Daudar Gora Book 2 Page 81
Shiru bai motsa ba har wasu sakanni. Kafin ya buɗe idanunsa da suka ɗan fara shanyewar barci a hankali. Sai kuma ya ɗan ɓata fuska yana ƙoƙarin kaudawa gefe. Riƙo fuskar tai cikin tafukan hanunnta tana murmushi da faɗin, “Oh oh beautiful Hafidi na faɗamin kaji”.
Idanunsa ya ɗan lumshe da jujjuya mata kansa kaɗan ya motsa lips ɗin da ƙyar da maganar nan nasa kamar ta dole, “Kawai ina son jin ɗuminki ne”.
“Uhyim, ita kuma Hafida-ti na aka barta ita kaɗai”.
Shiru yay kamar bazai tanka ba. Sai kuma ya yamutse fuskar daɗa duniya har cikin zuciyarsa ne ya wani kauda kai gefe, “Tanada hayaniya, gata da surutu”.
Mi Malikat Haseenat zatai banda dariya. Cike da nutsuwarta da ƙasaita ta shiga yin abinta. Ta ce, “Wayyo ni kai kuma gashi baka son hayaniya da surutu. Nikam ai ta burgeni, gara ta koya maka hayaniyar tata da surutun ko zamu samu ka dinga amsa mana magana biyar cikin goma. Naji daɗin hakan, dan itace dai-dai da kai”. A yanda take maganar zaka san lallai tana matuƙar jin daɗin. Shima dai acan ƙasan ransa murmushi kawai yake, dan ya sake tabbatar da kakar tasa mafi soyuwa a ransa na matuƙar ƙaunar ƴar hayaniyarsa da gasken gaske. Dama shi baya shakku a kanta, dan duk abinda Malikat Haseenat ta so to da gaske tana sonshi ne har cikin rai, idan kuma ta nuna ƙi to da gaske take ƙin nasa. Kamar tasan abinda yake tattaunawa da zuciyarsa ta cigaba da shafa kansa har yanzu da sauran murmushin dariyar da tai akan fuskarta. “Eshaan da gaske ina son yarinyar nan har cikin raina batare dana san dalili ba nima. Halayyarta kuwa na tuna min wasu abubuwa masu yawa. Yarinyar nada shiga rai, sannan tana da ɓoyayyun abubuwan ban mamaki tattare da ita. Karo na uku kenan ina aikawa nemomin iyayenta batare da kowa ya sani ba amma ana tabbatar min wai basa gidansu, a binciken ƙarshe ne na samu cikakken bayanin dalilin barinsu gidan, nasaka an bibiyar min kakaninta a ƙauyensu da aka tabbatar min su suna nan amma sai suma aka taki rashin sa’a. Na fara jin tsoron kar wani a cikin masarautar nan ne ya shirya cutar da su, dan tabbas abinda ya faru tsakaninka da yarinyar nan aike ne.. Bazaka tabbatar da hakan ba sai ka kusanta kanka da ita, kusanci mafi girma da a yanzu shine babban mafarki na, ina fata kafin na bar duniya naga jininka, a koda yaushe kuma na ayyana hakan zuciyata hoton yarinyar nan take kawo min matsayin uwar ƴaƴanka”
Yanda muryarta ke fita da sautin tabbatar da abinda ke zuciyarta ne ya saka shi ɗan buɗe idanu kaɗan yana kallonta, sai kuma ya tashi zaune shima a serious ɗin sa, shiru babu alamar zaice wani abu, ita har ta fidda rai ma da cewar tasa. Sai kuma a hankali taji sassanyar muryarsa ya ce, “Jaddah”.
“Yes Niger”
Ta amsa masa da kulawa. Kaifafan idanunsa masu nutsuwa da haske mai cika idanu da a yau launinsu ya ɗan surka ya zuba mata. Murya a can ƙasa maƙoshi da kamar an masa tilas ya jefa mata tambayar da ba ita tai tsammanin ji da ga garesa ba.
“Tambarin baƙi mai kamar tawadar ALLAH duk wani zuri’ar gidan nan ke da shi ko wasu ne a ciki?”.
Yanzu kam kallonsa take da mamaki matuƙa da ya gaza ɓoyuwa har a kan fuskarta. “Ban san miye dalilinka na wannan tambayar ba, ko kake son sani. Faɗamin miya faru?”.
Kansa ya girgiza mata alamar babu komai, sai kuma a hankali ya ce, “Ina son sani ne”.
Sam zuciyarta bata aminta da haka kawai bane, sai dai bazata matsa da son ji ba dan yana da hujjar ƙin faɗar, idan yaso wataran da kansa zai sanar mata. “In dai daga zuri’ar Aliy Qutb (mahaifin kakanka Abdull-Majeed) ka fito wannan tambarin shike tabbatar da kai. Sai dai bawai haka kawai ake gane kai ɗan zuri’ar bane da’an gansa. Akwai ajiyayyun hujjoji da ke tabbatarwar domin ana haihuwar jariri bayan yanke masa cibiya shine abu na biyu da ake duba masa. Yin wannan tambari a jikin duk wani jinin ahalinku ya samo asaline a dalilin kakanku na huɗu da yake da shi, mahaifin Aliy Qutb kenan, shi kuma Aliy sai yazam bashi da shi lokacin da aka haifesa amma sauran yan uwansa na baya duk sukazo da shi, maƙiya sai suka riƙe wannan hujjar a lokacin da za’a naɗashi sarki suka shigo da wata magana mai ban tashin hankali data girgiza masarautar nan baki ɗaya, har sai da ta kai anbi diddigin jinin Aliy da mahaifinsa. Wannan al’amari shi kuma sai ya riƙesa, bayan hawansa mulki duk wanda aka bincika bashi da tambarin sai an masa da wata alama da ke tabbatar da a cikin masarauta aka masa da hujjojin masu ƙarfi a rubuce.