Daudar Gora Book 2 Page 35
“Tuba nake Uwa mai share kukan masu kuka. Nayi kuskure a gafarceni bazan sake ba. Ni mai biyayyace ga umarninki a koda yaushe. Wannan ma saɓanin fahimta aka samu”.
Shiru kamar uwa bazata tanka ba, sai kuma ta hura mummunan hancinta dayin ƙwafa. “Dalilai biyu zasu sa na miki afuwa ta-ƙurya. Baki taɓa saɓama umarninmu ba sai a wannan karon. Na biyu darajar wannan masarautar da kike ci. Kije ki kalmashe bakin zaren aikinmu na ƙarshe, dan aikinki na gab da buɗewa. Ki kuma kiyayi kaima yarinyar nan hari kai tsaye, dan duk yanda kike tunanin zaki iya a kanta ta waɗan nan hanyoyin al’amarinta ya fi ƙarfin nan. A yanzu haka Ajlaan ya fara shinshinar ta. Kuma komai zai iya faruwa, dan muna a gaɓar da zai iya kashe ƙishinsa kanta a yanzun, babu makawa magajin kujerar daular ruman na kusanto duniya kenan…..”
Zabura ta-ƙurya tai jikinta na matuƙar rawa, sai wani irin rawa da lips ɗin ta keyi suma tama gagara furta abinda ke bakinta tsabar shiga tashin hankali. Uwa ta miƙa mata hoto cikin bada umarni. “Itace muke buƙata ta zama uwar Miran mai jiran gado, ki gaggauta, ki gaggauta tabbatar da ita cikin masarautar nan matsayin Zawjata-almilk daga nan zuwa ƙanƙanin lokaci. Inba haka ba kiyi kuka da kanki ta-ƙurya! Kuyi kuka da kanki!! hahaha!! hahahah!! hhhhhh!!!!!”.
Ta ɓace ɓat sautin mummunar dariyarta na amsa kuwwa cikin ɗakin kai kace duk masarautar za’a iya jinta.
“Wannan na sake tabbatar mana da ƙamshin gaskiya akan yarinyar nan Mammah”.
Daneen Ammarah ta faɗa cikin sanyin murya da jimamin abinda ya faru ya haddasa mata. Numfashi mai nauyi Malikat Haseenat ta sauke, kamar bazatace komai ba sai kuma ta dubi ɗiyar tata. “Akwai al’amarin dake tare da yarinyar mai girma da ko iyayenta bana jin sun san da shi tattare da ita ba. Inaji a jikina a dalilinta komai na gab da buɗewa a wannan masarautar”.
Cikin nuna mamaki Daneen Ammarah ta ce, “Babban al’amari kuma Mammah? Kamar wane iri kenan?”.
A karo na farko Malikat Haseenat ta saki murmushi mai ƙayatarwa, batare da tace komai ba ta danna kekenta yay gaba. Da kallo Daneen Ammarah ta bita baki sake, ita kam wani lokacin Mammah na hargitsa mata tunani da sakata a wasiwasi gaskiya…..
“Idan har ya kasance bakai bane kamar yanda ka faɗa to wanene kenan? Dama da gaske kamar yanda muke zargi bayan mu akwai masu harar rayuwar yarinyar nan kenan akwai ɗin?”.
“Ga alamun hakan ka gani. Sai ma nakega su ɗin sun fimu shiri. Sai dai abinda ke ɗauren kai su kuma miye nasu dalilin? Dan na hanga na hango a duk cikin wanda zasu iya aikata hakan burinsu zai kasance irin namu ne amma basu da hujjar yin hakan. Idan a matan mahaifinsa ne miye ribarsu tunda ba wasu ƴaƴane da su ba balle ace suna yaƙi irin namu ne? Anya kuwa ba iyalan Sayeed Khairul-Bashar bane ke son ɗaukar fansa?”.
“Idan kuma zasu ɗauki fansa sai su ɗauka akan wadda ba’ita ta musu laifin ba?. Idan har sune rayuwarsa zasu hara bata matarsa ba. Kuma ai tun farkon shigowarta masarautar nan aka fara wannan wasan. Akwai dai wata a ƙasa daya kama mu sani mu kuma san mai wannan shirin dan dalilinsa mai ƙarfi ne.”
Cikin gamsuwa Miran Jasim ke gyaɗama Miran Arshaan kai fuskarsa ɗauke da murmushi, dan koda basu suka aikata ba abinda ya farun ya musu daɗi har cikin rai yake jin farin ciki da nishaɗi..
Tunda Doctor ta gama dubata ta fice ya cigaba da tsaiwa akan ƙafafunsa lumsassun idanunsa da suka canja kala kaɗan na ɓacin rai ƙyam a kanta. Kallonta yake tamkar wata sabuwar halitta a rayuwarsa. Kallonta yake zuciyarsa na harbawa da sauri-sauri. Kallo yake mata irin na miyasa kika zaɓi shigowa rayuwata a haka?, bayan ba haka na so ki kasance ba. Ƙanƙance idanun ya sakeyi a kanta yana mai datse lips ɗinsa da haƙori har yanajin raɗaɗin hakan a karan kansa. Sannu a hankali ya fara kai kawo a ɗakin hannayensa duk biyu goye da bayansa. Sosai a wannan gaɓar fuskarsa ta nuna matsanancin fushi. Zuciyarsa ta fara kaiwa maƙura akan abubuwan dake faruwa a masarautar, ya fara jin bazai iya cigaba da jurewa akai gaɓar da yake buƙata ba tun farko.