Daudar Gora Book 2 Page 75
Da sauri ta sake maida natan kan nasa ta danne ta hanashi motsawa. Fuskar data kumbura yabi da kallo yana sake tsuke tashi, babu alamar wasa tattare da shi ya ce “Miye kuma?”.
“Ni wlhy ba sai ka taɓa ba zan yi da kaina, kuma ai yama daina”.
(Yarinyar nan zata kasheni wlhy) ya faɗa acan ƙasan ransa yana mai ture hannun nata ya matsa wajen. Zabura ɗaya tai ta kanannaɗe jikinsa tana fasa ƙara dan taji zafi na gaske. Yanda ta faɗo jikin nasa a bazata, ga hannunsa da yake ƙoƙarin toshe kunne saboda ƙarar da tai har cikin kansa. Baya sukai su duka, shi ya faɗa kan bayansa ita kuma tana a kansa. Bashi da zaɓin da ya wuce riƙota kawai. Wani irin dab-dab da juna fuskokinsu suka kasance, har hancinansu na gogar juna. Hakama idanunsu sun sarƙe cikin juna. Wani irin al’amari da ya sake rikita mata lissafin data manta da zafin ciwon da take ji ta gano cikin tsakkiyar ƙwayar idanunsa, da sauri ta kauda ƙwayoyin idanun nata a cikin nashi da son zame jikinta gaba ɗaya tsigar jikin nata na wani irin tashi, numfashinta kam fita yake da sassarfa. Hannunsa dake saman ƙugunta yasa ya sake maidota jikin nasa. Zafin da taji wajen bigewar ya sata matse fuska, sai kuma ta tura baki tana buɗe idanun nata kan ƙyaƙyƙyawar fuskarsa da gaba ɗaya kwarjininsa ya sa takeji ta kamar a wani kogon dutse suke a matse.
Yanda taki yarda ta sake kallonsa ya sa yaji murmushi na zuwa masa. Amma tsabar iya miskilanci da jin kai sai ya haɗiye kayansa yana ɗan lumshe idanun da sake buɗewa kan ƙyaƙyƙyawar fuskarta da tai wani takwaf-takwaf kamar zata saki kuka. Cike da son ta magantu ya ɗaura hannunsa kan inda ta bugun da ƙyau, murya a shaƙe kamar mai raɗa ya ce, “A kira Doctor?”.
Yanda yay maganar yana busa mata numfashinsa kan fuskarta ba ƙaramin yamutsawa tsigar jikinta tai ba. Cikin sauri ta jujjuya masa kanta tana ƙara ƙwaɓe fuska. Ita kanta bata sanin sanda take masa shagwaɓar nan, kawai samun kanta take a hakan. “Ni dai ya daina, ka barni na tashi ba ƙyau”.
Kafeta yay da kaifafan idanun nasa da suka sake shanyewa can ƙasa, cikin wani irin salon ɗagesu ya furta, “Mike nan?”.
Iffah fa gaba ɗaya ji take ma bada Shahan-shan take tare ba wani aljanin ne yazo mata a siffarsa. To inba haka ba taya za’ace ma Shahan-shan ne wannan. Mutum data sani ko kallo mutane basu ishesa ba, gaskiya wannan aljani ne, aljanin da ta jima tana gani kafin shigowarta masarautar nan….
Iskar da ya busa mata kan fuska ya sata jan numfashi mai nauyi alamar dawowa hayyacinta. Ya ɗan yamutse fuskan ta sa dake tsuketa, sake maida idanunta tai ta rissinar. Shima sai ya lumshe nasan ya ɗan sake buɗewa kanta yana motsa lips ɗinsa a hankali kamar wanda akaima dole. “Shi kuma wanda ya biya sadakinsa fa?”.
Idonta a rufen kanta tsaye, duk da muryarta a kasalance alamar ta fara laushi ta ce, “Kai dai ai baka biya ba, dan ta ƙarfi aka kawoni masarautar nan dan a lasheni kamar yanda aka lashemun yayu na”.
Da ƙyar ya iya gimtse murmushin da ke son kufce masa ya sake tsuke fuska a zahiri duk da ita bama kallonsa take ba. Daɗin biye mata yake ji, dan haka cikin ƙara ƙasa da murya ya ce, “In ma ban biya ba ai lokaci ne zai nuna. Mun taɓa lasar wani ne a gabanki zaki mana sharri?”.
“Babu wani sharri. So babu adadi ma”.
“Sai ki faɗa dawa-dawa muka lasa a gaban naki?”.
“Matarka da ta mutu mana. Kuma nima dan namana da ɗaci ne yasa kuka kasa, dan nifa nafi ƙarfin mayu, kaima nasan tsorona kakeji yanzu haka”. Ta faɗa da ƙarfin ikon son tabbatarwa tana wani ƙara tsuke fuska.
(Bazaki kasheni ba yarinyar nan) ya faɗa a zuciyarsa yana danne dariyar dake taso masa. A zahiri kam hannunsa ya maida a ƙugunta dai-dai inda ta bugu yana wani lumshe idanu da buɗewa, a hankali yake murza mata wajen batare data farga ba duk da tana ɗan jin zafi kaɗan-kaɗan. “Yaushe kika fara gano inajin tsoron naki? Dan nima dai naga kamar tsoron naki nakeji da gaske. Da alama baki barni haka ba kema mayyar ce ko?”.