Rabi Danja Hausa Novel Page 4
Rabi tana isa wajen ta taras Mijinsu Rabi Malam Tukur ya zo wajen sai masifa yakewa Biba sai zaginta yake, ita ma tana ramawa Tsohuwar nan da take uwar mijin su Biba sai cewa take “ka sake su ni dama wannan ƙaddararen auren ba sonsa nake ba, duk sun uzzira maka faɗan yau daban na gobe daban dan ɗiban Albarka, to Kwarankwatsa na gaji kasan yadda zakai da waɗannan mutanen da basu san komai ba sai tozarta ka a bainar jama’a”, Tukur kam da gani bazai iya sakin nan ba, cewa ya ke “Muje gida tukun Inna muje kome za’ai ayi a can, gida suka nufa Rabi dake tsaye taso taga ƙarshen chakwakiyar hakan bata faru ba, hanyar gida tayi abinta tana waƙe-waƙen ta abinta, a hanya kuwa ta daki Yaran mutane da yawa, idan sukai mata Allah ya isa sai ta ce “da bai isa ba da baiyi wance da wane ba”, sai ta ambaci sunan Iyayensu a haka ta isa gida ana ta ƙiran sallar Magriba.
Baraka tana zuwa gida a firgice Yaranta dake tsakar gida suna ta faɗin Baba Baraka sannu da zuwa ko kallon su batai ba, ta shige ɗaki ta cire kayan jiƙaƙƙu ta saka wasu yamutsatstsu ko tunanin wanka babu, ta yarɓa wanda ta dawo dasu a jikin ƙofar ɗakinta, ta haye gadonta da yake a hargitse ta kwanta ta rufe jikinta ta rintse ido, tsoro ne fal a ranta tana ta fargabar kar Yarinyar tazo mata, sai faɗi take “Allah yaso idona a rufe yake banga halittarta ba,Allah na gode maka”, Yaranta duk wanda ya shigo saita firgita.
Tana shiga gida ta rafka sallama, Inna da take ƙokarin yin Alwallar sallar magriba ta kalle ta ta ce “ina kika je Rabi?”, “Innata kinsan me?, banje ni gidan su Kattumen ba saina tafi Unguwar gini naga mutane da yawa……”, labari ta bata amma bata gaya mata abinda ta aikata ba, Inna da take Alwalla ta nunawa Rabi buta kana ta ƙarasa Alwalar ta tashi tana faɗin “Allah ne kaɗai yasan yau abinda kikai Rabi daga Allahn daya halicceki sai ke, Ubangiji ya shirya min ke akan tafarkin Allah madai-dai ci Rabi”, da Ameen Rabi ta amsa tayi cikakkaiyar Alwalar ta ta ɗakko hijabi tayi sallar ta , saida ta gama ta ɗakko abincinta kalan taci dan bata son cin abinci da yawa, ta shiga bawa Inna labarin kishiyoyi da yaƙi ƙarewa a bakinta, ita dai jinta kawai take, suna a haka Baba ya dawo, Murmushi ya yi ya ce “yau dai kam lafiya komai yake naga alamu, ya faɗa yana zama a mazauninsa da indai ya dawo nan Inna take saka masa Tabarmarsa da daddumarsa, dariya Inna tayi ta ce “aikuwa dai sai sam barka, sai dai an fita rangadi”, duk abinda suke da Rabi suke sai dai ba zata gane ba dalilin ƙarancin shekaruntaa, sannu da zuwa tayi masa ya amsa da walwalarsa tare da sa mata Albarka da Adduar shiriya da kullum basa dena mata