Furar Danko Page 8 Hausa Novel
Da ga airport babban kamfanin Jiƙamshi’s ya nufa ransa a ɓace. Kai tsaye ofishin Uncle Yousuf yay ma tsinke, sai dai yayi rashin sa’ar samunsa da ga bakin sakatariyarsa. Bayajin zai iya ƙara minti biyar a wajen, dan haka ya ajiye key ɗin motar tare da amsar takarda a wajen sakatariyar yay ɗan rubutu ya haɗa da key ɗin. A takaice yace, “Ki bashi idan ya dawo”. Da ga haka ya juya yay ficewarsa. Da kallo ta bisa tana tsarkake sunan ALLAH. Ga dai namiji har namiji sai dai aljihu babu ko sisi. A hankali taja ajiyar zuciya da ɗan taɓe baki…
Shiko da bai san ma tanai ba tuni ya fice, a ƙofar Companyn ya samu napep. Tsaki ya dinga ja a ƙasan maƙoshi har yanzu zuciyarsa na masa ƙuna da kaikawon abinda ballagazar yarinyar can ta masa. Har abada shi *_Aliyu Haydar Mika’il Idris Mawashi_* baiga talaucin da zai sakashi zama ana ƙasƙantar da rayuwarsa irin haka ba. Zai iya jure kowace irin wahala da ƙarfin ƙwanjinsa amma ba ƙasƙanci ba. Shi ba kowa bane, amma har gaban abadan bazai iya zama a ƙarƙashin takalmin kowa ba. Da’ace wannan yarinyar namiji ce yau wlhy sai ya kakkarya mata ƙasusuwa ya zubar da ita a airport ɗin nan. Amma ta godema ALLAH data kasance ƴa mace…..
“Ɗan uwa wane layi muka nufa?”. Mai napep ya faɗa ganin har sun shigo cikin anguwar ta fage. Sauka kawai yay daga napep ɗin maimakon amsa, ya zaro ɗari biyu a cikin aljihunsa ya miƙa masa. Bai jira mai napep ɗin da ke faɗa masa baida canjin hamsin da zai bashi ba yay gaba abinsa..
*_Aliyu M Idris Mawashi_* kenan da akafi sani da _Smart Mawashi_ yara da matasa na ƙasa da shi kan kirasa Uncle Smart. Abokansa kance Mawashi ko Smart guy, dan sune suka saka masa sunan dama saboda mutum ne mai matuƙar nutsuwa da kuma himma akan komai ga kaifin basira. Ɗa na bakwai a gurin Malam Mika’il Idris Mawashi. Shekararsa talatin da huɗu a duniya. Yayi karatunsa na addini dana zamani har zuwa matakin masters. Bayan nan ma yayi wasu couses har biyu. Sai dai har yanzu aiki ya gagara garesa. Uncle Smart mutum ne mai matuƙar nutsuwa, sannan babban hubby nasa a duniya shine ƙwallon ƙafa. Ya iyata matuƙa dan tun yana a secondary yasha ciwoma makarantar su wassani, bayan kammala sakandire ɗinne ya samu nasarar shiga Kano pillars. Ya buga wasu manyan wassani da suka fara fiddo darajarsa da sunansa wa duniya, sai dai abin mamaki sai komai ya tsaya masa cak, ya zamto in har ya shiga fili domin buga ƙwallo sai ya yanke jiki ya faɗi sai an kamosa an maida gida kamar wanda ya mutu. Da yawan mutane sun fassara al’amarin da asiri, sai dai shi yaƙi ɗaukar hakan da muhimmanci.
Daga baya ma sai ya tattara ƙwallon ya ajiye ya koma makaranta bisa shawarar mahaifiyarsa. Duk da haka yakan ɗan gwada yin ƙwallon amma dai ana nan jiya iyau, daya shiga fili sai dai a maidashi gida a sandare. A haka dai ya kammala karatunsa har yay bautar ƙasa ma, ya fara neman aiki amma yaƙi samuwa duk da takardunsa sunyi ƙyau matuƙa, abinda zai baka mamaki ma wani wajen har sai an ɗaukesa daga baya sai suce ba haka ba. Shi mutum ne da ya tsani wulaƙanci dan yanada saurin fushi. Sannan mutum ne da baya ɗaukar raini ga uban kowa duk tsananin wahala. Ya tattara aiki da ƙwallon ƙafa ya ajiye gefe ya shiga ƙoƙarin sana’a, sai dai anan ɗin ma dai komai yaƙi zama.