Daudar Gora Book 2 Page 55
Wani murmushi ne ya nema suɓuce masa a hankali, sai dai bai yarda ya bayyana akan fuskarsa ba ya hadiye kayansa yana mai lumshe idanunsa da launinsu ya canja baki ɗaya. Kamar bazai tanka ba sai kuma ya sake buɗe idanunsa ya sauke a kanta cikin wani irin kasalallen kallo da ya tilastata rissinar da nata.
“A ranar banga saƙonki ba dan bana cikin ƙasar nan”.
Ɗagowa tai da sauri ta dubesa. Idanunta a ware cikin rawar harshe ta ce, “Kamar ya baka cikin ƙasar nan? Bayan matarka an mata kisan gilla a tsakanin, hakama tsohon da kowa ke tabbatar da jayayyar da yay da kai ce tasa ka ɓaddashi. Kana nufin kuma da gaske kai ne Ajmaal ɗin dai?”.
Idanunsa ya lumshe ya buɗe a hankali, sai kuma ya miƙe a nutse zuwa gabanta, binsa take ita dai da idanunta da ke a waje gaba ɗaya kamar zasu faɗo har ya kai zaune a kujerar kusa da ita. Zamansa ya maida kafa ɗaya kan ɗaya idanun nan nasa masu kaifi shanye a kanta. Itama ta kasa daina kallonsa, dan gaba ɗaya kamar a rikice ma take. “Duk matar da aka kawo Masarautar nan da sunan tawa ni ke kaɗai na taɓa gani da idanuna, babu wacce ta taɓa rasa ranta ina a cikin masarautar nan kuma. Zaki san Ajmaal kamar yanda kike buƙata domin ina son muyi aiki tare”. Ya ɗan yi murmushin da ya nema ɗauke duka numfashinta batare da ya jira amasawarta ba ya cigaba, “Ki ɗauka anan tare kike da Ajmaal ba Shahan-shan Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed ba. Mi kike son sani?”.
Da ƙyar ta iya haɗiye yawu da rawar jikinta, dan itakam kallon komai take kamar a mafarki. Hasalima ya ƙara birkitar mata da kai ne. Cikin rawar murya kamar mai in ina ta ce, “Cafa kai baka taɓa ganin fuskar su ba, suna mutuwa kuma baka cikin masarauta? Taya hankali zai ɗauki wannan maganar?”.
“Ta yanda ya ɗauki zaman Tajwar Eshaan tare da ke anan babu wani shamaki mai shari’a”. Ya faɗa a hankali kamar ba daga shi kalaman suka fito ba. Yawu ta haɗiye da ƙyar tana ɗan tura baki jin ya kirata mai shari’a, sam zuciyarta tama ƙi yarda da wancan zancen nasa, “Ya akai ka zama abokin Sir Fawzan?”. Ta faɗa a hankali tamkar mai tsoron wani ya jita. Shiru babu alamar zai amsa mata idonsa na kallon ƙasa, dan dauriya kawai yake da surutun nan, da alama ita kuma kamar ma yanzu ya fara mata daɗi. Ya ɗan ja numfashi ya fesar a hankali, “A baɗini Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed abokin kowa ne a ƙasar ruman da sunan Ajmaal, dan haka shima Fawzan ya shigo ne kamar yanda kowa ke shigowa, a taƙaice dai na haɗu da shi ne a ƙasar Cuba, lokaci ina wani couse, abinda ya fara haɗamu so bawai sai an maimaita faɗarsa bane, kawai dai sanda nasan shi ɗan ƙasata ne naji farin ciki, na kuma nuna masa cewa nima asalina ɗan canne…”
Yanda yake maganar da ɗaɗɗaya kuma kamar da ƙyar sai taji ya bata tausayi da dariya, ta daɗe da fahimtar magana abune mai wahalar gaske a gareshi. Kamar ko yasan mi take tunanin, sai gani tai ya miƙa mata waya yana ɗan murza goshinsa da ke sarawa. “Mu cigaba a rubuce kaina yana ciwo”.
Dariya abun ya bata, tai murmushi idonta a kan wayar da yake miƙo matan. Kamar bazata amsa ba sai kuma ta amsa a zuciyarta tana faɗin (Miskilanci ma ai cuta ce gaskiya), a zahiri kam sai ta ɗan taɓe baki tana rubuta, “Miyasa randa na haɗu da kai a Eira garden ban ganku tare ba?, bayan kuma shi ya kirani ne dan na haɗu da Ajmaal?” ta mika masa wayar. Rubutun kawai ya tsirama ido harta fara ƙosawa, dan bashi da alamar zai bata amsa. Sai da ya gama shan ƙamshinsa sannan ya amsa a rubucen shima. “Dama banyi niyyar mu haɗun ba, dan ina son na fara sanin waye ke”.
Sosai ta waro idanu tana kallonsa lokacin da ta gama karantawa. Bama ta san bakinta ya suɓuce wajen faɗin, “Saboda mi to?”. Shiru yay kawai ya tsira mata idanu, sai kuma ya ɗago a hankali ya zare wayar daga cikin hanunta.