Daudar Gora Book 1 Page 111
Murmushi ya sake saki tare da mikewa ya kai jakar gabansu, cike da farin ciki suka buɗe suna mai fiddo duk takardun ciki. Bayan sun ɗan dudduba su suka ɗago fuskoki cike da murmushi suna yabama Barrister namijin ƙoƙarin sa. Shi dai nashi murmushi ne kawai. Ɗaya daga cikin baƙin da ake kira da Sayeed Harun Al-rashid, babban mutum ne a ƙasar ta ruman, dan riƙƙaƙen ɗan kasuwa ne na gwal da kowa ya sani kasancewar sunansa yayi matuƙar shura a wannan harkar data zama babban tattalin arzikin su na ƙasar, dan Ruman kam bata san iya arziƙin gwal da ALLAH yay mata ba, shiyyasa duk wani riƙƙaƙen ɗan kasuwa zaka samu gwal ɗin ne mafi rinjayen makaminsa kamar dai Sayeed Harun Al-rashid. Ta wani gefen kuma yana riƙe da sarauta sai dai yafi bama kasuwancin muhimmanci matuƙa. Zamansa ya gyara sosai yana fuskantar Barrister. “Barrister yanzu mi kake son ka sani?”.
“Ranka ya daɗe ba komai bane dama sai akan waɗan da naga case ɗin ya karkata. Na duba dukkan bayanan Barrister Abdallah Aas, sai dai a yanda na fahimta kamar ya gano inda su mutanen dake hannun naku suke, dan kafin ma ya rasa ransa kamar ya fito da ga ƙauyen Lufana ne wajen matar marigayin, abinda nake son cewa anan ina tsoron yazam bayan Barrister ɗin akwai wanda yasan wannan sirrin. In kuwa hakan ta kasance zaman mutanen a station ɗin dana fahimci kun ɓoyesu zai zama barazana ke nan koda anan gaba”.
Kusan a tare sukai murmushi, Sayeed Harun Al-rashid ya muskuta zamansa cikin nuna damuwa da zancen Barrister. “Maganar ka nakan hanya Barrister shiyyasa tun kafin yau muka gama maganin duk abinda kake gudun. Tun daga farkon wannan case ɗin idanunmu akan komai suke, dan haka ka kwantar da hankalinka. Su kuma tuni basa a police station ɗin, dama mun kai ajiyar su ne domin ɓadda kama bayan kwanaki kuma muka ɗauke su, amma kai a yanzu mi kake son cewa?”.
Anzo dai-dai gaɓar da Barrister keson azo, dan haka ya ɗan murmusa yana mai ƙara bama kansa nutsuwa. “Alhmdullh kun fahimci inda nake buƙatar akai ranka ya daɗe. Abinda nake son cewa kai tsaye shine ayi duk yanda za’ai cikin kwanaki biyun nan abar ƙasar ruman da mutanen gaba ɗaya”.
“Eh maganarka abin dubawa ce kam, amma kuma mizai hana kawai a ɓaddasu a wuce wajen, dan abinda ya zama dalilin zuwansu hanunmun ma an sameshi cikin sauƙi yanzu haka”.
Barrister yay ɗan jimm dan bai fahimta ba, amma sai ya dake bai sake musu wata tambaya ba gudun karsu zargi wani abu. Sai dai ya cigaba da faɗin, “Ɓaddasu bashine mafitaba ranka ya daɗe, dan a ɗan bincike da nayifa akwai babbar matsala game da mutuwar Barrister Aas”.
Babu wanda zancen bai daka ba a acikinsu, Sayeed Faizul-Anwar daya kafe Barrister da ido yay saurin faɗin, “Barrister bamu fahimce ka ba, mi kake son cewa?”
“Ranka ya daɗe yanzu zan fahimtar da ku. Idan har kun saurari dukkan labaran dake yawo har yanzu babu wani tabbaci na samun alamar sassan mutum a cikin motar Abdallah, wannan shine yaja hankalina tun a ranar farko bayan nabar nan na fara nazari da bincike. Tabbas Abdallah na raye, sai dai ya ɓoye kansa domin bada ƙafa. Na sanshi nasan mizai iya fiye da tunaninku. Shiyyasa nake ganin kashe mutanen a yanzu bashine mafita ba, muyi nesa da su da ƙasar nan ta yanda babu inda zasuji ɗuriyarmu, sai kuma mu samo wasu a madadinsu a buɗe shari’ar ta yanda zamu ƙona Barrister Abdallah Aas da ransa batare daya farga ba”.
Dukansu gumi suke na tashin hanakali, sai dai babu wanda ya iya cewa komai har zuwa wani tsahon lokaci. Sayeed Harun Al-rashid ya nisa yana mai share ɗan gumin daya taru masa a goshi. Ƙyaƙyƙyawar fuskarsa fara tas gaba ɗaya ta ƙwaɓe alamar rashin damuwa. “Zartar da hukunci bazai yuwu yanzu ba Barrister, amma kaje zuwa anjima zakaji komai ta waya”.
“Babu damuwa ranka ya daɗe”. Barrister ya faɗa cikin jimami shima, sai dai acan ƙasan ransa dariya yakeyi, yayinda wani gefe na zuciyarsa ke tabbatar masa akwai wani babba mai alaƙa da case ɗin bayan su, shiyyasa bazasu iya zartar da hukuncin ba kai tsaye. Yau ma dai an rakosa da kuɗi masu yawa har mota…….