Auren Sadaka Hausa Novel Complete
Saadatu shi ne asalin sunana amma ba a kirana da shi haka sai ɗai aikun mutane ne suke kirana da hakan amma yawanci anfi kirana da Sa’ade saboda ɓata suna irin na mutanen gari ma sai aka daina kirana da Sa’aden ake cemin Ade kawai haruffan ƙarshen sunan kenan don haka duk ragowar sunayen Sa’adatun da Sa’adah da Sa’aden da Sa’a duk sai suka ɓata aka koma Ade kawai saidai kawai wanda na tsira a gunsu Mamana da ƴan uwana sune suke faɗamin sunana mai daɗi amma even haka bazasu faɗi ba tun ina faɗa da fishi bare da nake mai zafi har na gaji na sallama musu,
Ƴan asalin garin Kano ne mu ta dabo timbin giwa ko da mai kazo an fika tsakiyar Birni cikin Unguwar Ƙofar Na’isa Mahaifina kenan shi ne haifafffen nan Mahaifiyata kuma ƴar asalin jihar kaduna ce cikin garin zaria kenan a nan ya Aurota ya kawota kano cikin ahinsa.
Gidanmu Babban Gida ne Family house da kakarmu wadda ta haifi mahaifinmu da yayyen mahaifinmu da ƙannensa su da matansu facaloli duk haka ake cakuɗe a gidan ana zaune kowa da sasanta amma kasancewar gidan kamar na gado tun da cancan tun mahaifinsu yana da rai ya bar musu gidan ya ce kowa yayi Aure ya sa matarsa a ciki bai yadda wani ya fita waje ya zama bare ba bayan babu ransa duk wanda ya fita to bai yafe ba, shi ne suka gyara gidan akai masa gyare gyare sosai kasan cewarsa Baban nasu mutum ne mai arziƙi na gaske tun a zamanin da yana zuwa fatauci gari gari ya tara arziƙi da dukiya mai yawa ya mutu ya bar musu Gado Da suka girma kuma sai arziƙinsu ya daɗa faɗaɗa don kaf cikinsu babu wanda bai bawa miliyoyi baya ba, kowa yayi Aure da matansu da ƴaƴansu
Mahaifinmu Shi ne ƙaramin cikinsu Baba Abdulhadi shine Babbansu ana kiransa da Alhaji Hadi, Sai na biyun Baba Musa ana cemasa Alhaji Kalla sai na ukunsu Alaji Isuhu, muna kiransa da Baba Isuhu sai na Huɗunsu Baba Maigida ni ban ma san sunansa na Gaskiya ba don haka na taso naji ana cemasa sai ɗan Autansu Abbanmu Salahu shi kansa baya son sunan Har yana faɗama Kaka mahaifiyarsa ta ce to in bayaso yana iya zuwa ya sayo sabon rago ya yanka amma ita bazaya zo ya dameta ba saboda ya sha faɗa mata haka ya kance Kaka bazan canza ba amma zan daina amfani da shi ba don da yawa ma bazasu sanshi ba Ya koma Alajin kawai sakamakon sauran ƴan uwansa da sai an haɗa da sunayensu Alhaji wane to har yai Aure mu ƴaƴansa muke cemasa Abba don haka ma ko a makaranta sunan muke amfani dashi kamar ni Sa’adah Abba, don kowa da haka yasan ni indai ƴan makarantarmu ne to Sa’adah Abba mutan gari Kuma Ade.
Ƴaƴan Mamanmu mu huɗu ne maza uku nice Auta ta huɗu Yaya Auwalu shi ne na farko sai na biyu Yaya Sani sai na ukunsu Yaya Salisu sai ni Auta Ade dukansu sun gama karatu suna taɓa kasuwanci kafin Allah yasa aikin ya zo ni kuma ina University yanzu Level one hundred ban daɗe da shiga ba,
Wan Abbanmu na farko Baba Hadi shima ƴaƴa huɗu gareshi duk maza kusan saanin su Yaya Auwal ne saboda bai samu haihuwa da wuri ba Yaya Mahmoud sai na biyunsu Yaya Amin sai na Uku Yaya Umar da Yaya Walid,
Sai Baba kalla shima duk maza Yaya ishaq, Yaya Abdul hadi me sunan Baba Hadi ana cemasa Abdul, sai Yaya zakariyya,sai karaminsu mai sunan Abbanmu salahu Ana cemasa Yaya Deen,
Sai Baba isuhu da Baba mai gida suma maza kowa biyu su Allah bai basu haihuwa da wuri ba yayan Baba mai gida Yaya Junaid da Yaya Ubaid, Sai Baba Isuhu Yaya Safullahi da Yaya Abbas,
Wadannan sune rankatakaf yan uwana na gidan sai uban yawa kusan mu ashirin da biyar a gida daya bataliya guda kenan gashi duk maza, kaf yayan gidan maza ne dukkansu ni kadaice mace a yaran gidan, shiyasa na taso rayuwata kamar irin ta maza a tsaye nake babu alamun raini sam a tattare dani Babu wanda zai ganni ya kawo min raini don ni mace ce mai kama da maza Mamana tayi tayi ta gyarani na daina Halina amma ina na kasa to dakinmu maza duk yan gidanmu maza a cikinsu na taso tun ina yarinya cin abinci dasu zuwa makaranta dasu wasa dasu komai na, Mamata babu irin fadan da ban sha ba a wajenta ta ce Babu kyau wasa da maza Sa’ada duk wanda yake wasa da maza Allah zai konashi a wuta amma cikin ikon Allah ina fita wasa maganarnan zata zirare ta bayan kunnena,
Dambe kam babu irin wadda ban iya ba tamkar yar rustling da harbi da kafa da naushi ga iya hawa bishiya tamkar yar biri to da na girma ne ma na dan samu na rage da rokon Allah da Adduar Mama don lokacin na fara zama yan mata amma dai ina nan yadda nake,
Da na shiga secondary school banada kawaye mata sam sai Abokai maza kala kala daga wannan sai wannan bana tsoron malamai balle kuma ajega prepet in tamun cin ubanta nake babu abinda ya shafeni akai karata wajen malamai iyakaci nai kneldown ko tsallen kwado wannan ko ba sabona bane bana tsoron ta mutu Ballantana tai rai na fita sanda nakeso nashiga class sanda nakeso Babu mai sani balle ya hanani raina fes, school bus ma hanani shiga akai saboda masifata ake aiko driver daga gida ya tafi dani
Bayan na dawo a makarantar Boko nai wanka a gurguje naci abinci nai sallah nashiga dakina nai wanka nasa JC kayan Ball dina nadau school bag katuwa na saba nasa cambers dina a ciki da Pcap na zura katon hijab na har kasa ruwan madara na zura slifas na fice falo,
Kamar yadda na zata Mama ita kadai na tarar a falo tana kallo nai mata sallama na ce ” Mama na tafi makaranta” ta ce “to yar Albarka yau da wuri hakam”? Na ce “Eh Mama zan bada hadda ne inaso kafin ya sayyadi yazo naje nayi murajia”, ta ce “To Allah yayi miki Albarka ya kareminke a duk inda kike ya shiryaki ya baki ilimi mai Amfani”, na Amsa da “Amin Mamata” kamin nasa kaina na wuce,
Ina fita na tarar da Yaya Deen tsaye kan mashin dinsa yana jirana yana ta faman duba Agogo yana doka uban tsaki na karaso zai faramin fada “na dakatar dashi as kaga Yaya Deen dakatamin bakasan da yaya ma na samu na fito ba kasan Mama na nan zaka faramin Bala’i, sanin halina da yayi da naci da mita ya ce “hau hau ni mu tafi ana can an fara muna nan”, na ce “to tsaya na cire wannan shegen hijabin kasandai bazan tafi da shi ba naje ya buga ni da kasa Babu gaira babu dalili”, na cireshi na cukuikuye na danna a jaka nasa slifas din shima a jakar na dauko booth din takalmina da P-cap na sanya na goya school back din badon gashina da ya leko ba da kirjina da cewa zaayi namiji ce sak, na dare kan mashin din ya tayarda shi yai juyi ya zana kwabo da tayar da kura sananna ya fananoshi a dari da sittin sai filin kwallo na Abacha Youths Center
Sun dawo dukansu su ukun Yaya Auwal Yaya Sani Yaya Salis Mama ta fito suna zaune a falo a kasan carpet Mama na kan kujera naje na gaishesu da musu sannu da zuwa aka amsamin ba yabo ba fallasa, na zauna kan kujera suka daka min tsawa harda hada baki wai suna kasa ni ina sama nai maza na sauko ina cuna baki dama sun tsaneni a cewarsu wai halina na banza suka tsana bani dinba,
Mama ta ce “to kun dawo zaku fara, kuyi mata a hankali mana in daya yace ta sauka ma zata sauka ba sai kun mata rubdugu ba”,
Mama ta mun wani mugun Kallo “Sa’adah dama baki daina wannan mugun halin da na hanaki ba?”, Na daga hannu zan fara rantse rantsen nawa ta dakatar dani
“Karki cemin komai munafuka nasanki nasan halinki wato ke babu Allah a ranki ko? Wallahi ki kiyayi kanki, ki kiyayi kanki Sa’adah dan Adam daraja ce dashi wallahi to na dai fadamiki kullum ana miki fada da waazi amma bakya fuskanta bakya ganewa ko? To duniyace zata koyamiki Hankali wallahi”,