗin itama. Gefensa kaɗan wani ƙyaƙyƙyawan bowl ne fari na tangaran, sai butar shayi kalar golden akan tray dake tabbatar da set ne dan harda ƙananun cups nashan shayi. Sanye yake da ƙananun kaya farare tas da suka fidda ainahin suffarsa ta masu ta’amalli da ƙarafuna, gashi sun sake fidda ainahin hasken fatarsa da sheƙinta irin na masu jin daɗi. Duk da tana a gab da shi aikinsa yake hankali kwance baiko nuna alamar yasan da zuwanta ba.

“Mi kake buƙata?”.

“Mi kake buƙata?”.

Sassaanyar muryarsa mai zurfi da kamewa ta daki kunenta da alamar akwai wanda yay tsammani ba ita ba. Ƙirjinta ne ya sake harbawa har tanaji kamar jininta daya tsinke na neman biyo hudojin gashin fatarta ya fito. Bata da niyyar cewa komai, gata tsaye tamkar an dasata ta gagara ɗaga ko ƙafa ɗaya tabar wajen duk da haka zuciyarta tafi buƙatar da tayi. Jin shiru ba’a amsa masa ba, ga tsaiwar mutum yanaji har yanzu a gabansa ya sashi ɗago lulu idanunsa masu haske da baiwar bakin ƙwayar tsakkiyarsu ya sauke a kanta. Komai tsayawa yay daga garesa, kamar yanda Iffah ma hatta kaɗawar iskar wajen ta tsaya mata cak… Fuskarsa dake a kame da kwarjini ya sake tsumewa yana sassauta girman idanunsa tamkar mai son lumshesu da gayya.

A fisge, tamkar an jawo furucin daga bakin Iffah ta yamutsa fuskarta da ƙanƙance manyan fararen idanunta da tun a kallon farko ta kaudasu da ga kansa alamar kunya irin ta mace, “Idan ma kai aljanine wlhy nafi ƙarfinka. Wace irin jaraba ce duk inda nai saina ganka”. Ta ƙare maganar da hura bakinta.

 

Kamar yanda bai motsa daga yanda yake ba haka bai ce mata komai ba, bai kuma janye idanunsa a kanta ba har yanzu. A zuciyar Iffah fa ta fara tsorata dajin tabbacin mutumin nan fa ƙila aljani ne. Amma sai taga idan ta nuna tsoronsa fa zai ma iya kasheta, saboda a yanzu haka ma ƙarfin hali take, tana matuƙar jin kaifi da tasirin idanunsa a dukkan ɓargon jikinta da jijiyoyi da gudanar jini. Amma sai ta dake a ƙasan ranta tana karanto addu’ar neman tsari da aljanu.

Kusan tunani iri ɗaya ne a zukatansu. Dan shima dai zuciyarsa ta ƙara yarda wannan abar aljana ce kawai, yana ganin kuma ya kamata yasan miyasa take bibiyarsa ne?. Nisan data fara masa a idonsa ya fahimci tabar wajen, ilai kuwa can ya hangota tana tafiya cikin sassarfa ta nufi ƙofa. Cin karo data kusan yi da mutum ya sata ja gefe da sauri. Ɗaya daga cikin matasan datai masa gani biyu da su ne, cikin nuna alamar mamaki da tsuke fuska yake kallonta. Harara ta balla masa ta ƙyaɓe fuska da raɓashi ta wuce, danji take ƙafafunta tamkar ba’a kansu take takun ba…..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button