Daudar Gora Book 2 Page 63
Jigum-jigum sauran matansa da yara suka zauna. Kowa ka gani cikin damuwa. Dan wannan abun kunya ne da in har ya fita koda a cikin masarautar ne bazasu taɓa jin daɗi ba. Mijinsu mugu ne, dan ba yau ya fara kai hannunsa kansu ba, sai dai in ka cire Tajwar Haysam da Malikat Haseenat da mahaifiyarsa Ameera Banafsha kafin ta mutu babu wanda yasan hakan. Ko ƴayansu Husam ɗinne kawai ya sani sai mai bi masa Faida data zama babbar budurwa, inda ma ALLAH ya bata miji da tuni tai aure. Koda yake ba mijin ta rasa ba, taƙi sauraren samarin ne saboda mutuwar son Tajwar Eshaan da takeyi tun dawowarsa ƙasar ruman. Hatta da mutuwar matansa bai taɓa saka Faida jin zata iya daina son sa ba. Randa ya bayyana fuskarsa ba ƙaramin hauka tayi ba, duk da kuwa itama ɗin ƙyaƙyƙyawa ce sosai, sai dai shi kuma baima san tanayi ba..
Abinda suke gudun dai kam sai da ya faru, dan tuni hadiman sashen nasu suka fara zare jiki kai gulma ga iyayen gidansu. Dan wannan al’adace ta masarautar. Mafi yawan hadiman kowane sashe zaka samesu ƴan leƙen asirin ɓangarori daban-daban ne, duk da iyayen gidansu kanji a ransu akwai ƴan leƙen asirin bazasu iya banbance su ko fitowa suce ga su ba balle su fiddasu a masu hidimar tasu. Hakan yasa dole kowa ya haƙura da kasancewa cikin taka tsantsan kawai. Fitar wannan magana kuma sai tai dai-dai da wadda ta fara yawo na sakama Tajwar Eshaan kayan tsafi a kujerar zamansa da maganar Miran Arshaan da kai tsaye aka fara fassarata da cewar da Miran Jasim ɗin yake. ga kuma abinda ya aikata yanzu na sake tabbatar da maganar Miran Arshaan ɗin akwai ƙamshin gaskiya kenan…..
Iffah kam da bata san mike faruwa ba rabonta da ganin Tajwar Eshaan tunda ya bar sashen ɗazun da azhar. Duk da dai itama barcinta ta sha bayan idar da sallar azhar ɗin. A makare ma tai sallar la’asar. Kaɗan ta tsakuri abincin da aka kawo mata har ɗaki. Sanin babu mai hawowa floor ɗin na ƙarshe sai shi da amintaccensa yasa ta ɗauka wayar da ya faɗa da card ɗin data gani ta fito katafaren falon da wani irin ƙamshi mai masifar daɗi ke tashi. Shiru babu kowa hatta da television a kashe suke, dan girman falon yasa kusan tv uku ne. Itama kallon bawani ya ɗaɗarata da ƙasa bane, barta dai da son bibiyar labarai saboda yanda take matuƙar ƙaunar aikin jarida. Shine burinta, kuma Insha ALLAHU sai ta cika shi in har ta cigaba da numfashi a doron duniya. Cikin ɗaya daga lafiyayyun kujerun ta shige tana mai bin haɗaɗɗen falon da kallo kamar yau ne ta fara shigarsa. Komai na ciki ka kalla kasan an narka dukiya mai ban mamaki, ya fita tsaf kamar ba’a duniyar mutane ake ba (😂to dama irin wanga falo kam ai sai duniyar novel🤣 lols). Baki ta ɗan taɓe tana ƙunƙunin da ita ta barma kanta sani, daga haka takai kwance ta fara sarrafa wayar domin yin online shopping ɗin da ya umarce ta, dan bata son takurama Mamy kunyarta ta ke ji, akan abin nan daya faru tana jin nauyin haɗuwa da mutane biyu, Malikat Haseenat da Daneen Ammarah, saboda yanda ta shayar da jininsu guba amma su goyon baya da son bata kariya ne burinsu, wannan al’amari na bata mamaki da ƙara sakata a kunyar gudun haduwa da su.
Wasu kayan motsa jiki ne kalar pink sukai matuƙar fara ɗaukar hankalinta, ta shiga sakin murmushi tana yaba kayan a zuciyarta. Sai dai kuma ganin kuɗin da aka rubuta na sayensu ya sata zaro idanu waje. Sai kuma ta ɗan taɓe baki da ɗage kafaɗa tana ƙunƙuni wai ai dai kuɗin ma nasu ne su talakawan RUMAN, garama ta ci musu. Da wannan shawarar zuciyar tata ta dinga jidar kaya masu ƙyau da tsada tana ƴar dariyar muguntar yau sai tama asusun nasa wawason taron dangi zai gane ita Iffah bata wasan yara bace. (Ni dai nace hummmm 😂)