Fulani Page 5 Hausa Novel
Police din da suke gadin Masarautar ne suka bude masu gate, suna dagowa Shattima hannun duk kuwa da kasancewar ba su da
tabbacin yana ganinsu domin bakin gilashin motar ba zai basu damar ganin ya karbi gausuwarta su ba ko akasin haka
Kai tsaye Baba Adamu ya nitsa da motar cikin harabar Masarautar kamin ya dauki wani bangare da zai sadashi da bangaren Momy.
Kamin su karasa wayar Shattima ta sake ringing cirota yai daga aljihunsa yana dubawa Hajiya Karama ce rubuce a gaban wayar, sai da tai ringing kamar ba zai daga ba sai kuma yai picking.
Mikewa tai tsaye daga saman kujerar da take zaune ta fito daga dakinta ta zagayo ta fito backyard ta tsaya tana hango motarsa.
“Okay”
Ta sauke wayar da already ya kashe kiran tun da ya bata amsa.
A gaban wata katuwar kofa wacce ta sha ado kamar ba za a mutu ba Baba Adamu ya faka motar sannan ya fito da sauri ya budewa Shattima. Cikin wata irin isa da kasaita Shattima ya sako da kafafuwansa waje ya fito daga cikin motar yana wata irin tafiya ta takama kamar wanda baya son taka kasa, a zahirin takamarce da isa da kuma kasaita a tare da shi kamar yadda idon kowa na cikin Masarautar ke gani, sai dai a badini sam babu hakan a tare da shi ko da rana daya be tana jin ya fi wani ba dan yana dan sarauta, be taba jin wani ba sa’ansa ba ne dan yana da dukiya da ilmi, ba zaka taba fahimtar hakan ba har sai idan ka zauna da shi ka fahimce shi sosai da sosai.
Fadawan da ke gadin kofar ne suka bude masa da sauri suna risinawa tare da zuba gaisuwa, dayan kuma nata aikin isar da kirari, ko kallonsu be yi ba balle ya amsa musu gaba daya hankalinsa yana gun dansa kiran da Zainab tai masa bayan na Nana yasa hankalinsa ya kara tashi.
Cikin tafiyarsa ta kasaita ya natsa kafarsa cikin wani babban guri.
Wani irin katon falo ne mai dauke da Turkish furnitures tun daga kan kujeru har carpet da center table, da kuma side table dake kowace kusurwa ta kujerun, ga katon Hoton mai Matarba, sai kuma hoton Ammy sai na Hajiya daga gefe na mai Martaba a tsakiya sai hotunna wasu muhimman mutane na Masarautar dake tsaye a falo, idan ka cire farin fentin da ya kawata falon komai na cikinsa ja ne gwanin sha’awa, falon ya sha ado sai dai ba ado irin na komai a zuba ba, a a adon yan zamani wanda za a kawata falon da abu kadan amman masu kyau da tsada ta yadda duk wanda ya shiga ciki sai ya manta a wace duniyar yake, idan kana a cikin falon za kayi zaton akwai hadari a waje ne ko kuma yamma ta yi ko ma kai zaton farkon budewar safiya ne sakamaon hasken da aka kawata falon da shi kadan ne, mai daukar hankali, sanyin ac ta ko’ina, ga wasu manyan kyandira irin na zamani masu aiki da wutar lantarki suna bada haske a falon gwanin burgewa, ta dayan bangaren kuma wani irin kamshi ne ke tashi a cikin falon kashin da ba zaka iya tantance wane irin kalar turarene ba.