Bakon Lamari 21
Ameerah ta lumshe idanu tare da cewa.
“To Anty kawai idan tai niyya tasa ya haɗe mu rana ɗaya mana?”
Anty tace.
“Barni da Hajiya Binta, dani take maganar ta ɗauka yadda nake mata a fuska har zuciyata haka yake? to sai da na laluba nagano zamu kwashi dukiya wajan ɗanta sannan nai mata kwanton ɓauna na shiga Jikinta Burina Ahmad ya aureki koda baki ce kina son shiba dama da niyyar na haɗaku bare da bakinki kince kina son sa sabida haka ki kwantar da hankalinki Ahmad Mijin kine Uban ƴaƴanki ki aure shi ki hayayyafa Komai nasa ya dawo namu Hatta uwar tasa ma sai yadda kika ce zai mata Sabida a rayuwa ina baƙin Cikin Mutum Biyu Hadiza da Binta sun fini komai Ita hadiza mijin ƴarta daya tsaya mata wannan abu na ƙona Mini rai Shiyasa jiya danaji labarin auren ta ya Mutu yau sai da nai sadaƙa sabida Murna ita kuma Binta Duba kiga kaf ƴaƴanta mata Uku dake ɗaki bamai auren talaka Shima Ahmad jibi yadda Allah ya ɗaukaka shi a aikin shi Lokaci ɗaya ga kuma kasuwancin sa wanda naji ashe ƙatuwar plaza ya saya ya zuba kayayyaki kuma ance kayan ma daga ƙasar waje ake shigo dasu ya damƙawa kamal a hannunsa yake kula masa da komai na ɓangaren plazar,sannan ya sami yarinyar dazai aura ƴar manyan Mutane, Binta a yanzu tafi ƙarfin Komai a rayuwa Hutu da jin daɗi kullum ƙara Huda ta yake shiyasa Sai da nai yadda nai da Gulma da Kirsa na rabasu da Hadiza don Muddin Suka haɗa kai ni tawa ta ƙare Sannan Kuma nasan yadda nai nake amshe saƙon matan gidannan Wanda take bani tace a raba musu na wajan Ahmad nake riƙewa nakuma toshe hanyar da zataji Duk dan tai baƙin jini acikin su to Alhamdulillahi wannan tarkon nawa ya kama domin kuwa yanzu duk matan gidannan haushin Binta suke ji suna ɗaukarta mace mai son kanta da izza Yanzu tarkona na gaba ki Auri ɗanta daga nan kuma ta kaɗe har ganyenta wallahi”
Zare idanu Ameerah tayi har zufa na keto mata.
“Haba Anty dan Allah ki bar yin haka wallahi babu kyau ko kaɗan Sabida bakisan ranar mutuwar kiba”
wata dariya Anty ta kwashe da ita kafin tace.
“Ke yarinya ce Ameerah baki san dawan garin ba ada can ma kafin a haifeku Mijin Binta Nada kuɗi Mijin Hadiza nada kuɗi kafin ya kwanta ciwo Ni kuma mijina baya cas bare as suke mana komai har Allah ya bashi malamin makaranta Kina kallo fa daga Alhaji sai Sha’aibu sai babanki sai sauran ƙannen shi Biyu su waɗannan bana ta tasu dan basa gabana amman waɗannan faccalolin nawa guda Biyu sun tsayan araina yadda bakya zato bafa zasu fini da Miji ba sannan suzo su fini da ƴaƴa Ina sam Ita waccan suruki ita waccan ƴaƴa musamman ma Ɗanta mai son ta mai kashe mata Kuɗi wallahi sai ma kin shiga gidan shi daga yau ki ɗau ɗammarar kota kwana”
Anty ta faɗa har idanunta na sauya kala zuwa ja.
Ameerah tabi ta da kallo sam bata fahimci me take Nufi ba akan waɗancan maganganun nata.
“Kuma sannan ba waccan matsiyaciyar ta dawo ba ki dinga janyon ita wallahi bazan ɗauka ba Ki tattara ki watsar da ita ke Budurwa ce ita bazzawara sabida haka hanyar Jirgi daban ta mota daban wallahi bana ƙaunar Amatullah ko kaɗan a duniya”
Ameerah tai saurin tashi daga wajan tayi ɗaki dan aduniya Ameerah bata son taji Anty na zagin Amatullah sabida ƙaunar da take mata Shaƙuwace tun ta yarinta zama suke na so da ƙaunar Juna ada Ko bacci baya rabasu duk da iyayen nasu mata basa shiri haka koda Amatullah tai aure Ameerah bata haura kwana biyu bata je ta ganta ba wannan shaƙuwa tasu har tai yawa basa Ɓoyewa Junansu sirrin Juna musamman ma Ameera data fi Amatullah yawan magana.