Daudar Gora Book 1 Page 122
Fuskokinsu ɗauke da murmushi duk suka shiga, Iyyani da Ummu a baya. Kaka ya shiga ta gefensa. Sai da ya tabbatar sun hau hanya ya gyara zaman norse mask ɗin fuskarsa da ƙyau, handkherciff ɗin gefensa ya matsar jikin ac kamar zai goge ya danna ac’n motar ya ƙure. A take ya busa tare abinda ke jikin handkherciff ɗin gasu Iyyani da kaka suka shaƙa har suna sakin ajiyar zukata kusan a jere. Kashewa yay da sauri yana faɗin, “Af kajini da karambani zansa Baba mura”.
Nauyin da kawunansu ya fara musu ya hanasu damar magana duk suka dafe kai kusan a tare, kaka ne ke ƙarfin halin cewa wani abu amma ya kasa, su Ummu kam tuni sunyi luuu jikin kujera alamar barci ya bugar da su. Kakan ma yay luuu a tasa kujerar. Nannauyan numfashi saurayin ya sauke da ɗan juyawa ya dubesu ta mirror. Tabbatar da sun suma yanda yake buƙata ya sashi janye Norse mask ɗin fuskasa da sakin murmushi ya latse wayarsa. Ana ɗagawa bai jira komai ba ya furta, “Done! boss”.
“Proud of you”.
Aka bashi amsa a taƙaice da ga can da latse wayar…..
Tajwar Eshaan da bai sake bi takan hadimin ba kam hankalinsa gaba ɗaya ya tattara ne ga computer ɗin gabansa a yanda yake harɗe. Cikin nutsuwa yake sarrafata a take saƙonnin da yake buƙatar gani suka bayyana kansu. Hannu ya kai ya sake daidaita gilashin idanunsa da ɗan yamutsa fuska ganin dogon text message ɗin daya buɗo… Dai-dai nan takunta da ƙyamshin sassanyan turarenta ya fara rige-rigen isowa hancinsa tun kafin bayyanarta. Wani irin harbawa daya tilastashi ɗaga ƙwayoyin idanunsa kaɗan ta cikin gilashin yay sai ko suka sauka akanta. Sanye take cikin shirinta da baza’a kirasa mai matuƙar ƙawa ba, ba kuma mai ƙasƙantarwa ba. Babu ko ɗigon kwalliya a fuskarta, ƙamshin turarenta ma a yau ƙasa-ƙasa ake iya jinsa. A zahiri zaka ɗauka yanayin da masarautar ke cikine ya sata kasancewa haka, sai dai a haƙiƙanin gaskiya komai a sukurkurce yake gareta. Duk wanda ya san alwashinta akan Tajwar Eshaan zai kalla wannan lokaci ne matsayin na farinciki a gareta domin ta kusanto hanyar cikar nasararta, sai dai zuciyarta danƙare take da wani irin ruɗani da ƙunci. Amma ta kasa dakatar da kanta, komai yana sarrafa kansa tare da ita ne tamkar wadda ake sarrafawa da na’urar remote. Yanda ta ɗanyi turus kamar wadda ta firgita da ganinsa ne ya sashi maida idanun nasa ƙasa cike da basarwa ga screen ɗin computer ɗin kai kace baima san da ko motsinta ba a wajen.
Da ƙyar Iffah ta iya jan numfashi, yayinda bugun da zuciyarta ke faman yi tsananinsa ya ƙara hauhawa. Sai dai mi, bata iya jin zata dakata duk da wani irin rauni da kasala dake cigaba da mamayeta. Tamkar wata hawainiya haka ta cigaba da takowa da sanɗa har inda yake, ta ɗan rissino ta gabansa ta dire tambulan ɗin hannunta a tebirin gaban nasa batare da tayi magana ba.
Amintaccen hadimin nasa da al’amarin ya zame masa kamar wani sabon abu, yay saurin dawowa hayyacinsa cikin rawar harshe ya fara miƙa gaisuwa gareta. Hannu kawai ta iya ɗaga masa a kasalance dai-dai tana kaiwa a kujerar dake gefen Tajwar Eshaan zaune. Dole ya miƙe da sauri ya fice a falon, dan cigaba da zamansa haramunne. Iffah dake jin kamar ta fasa kuka a dai-dai wannan gaɓar ta ɗaga idanunta da girmansu a yau gaba ɗaya ya shanye da ƙyar ta saukesu akan Shahan-shan da yay tamkar bai san da wani mahaluki mai numfashi a falon ba bayan shi.
“Bar… ka da sa.. fi… ya”.
Ta faɗa a rarrabe tamkar mai koyon magana. Da gaske yau ƴan izzar ne a kasan, dan haka bai nuna alamar yaji ba, dan bai ko motsa ba balle ɗauke ido akan abinda ke gabansa har kusan tsahon mintuna biyu kafin ya ɗaga mata hannu da ƙyar ya cigaba da abinda ke gabansa. A ƙalla da a ainahin Iffahr ta take salon nasa zai soke ta, bakuma zata iya haƙuri ba sai ta maida murtani. Amma abin mamaki sai ta miƙe jiki a saɓule ta nufi daning babu jimawa ta dawo da glass cup. Da kallon ƙasan ido ya bita zuciyarsa da jijiyoyin jikinsa na wani irin tsitstsinkewa tamkar suna masa ishara da abinda ke tinkarosa. A karo na farko takai durƙushe gabansa, tare da buɗe tambulan ɗin data shigo da shi mai ɗauke da tatacciyar madara dake gauraye da dafin macizai daban-daban har kala biyar. Jikinta rawa yake, har shi kansa sai da ya lura da hakan ta kallon gefen ido da yake mata. Madarar da bata wuce rabin kofi ba ta miƙa masa tana mai rumtse idanunta wasu hawaye da ƙarfinsu ya zame mata nauyi a ƙirji na gangarowa da gudun tsiya bisa ƙyakykyawar fuskarta.