Hausa Novels and Stories

Maraici Ne Ja Min Complete Hausa Novel 2

Sponsored links

A lokacin rahama tana zaune tana kallon wani program da ake mai matuk’ar muhimmanci da Jan hankali ga mata, tare da *AUNTIE FAUZIYYAH D SULAIMAN*, k’amshin turaren ta shiya ankarar da rahama zuwanta, ta d’ago tana kallonta har ta k’araso kusa da ita ta zauna a shagwob’e tana gaisheta, “auntie rahama Ina kwana”.

Zuba mata ido tayi ba tare data amsa ba har ta sake maimaita gaisuwarta.

“Aysha! Wai me yasa kullum abubuwan ki k’ara yin gaba suke? Saboda kinga nasa miki ido ko? Toh wallahi kuwa kwanan nan zamu sa k’afar wando d’aya dake, bar ganin Ina zuba miki ido ehe”.

A marairaice wannan karon ma tace, “kiyi hak’uri auntie rahama insha Allah zan kiyaye”.

“Yafi miki dai”. Shiru duk sukayi kafun rahama ta kalleta tace, “ga breakfast d’inki can a dinning”.

Bata amsa taba, hakan yasa yayar ta d’an kira sunanta da k’arfi, “Aysha!”, sai tayi firgigit tana kallonta, “zaki fara wad’an nan tunane tunanen banzan naki saboda na miki fad’a yau ko?”.

“A’a auntie, kawai dai so nake idan ba zaki damu ba ki daina sa baki akan duk abinda zaki gani tsakanina da Yaya mukhtar…”.

Cikin rashin fahimtar inda maganganunta suka tafi rahaman tace, “owkay na zuba miki ido kina rashin mutumci da da’a ga mutumin daya miki komai a rayuwa? Yayi dawainiya dake tun baki san kanki ba, yake ci gaba dayi har a yanzu ma?”.

“Ba haka nake nufi ba auntie, tabbas Abban Hanan yayi mun abinda bazan tab’a iya mantawa dashi ba, ya d’auki nauyin cina, shana, sutturata da d’awainiyar karatuna gaba d’aya, sannan dai dai da rana d’aya bai tab’a gazawa dani ba, Ina sane da abinda yayi mun matsayina na wadda ta taso cikin maraici da talauci, sai dai hakan ba yana nufin shi d’in bashi da kuskure ta wani fannin ba, ko ni bazan misbehaving a wasu abubuwan ba, a wannan gab’ar sai dai ince kiyi hak’uri auntie rahama, amma ki d’auki duk abinda nake ma mijin ki matsayin ajizanci irin na d’an Adam….. Ina fatan kuma don Allah zamu rufe babin wannan maganar gaba d’aya”.

Tunda ta fara magana rahama ta tsura mata ido tana kallonta, wani lokacin in Aysha tayi wani abun takan rasa gane Inda tasa gaba, ta kasa fahimtar abinda ke faruwa tsakaninta da mukhtar sam,,,,, sai dai fa ita no matter what ba zata yarda mutumcin mijinta ya zube a fuskar k’aramar yarinya kamar taba.

Basu sake ce da juna komai ba Aysha ta d’auki remote ta sauya zuwa wata channel da ake haska Indian series masu kyau, taso missing kuwa don an fara nisa a haska maimaicin firm d’in, tun asali shine abinda ya futo da ita da zumud’in ta sai kuma auntie rahama ta nemi b’ata mata rai a banza da maganar mijinta da a duniya bata iya ganin laifin shi.

*****Mukhtar yana zaune a office amma abun duniya ya mishi zafi da yawa, ya kasa fahimtar kanshi gaba d’aya cikin shekara d’aya zuwa biyun da suka gabata, akan Aysha yakan rasa gaba d’aya control, ya riga ya saba da rayuwa tare da ita, yadda take kula dashi ada ko rahama bata iyawa, zai iya cewa rahama tana auren shine amma yadda Aysha tasan komai nashi rahama bata sani ba, gashi yanzu gaba d’aya ta sauya mishi a lokacin da alak’ar su ta fara d’aukar zafi, maybe ko saboda tana tuna matsayinta gare shi da kuma rahama matarshi ne? Allah masani.

Da yamma ta sake yin kwalliyarta cikin wata rigar ba irin ta d’azu ba, tayi rolling madaidaicin gyale saman kanta, fuskarta d’auke da light make-up ta futo tana fudda sirrin k’amshi. Kitchen tayi don can take jiyo tashin k’amshin daddad’an girkin da rahama takeyi, tana shiga ta fad’ad’a fara’ar fuskarta tace, “mie auntie sannu da aiki?”.

Rahama tana kallonta tace, “ke za’a yiwa sannu Aysha irin wannan bacci haka wuni guda, da gaske dai hutun makarantar akeyi shiyasa ko d’an girkin da ake tayani shiryawa mukhtar an daina”.

A zuciyarta tace, “aikuwa in dai don mijin ki yaci yaji dad’i ne na daina wahalar da kaina a kitchen ina shiryawa k’aton banza abinci yana ci yana sude hannu”. (Nikam nace toh fah🤔) a zahiri kam cewa tayi, “ki bari hutuna ya k’are na koma school sai aci gaba da fafatawa”. Rahama tace, “toh Allah yasa”.

“Yauwa auntie zan futa Yaya Fu’ad yana jirana a waje”.

Rahama tace, “ayyah toh sai kin dawo, amma don Allah kiyi k’ok’ari ki sallame shi kafun Abban Hanan ya dawo kinsan baya so”.

“Hum kada Allah ma yasa yaso shiya sani matsalar shice ni kam ba abinda ya shafe ni, haka kurum duk friends d’ina suna aure shi yana son dak’ile ni saboda wani dalili nashi daban na banza, da anyi magana yace karatu karatu, karatun da in naso a yau zan iya zab’ar aure na barshi”…… Duka wad’annan maganganu Aysha tana yinsu ne a cikin zuciyarta.

Ganin ta tafi tunani sai rahama ta tab’o ta, “Aysha are you okay?”.

Da sauri tace, “I will take care insha Allah, saina dawo”. Ta k’arasa fad’a tana futa da sauri ba tare da ta sake jiran abinda rahaman zata ce ba,

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button