Hausa Novels and Stories

Idon Naira 1

Sponsored links

_Bismillahir rahmannirRaheem_

_*Uba daya ne ya haifesu, yabasu tarbiya daya,kauna daya,matsayi daya..*_

*_Qaddara ta bambamta rayuwarsa ga bangarora guda Kashi biyu Wato haske da duhu,_*

_*haske da duhu shine qaddarar data zama tazara a rayuwarsu har suke tsananin qyamatar junansu,*_

*_qaddararsu ta gangaro har kan ‘yayansu Wanda suke tamkar black and white maana baqi da fari suma gurin bambamci fiyema da iyayen nasu,_*

*_kaman yanda haj Maryam ta fada har abada babu alaqa ko kusancin dazai hada zuri’arta tsarkakka mara najasa da daudar zina da zuriar Yar uwarta dasuka kasance gewaye cikeda daudar rayuwa mara kyau da amfani ta karuwanci.._*

*_Labarin IDON NERA kenan Wanda yazo cikin wani qayataccen salo da sabon tsari tareda nutsatsiyar kauna da soyayya kaman yanda muka saba wannan karon salon na musamman ne._*

 

_ALLAH YABAMU IKON GAMAWA LAFIYA KAMAN YANDA ZAMU FARA LFY.Amin_

Daga kwancen da ta ke bisa kan gadon ɗakin baccinta, ta kai hannu ta shafa cikinta ɗan watanni bakwai zuwa takwas, tana jin tarin ƙauna da soyayyar cikin na sake huda zuciyarta.

Sai dai a duk lokacin da ta tuna irin zaman da ta ke yi da uwargidan mijinta da kuma ƴarsa, sai ta ji wani tsoro na shigarta na yadda za ta haifi ɗa ko ƴa su rayu irin kalar rayuwar da ta ke yi a cikin gidan.

Wata iriyar rayuwa me sanya kewa da ƙunci wanda ba a taɓa ɗaga ido anyi mata duba na sassauci, bare har ta sanya rai watarana za a ƙaunaceta ko abinda za ta haifa ba.

Basu taɓa faɗa da juna ko musayar kalamai a tsakaninta da kishiyarta ko ƴar kishiyar ba, sai dai irin zaman shariya da wofintar da ita da suke yi a cikin gidan, ta gwammace ace faɗa su ke yi kullum ko banza a ce suna musayar kalamai marasa daɗi a tsakanin junansu.

Amma zaman da ta ke yi dasu zama ne na ba ruwan wani da wani a cikinsu, idan sun haɗu sai dai su kalli juna kawai, don ko ta kwantar da kai ta gaida abokiyar zamanta, ba za ta taɓa tada kai ta dubeta ba bare ta sanya ran za ta amsa mata gaisuwarta.

Kazalika Maryamah wacce ke amsa matsayin ƴar mijinta tilo da ta zo ta tadda a gidan budurwa me kimanin shekaru sha bakwai a duniya, wacce ta fi uwarta nuna mata zafin kishi da tsana tamkar ita ce kishiyarta ba uwarta ba,

 

Maryamah nada kishin abinda takeso take Kuma ganin nata ne,

 

Kaunar datakewa mahaifinta yasa takejin kishin aurensa sbd zai Haifa wasu yayan ya hada da ita,

A duniya abinda tafi tsana shine ‘yan ubanci,

Tanada wata irin fitinanniyar qyama da qyanqyami akan a hada Jininta da wasu shiyasa take Jin rashin kaunar matar mahaifinta.

Sam bata shiga duk wani sabga da zai haɗata da ita, kallo ma bata ishe ta ba bare ta sanya rai wani abu zai iya shi ga tsakaninsu,

Babu abinda hafsatu ta ke hangowa a cikin idanun Maryamah face qyanqyaminta da kishinta me zafi,

Ko mahaifiyarta takan jisu wasu lokutan tanawa maryamah din fadan rage qyamar shiga mutane Wanda ita Kuma tamkar halittace hakan Allah yayita idan tanason Abu tanaso,

Idan tana kaunarsa to tana kaunarsa

Idan batason Abu to da gaske take qin ko son kallonsa.

Hannu hafsatu takai ta shafa cikinta dake juyawa ahankali cikin cikinta tana sake jin wani irin abu na danne zuciyarta,

”Shin za su ƙaunaci abinda za ta haifa?

ko shi ma ba zai samu arziƙin ko kallon banza daga gare su ba? Maryama za ta rungumi ɗa ko ƴar da za ta haifa a matsayin ƴan uwanta na jini ko kuwa ƙiyayyarta da ta ke bangowa a idanunta shi zatawa abinda za ta haifo?”

Waɗannan tunanikan suka sake sanyaya zuciyarta har ta ji hawaye na biyo fuskarta ta Dan gyara kwanciyarta daidai lokacin da muryar mijinsu Malam Adamu ke ratsa kunnuwarta lokacin da ya ke kiran sunanta,

“Hafsatu! Hafsatu!”

Sai ta yi saurin kai hannu ta share ragowar hawayen da suka zubo mata tana amsawa da cewa,

“Na’am Malam gani nan fitowa

Daga haka ta nufo hanyar fitowa falon gidan wanda yake na tarayya ne kuma anan suke haɗuwa su ci abinci kowane lokaci sai dai idan randa Malam ɗin ya yi balaguro ne kawai ba a zaman cin abincin.

Ta samu wajen zama daga gefensa na dama ta zauna idanunta na satan kallon yadda Maryama ta ɗauke kai daga duban sashin da zata zauna ma baki ɗaya ta maida idanunta kan mahaifiyarta da ke hidiman zubawa Malam Adamu abinci a plate.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button