Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 55

Sponsored links

Har mom da dad suka karaso unguwar su mami  dad be dena fada ba, har wani ji yake kamar yayi tsuntsuwa ya gansa a cikin gidan, tsabar yanda ransa ke a bace shi yake driving da kansa ko driver be tawo dashi ba bare securities, yana shirin horn bayan sun karaso gidan suka ga gate din gidan a bude, lokacin an budewa mami data dawo daga office gate, danna kai dad yayi ya shiga shima, securities basu hanashi ba dan sunyi tinanin tare suke da mami………

Lokacin da dad yayi parking mami harta shige ciki, da sauri yabi bayanta saboda hangota dayayi tashiga main parlor dinta………

“Fatima! Fatima!”…..

Mami da har ta fara hawa sama ta juyo muryar dad a cikin parlornta……

Juyowa tayi da sauri cikin mamaki tace;

“Ya zaka shigomin parlor kai tsaye haka? Who even permitted you to come in?!”……

Cikin hargowa yace;

“Har sai anbani wani permission a wannan tsinannan gidan zan shigo? Toh open your senseless brain and listen to me; zan daurawa Deen aure da Hamida in few weeks time saboda haka ki janye maganar koma wacece kikeyi, sannan ki fita daga sabgar yaro na dan ban gane kanekanen da kikayi a rayuwarsa ba ko wayata ya dane dauka saboda makircinki”………

Katseshi mami tayi tana nunashi da yatsa tace;

“Dakata mallam!! Kai har ka isa ka tako har gidana kana gayamin maganar banza? Toh bari kaje sai yadda nayi da Saifuddeen yanzu kuma babu yanda ka iya, zancen daga wayarka kuma ban basa dama bane shiyasa, da’na kuma baze auri yar munafukar matarka samira ba!”…..

“Yi mana shiru karamar yar iska kawai! Ke har kin isa yaya tana fada kina fada dan baki da mutunci bakida kunya butulu! Kai kuma Abubakar ka bani mamaki! Yanzu har zaka iya kwaso jahilar matarka kuzo kuciwa yaya mutunci har gida? Toh wallahi bazamu yarda ba this is against the law! Ku saurari sammaci mahaukata guda biyu kawai!!”……

 

Umm da fitowarta kenan ta katseta cikin bacin rai, bacci take taji hayaniya na tashi tana kuma jin maganganun da suke fada sama sama, sakkowa tayi ba shiri shine taci karo da maganar da samira take gayawa mami, ba karamin baci ranta yayi ba abinka da wanda be iya fushi……….

 

Sosai jikin dad yayi sanyi dan tinda suke samun sabani da mami Umm bata taba sa baki ba, har haduwa sun tabayi da ita suka gaisa cikin mutunci kamar babu komai tsakaninsa da yayarta, sannan ko lokacin da aurensu ya mutu tayi making effort sosai gurin sasantasu suka nuna mata bazasu sasantu shine ta hakura ta zuba musu ido, sai gashi yau Umm ta kalli tsabar idansa tana gayamasa maganganu, harda ce musa mahaukata shida matarsa……… Amma be karaya ba dan ya riga yayi nisa baya jin kira, yana shirin bawa Umm amsa daidai da ita kenan aka banko kofar parlourn…..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button