Idon Naira 35
Shiru tayi zuciyarta na shiga tunanin lamarin
Shiyasa umman tazo kenan dai akwai rigimar da akeyi din Wadda tasa suka aminta zasu amsheta
Amma dai kuma a yanzu datakeda ‘ya batajin zamanta gidan haj maryamah din zai yiyu sbd Dalilai da dama,
Haj maryamah bazata taba son Maryamah qarama ba sbd tun asali batason masu aiki dake da qananun yara Bare ita datakeda jinjirar ‘ya,
Tayaya zata iya watsi da yarta tayita aikin bautarda ko yar tasan baa kaunaci ganiba,
Bayan haka Tayaya zata koma kurkukun da Allah yasa ta fito da qyar da ‘yar marainiyar ‘yarta suje itama rayuwarta ta mutu kamar Tata tun kuruciya har tsufa dan kafin Aqeel yadawo ya zama Gatan maryamah din tuni ta rasa abubuwa da dama.
Ganin yanda tayi shiru yasa umma kallonta a shagube tace,
“Ko kinfi karfin zama gidan ne tunda yanzu kema kin zama uwa babu Wanda ya isa dake.
“Da tsufana amma kullum Ina hanyar tafiya mai shegen nisa sbd ke zainab,
Duk zuwana babu na lafiya sbd rikicin halinki ne Dana yar uwarki,
Yanzu Ana fatar yaron nan ya tafi karatun nan angama komai rana tsaka sbd ke yasake cewa bazashiba
Yanzu an samu ya aminta Zaije tunda ya shiryaki da mahaifiyarsa kin tsaya tunanin ta yanda zaki sake hargitsa lissafinsa ya fasa tafiyar ko zainab?????
Mun koma ga wadda ta Haifi ‘dan ga wadda muke rarrashi akansa sbd isa da ikonsa da Allah yabaki..
Jin hakan yasa zainab taqaita fitinar da cewa ta amince zata koma can din karya damu ya wuce karatunsa kawai Allah yabasa saa da nasara.
Batason fitina da tashin hankali da gorinsu umma dan haka ya yanke zancen da hakan dan a samu ya tafi
Suma su umman dan asamu ya wuce din yasa sukace sun shirya da zainab din komai ya wuce duk da kusan umma ce take kidan kuma take rawar
Ita haj maryamah dai taqi saka baki sbd jikinta da zuciyarta dasuka kasa sakewa idan ba ganin tayi Aqeel din ya tafi ba dan kuwa da gaskiarsa magana daya tak yake tsayawa akai ba tafiyar zaiyiba idan ba zainab da ‘yarta yaga yabarsu a cikin kulawaba.
Yaje ganin little MARYAMAH amma basu bashi damar daukantaba saidai yaganta daga cikin kwalban Dan haka yayi mata addua sosai da fatar tsarin Allah gareta yafito.
Zainab duk inda zuciyarta take tayi rauni sosai na rabuwa dashi din amma ta boye ta danne a ranta sbd kaucewa laifi gun umma kokuma hanasa tafiyar…
Addua tayi masa sosai tareda fatan samun dibbin nasara da cigaba a rayuwarsa.
Harya baro asibitin kasa hada ido yayi da maminsa sbd yana iya hango damuwa da tashin hankalinta harma da firgicin tafiyarsa ya barsu itada little amma kuma tunda yasan gida yabarsu to tasa damuwar ta dan ragu yanada nutsuwar tafiya yanzu.
Yana barin asibitin ta zainab ta sauke wani kasalallen numfashi tareda sauke kanta qasa sbd idanuwanta dake kadawa jajir..
Fatan samun nasara da albarkar ubangiji tayi Masa a duk dinta yake sbd Allah ne kawai yasan ranar dawowarsa yasamesu ko wane yanayi Kuma sai yanda Allah yasa.
Zamewa tayi ahankali ta kwanta kan gadon datake tana rufe idanuwanta duk tasan ba baccin zatayiba.
Aqeel kuwa Yana Isa gida breakfast yayi batareda Bata lokaciba yagama aka fiddo da luggages dinsa suka fito hannunsa cikin na mahaifiyarsa dakejin kamar ta goyasa Dan dadi da farin ciki,
Ta matsu taga ya wuce kafin zainab ta bugo tace ‘yarta ta mutu yafasa tafiyar Kuma.
Dashi da uncle dinsa alh Yusuf suka wuce
Har airport haj maryamah din ta rakasa sukabi jirgin Abuja Wanda a Daren ranar jirginsa zai tashi shima daga Abujan.
Tana dawowa wata irin lafiyayyar hamdala tayi tada tabbatarda jirginsu ya daga
At last dai tasamu ‘danta yatafi
Yayi nesa da zainab
Yanzu tasamu damar da zata ringa ziyartarsa shaquwa da kaunar dayakewa zainab duk zai maido kanta ya ragewa zainab din.
Wuni sukai a gidan cikin nutsuwa da farin ciki daga ita har umma.
Saida yamma tafito a shirye Dan zuwa asibiti ganin likitanta dazai sake duba dp din nata.
Umma ma ciwon baya da qafafun datake fama dashi aka dubata akai suka fito zasu nufi mota umman tace suje haj maryamah ta dubo zainab tunda tana asibitin itama.
Da mamaki haj maryamah takalli umman sbd sanin asibitin ta kudine sosai Dan basuda ko irin dogayen dakunan ward haka
Duka dakunansu daddaya ne Amenity rooms dai Kai tsaye.