Sanadin Zane 19-20
Bismillahir Rahmanir Rahim
Lalube kawai takeyi cikin duhu Dan wayar Bata fiya lafiya ba ,ganin ta gan wayar Bata gan battery ba sai abin ya Kara Bata haushi abinka da kurma da mugun zuciya ji tayi numfashinta yayi Sama
D’agowa tayi da niyyar yi me tijara ta saci kallon motar da aka paka tasan masu kudi ne a ranta ta Raya kila sanadin samun sabon wayarta kenan ya yayi Dan tijara zatayi musu har sai sun siya Mata waya
Juyawa tayi Dan ta ta tada musu hankali aiko kamewa tayi dan idanunta sauka yayi a kansa aiko fidda idanu tayi zuciyarta na mugun bugu
Kawu ya karaso Yana cewa bawan Allah kawo ruwa kardai yayi mutuwar sojoji a tsaye subhannah bazanyi mamaki in Marin ya gigitashi kasan da zuciya take Kai duka fah
Abbas ko kasa motsawa yayi kamar wani soko saboda lamarin ya mugun gigitashi ko kad’an be ma kalli kurma da nadama ya mamayeta ba
Kawu ya kalleta yace”ikon Allah kowa da yanayin da ya shiga
Keee lafiyarki
Duk tunanin da zatayi Taki samun mafita sai yanzu ta gane dalilin kamewarsa ta dinga salati a zuciyarta dan tasan
Ba karamin mutum ta kaiwa bugu ba
Kawu ko Yana ganin irin motar dake pake tunaninsa ya canza burinsa Kar kurma tayi yaren kurmaci su Gane kurmace
Kallonta ya sakeyi sai ya gan ta rude abin ya mugun bashi mamaki
A hankali tayi ta matsawa kusa da taku d’ad’aya harta Kai kusa da yarima
Ai ji yayi ta zube jikinshi a Dole ta Suma
Kawu rungume hanun yayi Yana kallon ikon Allah Dan yasan ba Suman da tayi tsagwaran iskancine
Fadiwar da tayi jikinsa shi ya dawo dashi hankalinshi ya wani tunkude ta be Kara ko minti daya ba bare ya kalleta yayi mota Abbas na binsa a baya amma sauri yake sosai
Driver side ya shiga har Abbas ya Kama handle din motar sai yaji ya jata a sittin
Tunda Abbas ya gan Haka yasan ran maza ya bace dan tunda yake tare dashi be tab’a ganin yayi driving ba infact zai iya cewa be tab’a driving da kansa ba in Banda a lokacin da ya koya ba at his early age
Jikinsa yayi sanyi Dole zai bi yarima hakan yasa ya tare napep dan ko ya tsaya ya rasa irin hukuncin da zaiyiwa yariyar
Suna barin wurin kawu yace”keee tashi kafin in wanka Miki mari yariya Ina Miki kallon kurma Ashe dai shegiyar d’ari ce,yariya daga ganin mutum sai ki Fara karuwanci ikon Allah ”
Kurma kin Bude Ido tayi saboda pretending wani shuri kawu yayi Mata ta tashi da wuri ya cigaba da magana Yana cewa”yariya dake kin San ki mannewa namiji ikon Allah, ikon gaske
Ummi dake kallo a dan karamin akwatin tv ta ta fito
Yace”kina ganin yariyar Nan ko na so ki gan karuwancin da ta zuba data gan wani gaye wallahi sai kin Sha mamaki abin ya kazanta Wai fa fad’awa namiji tayi a jiki,toh aurar da ita zanyi in huta wallahi kafin labari ya Sha bambam in Shiga uku
Hafsat dake kwance kofar d’akinta tace”ka fasa aurar son me kudinne”
Yace”ai Sha kuruminki Kamar kinyi bako ya mutu na gan wani had’ad’e yanzu Nan shi Zan bawa Dan na gan alamu da canji hanunsa
Hafsat tace”Wai kabiru meyasa kake b’atawa yariyar Nan lokaci ne tana da masu santa ga wanan yaron isah gwargwado Yana da rufin asiri Amma kaki bashi Daman aurenta wani me kudi ne zai aureta a Haka ko mance kake kurmace ”
Yace”kurmanci ya Hana ta Zama macene wanan da kike gani sai tafi me magana kawo wuta
Hafsat tace”Allah ya kyauta muna Nan ai ”
Yace”Kuma zaku ji alkhairi ai da yarda rabbi izzati ”
Hafsat Bata Kara cewa komai ba ummi ta koma d’aki abinta dan lamarin kabiru da kurma na caza mata kai
Yace”ya wuci mu b’oye Masa larurarta mu ninke shi baibai”
Hamma da kurma takeyi yasa shi cewa je kiyi wanka kiyi sallah ki kwanta
Bata jishi ba tayi d’akin ummi shima ya Shiga yayi wanka
________
Abinda ya faru ya shiga jikin yarima sosai Dan Yana shiga d’akinsa a masaukinsa jikinsa ya Fara rawa wanan ai insult ne wa royalty dinshi baya Jin ma an taba dukansa
Gaban madubi yaje ya tsaya Yana kallon kumatunta who is she…ita din wacece a garin Nan Yar wacece Kuma miye ya Bata gut din Kai Masa Mari
Sosai jikinsa ke rawa idanunsa ya canza kala sai yanzu yake mamakin tahowa
Watsi yayi da kayan saman mirrow din ya kaiwa madubin naushi ji kake tasss ta tarwatse aiko ta yanke hanunsa
Yayi zaman dirshen a kusa da gado ya hade Kai da kunya har yanzu karkawa yakeyi danshi mutum ne me pride da eagle
Abbas ne ya turo kofa a hankali cike da tsoro ya karasa inda take zaune dan ko motsawa beyi ba ga jini na bin hanunsa ya saki salati tare da zuwa ya karasa ya duka cike da girmamawa ya Kama hanun
Fisgewa yayi ya kalli idon nan Kamar garwashi yace”wacece ita ”
A firgice Abbas yayi baya yace”what gave her the gut the audacity to lay her filthy hand a kumatuna
Cike da rashin Hankali jinin dake zuba a hanunsa Abbas yace”ranka dade ka Bari muyi dressing din ciwon Dole nema a hukuntata
Shako Abbas yayi yace”ta Yaya za a hukuntata bàyan a kasar su muke bazaiyi yiwu ba Dan zasu iya kaimu Kara
Abbas yace”Dan Allah yallabai ka Bari in Kira ayi dressing ciwon
Kallon jini yayi kamar mahaukaci ya kaiwa center table din naushi da hanun dake jini Saida ta tarwatse shi kanshi ya ji wani zafi ya ratsa kwakwalwarsa ya saki Dan kara
Abbas ya Kuma kai hanun zai kamo hanun ya d’aga me hanun
Kamar wani me bori Haka ya dawo ya saki murmushi kamar ba me natsuwar yarima ba
Shako Abbas yayi yace”Ina son a wulakantata,wulakanci mafi Muni I hate Nigerians I hate them,they are all the same ko kasan kurma data kashe mahaifiyana Nigerian ce a hate them,Abbas ka wulakanta min ita Kai Ina son in huce haushin abinda kurma tayi min a Kan wanan shashasha ka koyar da ita tarbiyya
Kada Kai kawai yake kamar sabon kamu shima Dan be tab’a ganinsa a Haka ba
Zaiyi magana yarima ya katseshi da cewa get ou……..”
Abbas ya katse me hanzari zaiyi magana ya daka me tsawa yace”I said out of my room”