Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 70

Sponsored links

Yanda ta faɗa tana tura baki da share hawayenta ba ƙaramin tunzurashi yay ba. Amma sai ya kanne yana ƙara ƙanƙance idanun nasa a kanta da motsa lips ɗinsa kaɗan yana binta da shegen kallon nan nasa. Sai kuma ya ɗan laɓe baki a fisge ya furta, “Sadakina na kalla ai”.

 

Furucin nasa yazo mata a bazata, dakatawa tai daga ƙoƙarin kai kofin shayin bakinta ta dubesa da sauri domin tabbatar da shi ɗinne ya faɗa ko wani aljani. Bayan ita da shi ɗin dai babu wani a ɗakin, sannan kuma ya ƙi ɗauke idanun nasa da ga kanta, sai ma sake narkesu yake da wani salon kallo mai saka tsigar jiki tashi kamar mai jiran cewarta

Wani irin tashi tsigar jikinta ta shigayi da salon kallon nasa, yayinda bugun zuciyarta ke amsa kuwwa cikin ƙirjinsa. Numfashi ta ɗan ja a hankali ta maida idanunta ƙasa, batare da ta sake gigin ɗagowa ba dan haka yafi mata kwanciyar hankali.

 

Ganin bazatace koman da yake buƙatar ji ba ya wani ɗauke kai gefe cikin son basar da shock ɗin da ya fahimci maganarsa ta jefata yana wani lumshe idanunsa. Sai kuma ya buɗe da sake juyowa ya ɗan ɗage gira sama, “Tunda bakin ya mutu mu cigaba da maganarmu ta ɗazun?, dan da gaske ina son muyi aiki tare”.

Ƙin ɗagowa tai yanzun ma ta jin jina masa kai kawai alamar eh. Shiru ya ɗanyi na wani lokaci kamar mai tunanin abinda zai fa ɗa, sai kuma ya nisa da ƙyar ya furta, “Abinda ya faru ki ɗaukesa kamar bai faru ba, tana cikin fushine kawai. Duk abinda kike buƙatar sani da ga gareni na baki da ma”.

 

Yanzu ma kanta ta jinjina masan tana wasa da yatsunta, ta fahimci akan mahaifiyarsa yake magana. Batare da ta dago ba ta ce, “Miyasa ka yarda da ni, bayan na sanar maka duk abinda ke raina game da kasancewa da kai? Har ma na aikata, na kuma amsa na aikata”

 

Ɗan murmushi ya saki kaɗan yana mai bin yatsun kafarta da take wasa da su da kallo, sai kuma ya kauda kan gefe yana ɗan lumshe idanun da buɗewa. Kai daka ga yanayin nasa ka tabbatar bazai iya jure doguwar maganar ba, duk ma a takure yake da yawan surutun. Iffah da ke binsa ta kasan ido da kallo sai ta samu kanta da kasa daina kallonsa, a zuciyarta kam ayyanawa ta ke (murmushi yana masa ƙyau). Kamar ya fahimci mi take ayyanawar kuwa ya tsuke fuskar. Wayar da ya ajiye a gefensa ya ɗauka, yay ɗan rubutu ya ajiye gabanta. Rinannun idanunta ta sauke akan wayar.

_“Ki faɗamin gaskiya ya akai kika san an saka abubuwan can na ɗazun?”._

Shayinta ta cigaba da sha kamar bazatace komai ba. Sai kuma taja ajiyar zuciya, cikin muryar nan tata dake shaƙe ta bashi amsa. “Kamar yanda na sanar maka a mafarki na gani. Iya gaskiyar kenan”.

Bawai bai yarda da ita bane, dan ya fahimci ita tana cikin mutane marasa ɓoye abinda ke ransu koda kuwa laifi ne a kansu. Amma zuciyarsa rawa take da amsar tata kasancewar al’amarin bazai kama hankali ba, musamman ga irinshi da ba wani gama sanin abubuwa irin waɗan nan yay ba da ƙyau. Wayar ya sake ɗauka ya rubuta, “Miye alaƙar wanda kukai aikin farko da wannan?”.

 

Wayar ta ajiye tana ɗan murmushi, “A baɗinin abinda na gani suna da alaƙa, a zahiri kam bani da shaidar tabbatar da hakan dan ni kaina ban yarda mafarki na zai zama gaskiya ba”.

“Ina son na sansu”.

“Bita kawai kake buƙata amma nasan ka sansu”.

Jin yayi shiru ta sake nisawa da ajiye kofin. “Bayan nan mi kake son sani?”. Kansa ya jinjina mata alamar babu. Ta ƙara faɗin, “Ni zan iya tambaya?”. Nan ma kan ya jinjina mata alamar eh.

“Kace baka san duk matan da aka aura maka ba sai ni, a ɗan gajeren labarin da naji kuma ance sai an kawosu sashen nan suke rasa ransu ai, bayan mutuwarsu ka taɓa ganin gawarsu?”.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button