Daudar Gora Book 2 Page 7
Yanda mummunar daiyarsa ke amsa kuwwa a jejin haka sautin bugun zukatan Miran Jasim da Miran Arshaan ke bada nasu sautin a ƙirazansu. Hatta yawun dake gudana da kai kawo a bakunansu zuwa maƙoshi ya ƙame ƙaf. Hargitsatstsun idanunsu kawai suka iya zubawa boka Barbushi da ke kwasar dariya har yanzu. Cikin ƙarfin hali da tsawa-tsawa na fitar hayyaci Miran Jasim yay ƙoƙarin dakatar da shi a kausashe..
“Koma mi ya taka ko yake taƙama da shi mu bai damemu ba. Muna son a ƙarasa mana rayuwarsa a wannan dare, haka itama yarinyar ta hanyar uwarsa Malikat Bushirat, asirinta ya tonu duniya duk ta shaida itace ta kashe yarinyar kaga sai ya gana da ƴan jaridar da hujja. A haddasa babban rikici tsakaninsu da talakawan ƙasar nan harma da tsohuwar can da rayuwarta ta zame mana ƙadagaren bakin tulu. Mu kuma zamuyi amfani da wannan rikicin wajen kawar da Eshaan ɗin ta hanyar aikin da likitoci zasu masa, sai kawai ace bugun zuciya ne dalilin abinda ke faruwa..”
“Hhahahaha!!! Hhhhh!!!” Barbushi ya shiga kwasar dariyar wulaƙanci sa mai tsananin bada amsa kuwa. “Ina son mugunta da mugu hhhhh!!. Ina son naga ana mugunta HHhH!!. Koba komai ƴan wuta sun sami ƙaruwa hhhhh!! (Wa’iyazubillah. Ya rabbi badan halinmu ba ka karemu daga nema a wajen waninka, ka tsaremu daga shirka da mushirikai🙏😭).
Duk da kalamansa na ƙarshe basu ji ko gezau ba akan ƙudirinsu, duk da kuwa sunyi imanin UBANGIJI ya halicci (WUTA DA ALJANNA) babu kokwanton zai cikasu kuma kamar yanda ya alƙarwanta, sai dai son cikar burin duniya na ƙanƙanin lokaci ya rufe zukatansu da idanunsu, sun jima matuƙa tare da shi sai gabanin asubahi suka koma masarauta ta ɓarauniyar hanyar kamar yanda suka fita….
Ƙarfe goma na safe ƴan jarida da taron al’ummar ƙasar ruman sun cika ƙofar masarautar Ruman cika mai ban mamaki kai kace Tajwar Eshaan ɗin zai fito ne ƙuru-ƙuru su gansa kamar yanda suka jima suna bege a rayuwarsu. Dole aka baza jami’an tsaro saboda gudun abinda zaije ya dawo……..
Tun a jiyan Doctor Afif yaso fahimtar da Tajwar Eshaan haƙuri da wannan zama saboda jikinsa har yanzu bawai ya kasance yanda ake bukata bane ba. Hasalima ana shirye-shiryen masa aikin da ya rage ne daga nan zuwa kwana biyu. Kallonsa kawai Tajwar Eshaan yay har ya kammala masa bayanin cike da girmamawa kai a rissine. Bai ce da shi komai ba tsahon lokaci, sai daga baya ya ɗan girgiza kansa kawai iya amsar kenan. Dole doctor Afif ɗin ya haƙura gudun shiga hurumin daba nasa ba.
Kamar yanda ya saba komansa kafin faruwar al’amarin haka ya gudanar a yau ma duk da rashin ƙarfin jiki dana ciwon dake sukarsa kaɗan-kaɗan. Sai dai kasancewar jarumin jarumai gwanin juriya da shanye kowane irin al’amari cike da ƙarfin hali ya shirya cikin ƙasaitaccen shirinsa mai firgitar da duk wanda ya ɗaura idanunsa a kansa shi ɗin wanene. Shirine da ya bayyanar da tsantsar ƙyawun da ALLAH ya bashi da cikar kamalar mulki mai tafiya da kwarjinin kasancewar sa cikakken mutum mai matuƙar zama barazana ga kowa. Ƙamshinsa matuƙar narka da zuciyar mai shaƙa yake a kowane motsinsa. Ya cika ɗawusun da al’ummar ƙasar sa ke kiransa wajen iya ado da zauna masa a jiki koma ya zarce. Dan tabbas ko’a cikin dubu baya boyuwa da lalube ma cankosa ake kasancewarsa ɗaya ƙwallin ƙwal Shahan-shan Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed da babu wani mai irin matsayinsa a ƙasar ruman da kewaye kaf.
A lokaci ɗaya gaba ɗayan masarautar ta ɗauki tsitt kasancewar fitowarsa a zahirinsa cikin takun dake tabbatar ma ga duk wanda bai san wannan fuska a zahiri ba shi ɗinne dai da suke cike da ƙishirwar son gani. Cikin karkarwar jiki data zukata hadimai ke faman zubewa bisa kafafunsu zukatansu na neman wantsalowa ta bakunansu duk da a kallo ɗaya da suke masa basa sake iya daga kai yin gigin kallo na biyu. Baga hadiman kawai ba hatta da masu faɗa ajin masarautar ma wutar kawunansu gaba ɗaya ta gama ɗaukewa dan al’ajabi. Domin kuwa tun fitowarsa hadimansu ƴan leƙen asiri har ci da goshi suke wajen isar da tsegumi ga iyayen gidan nasu kan fitowar Shahan-shan Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed yau a zahirinsa ga kowa babu shamaki…..