Daudar Gora Book 2 Page 89
Rasama abin cewa Daneen Ammarah tayi, sai kawai ta miƙe jiki a saɓule cike da tausayin Iffah. Tabbas dolene ta dinga kuka, a hakan ma sai taga dauriyarta, dan in har watace tofa sai duk masarautar nan sun fahimci halin da ake ciki. Fitowa tai ta samu Malikat Haseenat da ke zaman jiran fitowarsu. “Mammah akwai matsala fa gaskiya, dole a nema likita dan yarinyar nan taji ciwo bana wasa ba”.
Idanu Malikat Haseenat ta ɗan lumshe tare da buɗewa a lokaci guda. Dama ita ta fahimci hakan ai tun sanda tasa Iffah zama, ta kuma yi hakanne dama danta fahimta. Amma saboda ta sake tabbatarwar tasa Daneen Ammarah ɗin sake taimaka mata, turarrukan data bada a saka mata in har Iffahn taji ciwo mai yawa to bazata iya zama ba daman. “Ammarah wannan sirrine mai girma na shugaban daular ruman. Bazai yiwu ya fita ba kema kin san bama zai yarda ba. Dole ke zaki bata kulawar da ta dace”.
“Hakane Mammah, amma ni na ɗauka shekaru rabona da yin wani abu a matsayin likita. Kar’a samu kuskure”.
“Baza’a samu ba insha ALLAHU Ammarah. Na sanki akan komai shiyyasa nake alfahari da ke”.
Da ƙyar Daneen Ammarah ta iya haɗiye kukan da ke taso mata. Dan in har aka tuna mata ita ɗin ƙwararriyar likitace a baya yakan sosa mata wani ɓangare na rayuwarta data shuɗe da bata son tinawa. Dan tamkar fami akan gyanbon da tasan har gaban abada bazai taɓa ya warke ba a zuciyarta ne. Muryarta na ɗan rawa ta ce, “Zanje clinic na samo kayan aiki”. Da ga haka ta fice. Da kallo Malikat Haseenat ta bita zuciyarta itama na raunana. Tana son Ammarah, matuƙar so da duk a cikin ƴaƴanta sai dai a biyo bayanta. Sai dai tana dannewa da nuna iya tausayinta kawai gudun karta raba kan zuri’arta da kanta….
Tsaf Daneen Ammarah taima Iffah da ke kuka na fitar hankali ɗinkin, wai dan ma ta mata allurar kashe raɗaɗi fa kafin ma ta taɓata. Ana kammalawa ta dinga rawar sanyi na zazzaɓi kanta kam ai kamar zai fashe da ciwo. Malikat Haseenat ta tafi domin basu waje, sai dai ta aiko da lafiyayyen farfesu na musamman da wani irin kunun madara mai zafi shima na musamman. Sai tarin wasu sirrika da Iffah zata dinga amfani da su yayin sit bath da zai taimaka mata warkewa da wuri da kuma wanda zata sha dan tasan in dai wannan yaƙinne kam Iffah yanzu ta farashi. Dan in ma fitinar ce shi kam kamar yacema kowa bai iyaba a ahalin nasa. Gashi yana ɗage-ɗagen waɗan nan shegunan ƙarafunan abu goma da goma.
Daneen Ammarah sai da ta tabbatar ta gyara toilet ɗin ɗakin tsaf duk da bawani datti tunda ba’a nan suka kwana ba. Bata canja mata rigar Tajwar Eshaan ɗin da har yau take jikinta ba duk da ta mata girma da tsaho, dan ko’a wajen gashin dama sakata tai ta nannaɗe kawai. Zaunar da ita tai kan filos masu taushi amma ta kasa zama da ƙyau sai da ta karkace. Bata hanata ba ta zuba mata madarar da ke ta turiri tare da farfesun naman tsuntsayen da ke ta tashin kamshi.
“Mamy na ƙoshi bakina ɗaci barci zanyi”.
“A’a Ibnati daure kinji, idan kika sha madaran nan kikaci wannan naman sai na ƙarasa miki ɗayan alluran ki kwanta barci har sai sanda kukaso tashi kinji. Bakiji jikinki yayi zafi ba sosai. Haba ɗiyar albarka haihuwar alkairi”.
Da wannan lallaɓawar Iffah ta fara shan madarar a hankali, Daneen Ammarah na bata farfesun da kanta cike da kulawa. A haka Tajwar Eshaan ya shigo ɗakin da sallama ya samesu. A cikin kwalliya ya ke tsaf ta alfarma ga uban ƙamshinsa da ya cika ko’ina na ɗakin, a taƙaice dai a Shahan-shan ɗin sa yake. Cikin dakewar nan tasa mai ɓoye duk wani sirrin zuciyarsa da ainahinsa yake. Idanunsa sakaye da eyeglasses. Ya wani ƙara ƙyau da cikar kamala ga wani kwarjini mai ƙara yalwata haibarsa ga mai kallo. Daka gansa kasan shi ɗinne dai ɗaya tilo Shahan-shan ɗin ƙasar ruman mai rumawa da ƙasar ruman. Sai wani shining yake da ke tabbatar da yau ɗin ranarsa ce ta musamman mai ɗunbin daraja da tarihin da bazai taɓa goguwa a garesa ba.