Daudar Gora Book 2 Page 99
Kusan mintuna uku suna a hakan kafin ya bude idanunsa ya sauke a kanta yana mai kai hannunsa saman veil din ta ya shiga warwarewa a hankali. Tanaji tana gani ya raba jikinta da kayan da suka gama jikewa sharkaf shi ma ya cire nashi. Jikinsa ta fada kawai nata na rawa ga wata matsananciyar kunyarsa na ratsata. Sosai hakan da tai yay masa dadi, dan ya samu damar sake gain tawadan ALLAH din nan ta bayanta yanda ya kamata, yanda har sai da ya haddace ta. Ita kam har aka kammala wankan bata yarda ta bude idanunta da ta rufeba.
Baya ta juya masa tana murmushi, hannunta ya kamo ya sake juyo da ita. Ya dago fuskarta da kyau ta hanyar dago da habarta. “Baki yarda ke ta musamman ba ce?”
Tana dan danne murmushin ta ta ce, “Ka dan dai”, Yanda ta fada da yin kamar zata dan kashe ido daya sai kuma ta jujyasu wani luuuu hakan nan zuwa gefe ya sashi jin jikinsa duk ya saki,amma sai ya kanne yayi dan murmushi kawai da sake rankwafawa suka zama dai-dai tsaho. “Zan tabbatar miki k ta musamman ce Mrs Eshaan.Dan bazaki sake rayuwa babu Eshaan a gefenki ba har abada insha ALLAHU”
Cikin dan waro idanunta kadan ta ce, “Har a kurkuku idan na koma”.
“‘Koda a tandun mai ne Babie. Hukunci na gama yankuwa zamu tafi can abunmu muyi zamanmu har sai kin haihu”
Takwaf-takwaf tayi da fuska kamar zata sakar masa kuka. “Wai da gaske kake sai ka maidani kurkukun?”.
*kyar ya iya danne dariyarsa, a zahiri ya dan Kara tsuke fuska da daga mata gira. “Way,miki ko Mrs Eshaan zata tsira da ga hukuncin Shahan-shan ne. Ai sai munje kurkuku dole, irin wanna laifi haka da muka rakitowa kammu”.
Baki ta bude a hankali zata sake magana ya manne lips dinsu waje guda, dole ta hadiye. Duk da a tsorace take da shi batai yunkurin hanashi ba, sai dai kuma bata bashi kowane irin gudunmawa ba har yay kidansa yay rawarsa ya barta. Da ga haka bakin ya mutu suka hau shirin barci, dama da biyu yay hakan dan ya gaji da maganar. Ya fara kula yarinyar nan so take tamaidashi parrot na karfi da yaji su Jaddah su sami abin masa gori. Wasu shegun kayan barci da bata san ina ya samo su ba ya dakko zai sakamata. Tako zaro ido zatai magana dan bakin faya fara dawowa (lols 😂)). Yatsansa ya daura saman bakinta ya ce, “Shill!!!”. Dole ta hadiye abin cewar tanaji tana gani ya saka mata su. Ina kasa Iffah ta shige ta buya kota huta da kunyar da bawan ALLAHn nan ke dawainiyar jefata ciki itakam. Shiko gogan naku ko’a jikinsa. Sai ma nasa shirin da yay cikin pyjamas dinsa shima marasa nauyi ya jata suka fito. Zaunar da ita yaya daya daga kujerun dakin shima ya zauna kusa da ita. Idanunsa da basu ko kyaftawa a kanta ya motsa a kasalance. “Zaki sha madara?”. Bawani tana jin yunwa bane, dan haka ta daga masa kai batare da ta yarda ta kallesa ba ita. Dan harga AllaH tsoron ma kallon jikin nan nasa take a tsaye, ga shi ya sa kaya marasa nauyi da gaba daya suka bayyana ainahinsa. Shi da kansa ya zuba madarar ya bata, ta amsa tana fadin, “Nagode”. Shi dai nasa kawai kallonta. Yanda take shan tata a takure harya kammala ita bata gama ba, dan haka suka dan jima wajen a zaune har ta fara hammar barci.
Koda suka kammala brush suka sake yowa ya ce mata ta kwanta dan ya fahimci barci takeji sosai. A darare ta kwanta har fuskarta na bayyana tsoronsa. Yi yay kamar bai lura da ita ba, yama koma cikin sofar da ya tashi ya zauna.Itako luff tai zuciyarta cike da toro da kuma mamakin abubuwan da tai yau a sashen Malikat Bushirat. Ta jima da sanin akwai wasu lokuta da take ganin abu baro-baro a zahiri bayan ta gansa a mafarkinta, amma fa yau ita kam kawai jitai tana zano zantuka ga Malikat Bushirat din wanda itafa kamar ana nuna mata su ne cikin idanunta a lokacin, sannan tana jin wani karfin iko da izzar fadar tasu babu o dar tattare da ita. Ta dafe kanta da ke dan mata ciwo kasa-kasa, ga wani barci da ke rinjayar idanunta mai nauyi. Dole ta tattara tunanin da tsoron ta hakura tai addu’a sai ko barci.