Daudar Gora Book 1 Page 108
Ya zayyane mata labari tiryan-tiryan kamar yanda ya bincika. Babu kuma banbanci da abinda ta gani a wancan video ɗin na farko. Ya kare da faɗin, “Wlhy har yanzu akan binciken inda aka kaisu ake amma babu labarinsu. Nima kuma a yanzu haka ina yin nawa ta ƙarƙashin ƙasa amma har yanzu ban samu wani bakin zaren ba….”
Kukan data fashe masa da shi ne ya katsesa daga jawabin nasa. “Ba zaku gansu ba, ba zamu ƙara ganinsu ba, sun rabani da su kamar yanda suka rabamu da ƴan uwana. Wlhy nima sai na kasheshi kamar yanda ya kashesu. Na rantse bazan barsa ba, bazan taɓa barinsa ba. Yanda ya halakasu da macijin tsafi sai na halakashi da dafin maciji na gaskiya. Shima sai ya ɗanɗa……” kuka ya sarƙeta ta kasa cigaba da magana…
Cikin tashin hankali daga can Sir Fawzan ke faɗin, “Iffah ban gane ba. Dan ALLAH ki daina kuka kimun bayani, kaina ya kulle dan ALLAH kiyi shiru kinji, wlhy na miki alkawarin taimaka miki akan koma minene, koda kuwa nima zan rasa rayuwata ne…..”.
“Babu wannan lokacin sir, bani da shi. Kai dai kawai ina zan samu dafin maciji mai haɗarin gaske?”.
“Ya ALLAHU! dan ALLAH ki faɗamin mike faruwa? a yanda zan fahimceki”.
“Idan bazaka samamin abinda nake buƙata ba na Barka lafiya”.
Yana hello-hello bata sauraresa ba ta yanke wayar, koda ya sake kira bata ɗauka ba, da taga zai dameta ma sai ta jefa shi a black list. Kaikawo ta cigaba dayi a ɗakin tana kuka. Komai ya cakuɗe mata, zuciyarta ta gama ƙeƙashewa da bushewa. Ta sallama duk wani ɗan sauran rangwamenta. Abinda kawai idonta da zuciyarta ke gani gawa huɗu ta ahalinta kwance duk a dalilin mutum ɗaya tak, lokaci yayi da zatai abinda ya kawota itama dan bai cancanci cigaba da rayuwa ba mutumin nan sam, tayi alkawarin tare zasu mutu, amma sai ta kasheshi ta kuma bayyanama duniya wanene shi.
Yanda taci kuka ta fita hayyacinta dole ta bama duk wani tausayi, da ƙyar ta iya zaman rubuta komai da ya rage, ta tattare ga Ajmaal, a ganinta ta gama tattare dukan abinda ya dace ta tattare masa. Hatta ƙudirinta na kawar da Shahan-shan ta hanyar dafin maciji bata ɓoye masa ba. Ta kwashe videos ɗin dake wayar zuwa wayarta ta turama Ajmaal ɗin, takumayi gajeren video da kalaman masu girgiza zuciya har biyu. Ɗaya na Ummu da su Kaka ta roƙa ya bamawa, ɗaya kuma na al’ummar ƙasar ruman ne baki ɗaya. Shima tai masa godiya da fatan alheri da nasara har ƙarshen rayuwa.
Barrister dake jin kamar ya ƙwaɗa wayar da ƙasa ya rumtseta a hannunsa da masifar ƙarfi, a karo na farko wasu zafafan hawaye suke silalo masa. Jarumar zuciyarsa zugasa take kada ya yarda ya amince koda zai rasa rayuwarsa, yayinda wani ɓangaren kuma ke haska masa iyalansa da yafi so fiye da komai a duniya a halin yanzun. Wannan shine tashin hankalin mafi ƙololuwar girma daya taɓa cin karo da shi a rayuwarsa….
Washe gari da safe wujiga-wujiga ya wayi gari, amma hakan bai saka ko gezau ga mutanen ba. Sai ma duk wani details daya shafi case ɗin da suka dire masa. Mamaki da tsoronsu ya sake mamayesa ganin duk wani abinda ke hannunsa ne. Kuma ya adanasu ne a mabanbanta wajeje. Akwai wanda a gidansa suke, akwai wanda a office suke, akwai na mota ma. Amma abin mamaki gasu duk a gabansa sun tattaro sun kawo masa. Tabbas ya sadaƙar, dan mutanen nan hatsabibaine na innanaha. In har zasu iya hakan a kankanin lokaci bayaji idan ya bijire musu iyalansa zasu tsira kuwa….
“Barrister baka da lokacin dogon tunani, ka shirya dan a yau oga ke son ka tattaro masa duk bayanin da yake buƙata a wajen mutanen can. Ciki har da sanin su wanene ainahin masu aikin, da inda suka ɓoye Abu Hanash da ɗansa”.
Karan farko Barrister ya dubeshi a razane, har ƙoƙarin taune harshe yake wajen faɗin, “Kana nufin dama baku bane ke riƙe da su Abu Hanash ɗin…?”
Saurayin yay ɗan waige-waige alamar baya son wani yaji, cikin raɗa-raɗa yace, “Bamu bane Barrister. Muma kuɓutar da su muke son yi har ma da kai kanka. Sai dai ban san miyasa oga bai son ka sani ba ya zaɓi baka aikin a kife”.
Ba ƙaramin zabura Barrister yay ba jikinsa har rawa yake ya matsa gab da saurayin. “Dan ALLAH kada ka yaudareni ka faɗa min gaskiya”.
Da sauri saurayin ke masa nuni da yay ƙasa da murya kar wani yaji, “Barrister wlhy kaji na rantse maka abinda na faɗa maka shine gaskiya. Na kuma sanar maka ne saboda ka bani tausayi. Amma iyalanka kansu suna zagaye da tsaro ta yanda wani bazai taɓa iya samun damar cutar da su ba, kai kanka kusan sati uku fa muna tare da kai batare daka sani ba. Oga ba azzalumi bane ba, amma ban san miyasa bai son kasan taimakonku zaiyi ba. ya kamata kaima ai ka gane hakan tun farko musamman aikin daya baka ɗin, taya wanda zai cutar da kai zai kuɓutar da kai?, taya wanda zai cutar da kai zai ɗauraka akan hanyar abinda kake nema ya baka bakin zarensa haka cikin sauƙi?”.
“Hakane wlhy ɗan uwa hakane. Kaina ne ya kulle a ruɗani nake gaba ɗaya. Nagode nagode yanzu kam ka bani ƙwarin gwiwa, insha ALLAHU kuma sai na bada mamaki. Dan a wannan gaɓar sai su Abu Hanash sun fita da izinin UBANGIJI, zan kuma gano koma wanene da hannu a kan ɓoyesu”.